← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 165

Sashe 25

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hey idan ka ga dama zaka ajiyeni a well care yanxu yanxu" tana fadin haka ta juya ta bar wajen. Da ido ya bi ta, sai kuma ya mike ya ciro makullin a aljihunsa ya bi bayanta, tana tsaye compound din ta kira Aliyu, ta sanar masa gata nan xata fito, bayan ta gama wayar ta karasa ta shiga bayan motar, sai da suka hau saman titi sannan yace "Kwatance xa ki yi" Ta hade rai tace "Kai ko ina sai kace baka sani ba sai an maka kwatance, baka da Google map ne??" Yace "Ban da" Tsaki ta ja, haka ta dinga gwada masa inda xa su bi har suka iso well care, parking yayi a space da ake parking din, tayi dialing number Aliyu, yana dagawa tace "Are u inside?" Waige waige ta fara yi jin abinda yace, tace "I am also outside, where did u park?" Sauke glass tayi, lkci daya ta hangosa, murmushinsa me kyau ya sakar mata yana kallonta, xata katse wayar yayi saurin cewa "Waitt" sai ta fasa kashewa tana sauraronsa, yace "What if idan an ɗan basa wani abu mu ce ya jira mu a nan, mu je eatry... i am jet hungry" Rasa abinda xata ce masa tayi, don ta ce ma Mumy baxata dade ba, can ta saci kallon Khalil ta ga idonsa a kan Aliyu yake ko kiftawa bai yi, duk da glass din a dage yake, kuma tinted ne ba me duhu can ba, a ranta tace wannan ma yayi kama da wanda xai amshi abu idan an basa, bude motar tayi ta sauka ta nufi inda Aliyu yake, shi dai Khalil bai daina kallon Aliyu ba kamar ya ga wani halitta na daban, tana karasawa gun motar Aliyu dake ta kallonta underneath his breathe yace "Waow, baby kin kara kyau fa, tell me what is d secret" Tayi masa murmushi wanda har dimple dinta sai da ya lotsa, sauke idonsa yayi kasa, can ya zaro dollar 100 a aljihunsa yace "In bashi wannan ya jira mu a nan?" Tana kallon kudin tace "Toh kasan dai ba wai mun saba da shi bane, snn bashi da kirki fa wllh" Aliyu yace "Kudi ne baki fara basa ba shi yasa baku saba ba, yana ganin wannan yanxu xaki ga kun dawo kun dai daita kun saba" Bude motar yayi ya fito, walking majestically ya nufi motar, Nihad ta bi sa da kallo, Waige waige khalil ya fara yi da sauri, as if looking for an alternative kafin Aliyu ya karaso gun motar, lokaci daya kawai yayi locking motar kafin ya iso, Aliyu na karasowa ya bude motar yaji a kulle, kwankwasa glass din motar yayi, Khalil ya kauda kai duk da Aliyun ba ganinsa yake ba, Sau biyu Aliyu na kwankwasawa kafin ya daga kai ya kalli Nihad, ta buda masa hannu alamar i told u dama, mamaki ne ya cika Aliyu ya dinga kallon motar, can ya sake Kwankwasa glass din, tace "Dear just leave him ka bar wajen kawai, ba nace maka ɗan iskan yaro bane" Aliyu da ransa ya gama baci yace "Who did he think he is, da driving din da yake yi ake biyansa yake takama ko me? Waye shi yana matsayin just driver xai kulle mota yana jin ana kwankwasawa ya ki budewa, kuma ba wai bai gan ni bane" Nihad tace "Ai ban ta6a ganin mutum me karfin hali irin yaron nan ba" Aliyu yace "Look Nihad idan kika shiga school gobe xa mu hadu, i can't stand here any longer, mood dina ya baci seriously, ba a ta6a ci min fuska irin yau ba" Nihad tayi shiru tana kallonsa duk jikinta yayi sanyi, don kana ganinsa kasan ransa yayi mugun baci da gaske, tafiya ya fara yi kawai ya koma gun motarsa ya shiga ya tada yayi zoom off, da ido khalil ya bi sa har ya hau saman titi, Nihad ta dinga kallon motar tana jin kamar ta rushe da kuka ko xata ji sauki a ranta, mutumin da tayi wata da watanni bata gani ba, shine wannan drivern xai 6ata ma rai har ya tafi?? Ta fi minti biyu tsaye kawai kallon motar take with different thought running her mind ga wani kullutu da ya tokareta a makogwaro sbda bakin ciki da takaici, a duk abubuwan da yake mata bata jin akwai wanda ya mata ciwo ya ta6a har karshen xuciyarta irin wannan, she is trying her best not to cry, don har idonta ya cicciko, kiris ya rage ta fashe da kuka a wajen, Khalil dake ta kallon duk expression da reaction dinta ya shafa kansa, sai kuma ya sauke both glasses yace "Naga kamar kin fasa siyayyan, kuma ga hadari, ni kuma bana tuki cikin ruwa ko in baki makullin in yi tafiyata??" Wani matsiyacin shegen kallo tayi masa, ta bude back seat ta shige motar ta kulle da karfi tana kara danne kukan dake cin ta, tada motar yayi, yayi reverse ya dau hanyar gida, har suka isa gida Nihad danna kukanta take, bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta tafi gun driver seat ta tsaya tana nunasa da yatsa tana huci tace "Sai kayi da ka sanin abinda kayi min yau wllh, kuma ni ce sanadin barin ka gidan nan, banza mahaukaci kawai talaka" Kashe motar yayi ya sauka yana kallonta ya kara mata kunne gaba yace "Kamar kina magana?" Da wani bakin ciki ya mamayeta bata san sanda ta cakumo kwalarsa ba duk da uban tsayinsa tsaurin idonta bai sa taga hakan ba, tana jijjigasa da duk karfinta hade da kunduma masa wani mummunan zagi, mai gadi dake ganin komai ya karaso da gudu jikinsa na bari yana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Subhanallahi... " Khalil dai kallonta kawai yake baya ko kiftawa, cikin nutsuwa yace "Cika ni" Ta buga wani uban tsawa tana dungure masa goshi tace "An ki a cika ka din, kayi uban da xaka yi in ga, kai har ka isa kana aiki ƙarƙashinmu kana matsayin Drivern gidanmu ka dinga kawo min raini? Ni ce ma zaka raina? Kasan wa ka walakanta daxu?? To wllh ko kaff zuri'arka xa a siyar idan har Aliyu ya daureka kudin da aka siyesu bai isa yayi bailing dinka ba" Nihal ta fito cikin gida da kawarta xata mata rakiya ganin abinda ke faruwa ta karaso da sauri xata ta janye Nihad tace "Nihad what's this u are doing, don't u have manners? Meye wannan kike yi?" Nihad na huci ta bangajeta a fusace tace "Eh ban da shi, sai ki ara min naki ke me shi, a kan matsiyacin nan xaki ce min bani da manner, kin san abinda yayi min ne?" Nihal na kallon Khalil cike da damuwa tace "Don Allah kayi hakuri" Yana warware rigarsa da Nihad ta cakuikuye yace "Ba komai... fita xa ki yi ne?" Nihal dai duk jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, yace "Ko ba fita xa ki yi ba?" tace "Aa Kawata xan raka bakin titi" ya kalli kawartata dake tsaye ita ma tana kallon abun mamaki, yace "Ohk to, ta hau sai na ajiyeta a gida, xan jira ta a waje...." Yana fadin haka ya koma motar ya tada ya bar wajen, mai gadi ya tafi da sauri ya bude gate, Nihad bata san sanda ta fashe da kuka ba, da hanzari ta shige cikin gida tana kuka sosai. Bayan ta ci kukanta me isarta ta dau wayarta ta kira Aliyu, har ya katse bai daga ba, ta kuma kiransa nan ma no response, hawaye ne ya dinga sauka idonta, bayan kusan awa daya ta mike ta gyara idonta ta fita, bangaren Mumy ta tafi sai taga kamar tana da bakuwa, hakan ya sa ta bar wajen ta tafi gun Umma, Umma tace "Lafiya me ya sami idonki Nihad?" Cikin rawan murya tace "Umma Aliyu ne ya dawo shine muka yi da shi xa mu hadu a wellcare, bayan mun hadu sai ya sauko daga motarsa yace bari su gaisa da driver ai ko in gaya maki mutumin nan yayi masa walakanci mafi muni, ya kulle motar ya kuma ki ya sauke glass, banda Abba da ya ja mana ina Driver xai ma tsaya same place inda nake balle Aliyu? Yasan waye uban Aliyu a kasar nan, kaskantar da kansa fa yayi ya tafi su gaisa maimakon shi drivern ya sauko ya taho har inda yake ya gaishesa amma ya masa wannan mugun walakancin" Umma dai sakin baki tayi tana kallon Nihad, can tayi kasa da murya tace "Wai har yanzu kuna tare da Aliyun nan ne dama?" Nihad ta gyada mata kai tana matsar kwalla, Umma tace "Ba kince min kun rabu ba kwanaki?" Nihad tace "We came back together 1 month ago" Umma tace "Ke dai bakya ji Nihad nace ki fita harkan yaron nan, ba mutunci ne da familynsu ba kin ki, nace ki rabu da shi in kina son sama ma kanki mutunci kina son ki tsira da mutuncin ki, ina ke ina Aliyu banda dai yaudaran kai Nihad? Kika san wasu irin yan mata yake hulda da? 'ya yan shugaban kasa yake hulda da fa" Nihad taki cewa, Umma tace "Gaskiya kar ki sake kulasa ni dai na gaya maki, yana son ki ne ko sau daya bai ta6a takowa ya xo gidanku ba? Sai dai soyayya a titi da makaranta, kema kinsan yaudaran kanki kike don Aliyu ya fi karfin ki, me ma xai kawosa gidan nan? waye ubanki a inda ubansa yake, inaa ai nisan ma yayi yawa, balle ma duk yan iska ne yaran masu kudin nan wa enda idonsu ya yage har kunne, banda lalata yara da bata masu rayuwa babu abinda suke" Nihad still ta ki cewa komai, Umma tace "Kin min alkawarin xa ki rabu da shi kiyi blocking dinsa kamar yanda kika yi blocking din Ahmad yanxu?" Nihad ta turo baki tace "Ni dai ina sonsa Umma, shi ma kuma yana so na ai, da baya so na baxai dinga kirana ba har yace mu hadu a wani waje, dama ce maki xanyi xan je gidansu Baffa ko da Mumy ta tambayeni" Daga haka tayi ficewarta daga parlon Umma ta bi ta da ido ko kiftawa babu, Nihad na sauka
Chapter 25 · 0% Book details