← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 165

Sashe 16

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kawo min kararsa, ashe d'an iska Habibu ya turo ma Alhaji ba a sani ba, to kuwa xai kama gabansa yanxu yanxun nan, kwanansa daya dubi isa da mulki da yake gwadawa ya yanmu?, nan gaba ai har Alhajin ma cewa xai yi baxai tuka a mota ba" Mumy bata kuma tsayawa ta saurareta ba ta wuce part dinta. Mai gadi na kallon Khalil bayan ya gama shanya kayan da Nihad ta xuba masa ruwa yace "Hakuri kawai xaka yi, amma lallai yarinyar nan shaidaniya ce a siffar mutum..." shi dai khalil bai ce komai ba, mai gadi yace "Ga can abinci da aka kawo mana, na debar maka naka na ajiye" Khalil yace "Aa na koshi, yanxu wanka nake so xan yi" Mai gadi yace "To mu je in raka ka bangarenku" A tare suka nufi boys quarters din bayan mai gadi ya dauko wata er jakar kayan Khalil da ya bari a dakinsa tun xuwansa da safe, suna shiga parlon banda warin kartin maza babu abinda yake, ko ina soo dirty and unkept, ga saminu yayi bake bake kan 3 seater yana kallo ga plate din abinci da ya ajiye saman kujeran, Isiya na one sitter yana shan rake da yake tarawa nan kasa gefensa, Shafi'u kuma na 2 seater ga tasa plate din abincin ya gama ci ya bari saman kujera, Mai gadi ya nufi Saminu yayi kasa da murya yace "Saminu ko xaka ɗan sam masa waje ya dinga kwana a dakinka, ka gansa bashi da matsala wllh..." Ko rufe baki Mai gadi bai yi ba Saminu yayi saurin cewa "Aa nima dakin yayi min kadan" Mai gadi ya kalli Isiya dake jin abinda ya ke cewa, kafin mai gadin yace masa komai yace "Toh wai ba falo kace xai dinga kwana ba" Shafi'u yace "Shi dai na gani, Duka dakunan kaga ai babu waje, wa ke son takura" Khalil ya amshi jakarsa dake hannun mai gadi, mai gadi yace "Ko xa mu je can dakin nawa ka dinga kwana" Khalil yace "Aa kar ka damu, kayi komawar ka bakin gate" Yana fadin haka ya nufi space da aka tanadar domin dinning area a parlon, Kofar da ya gani ya bude ya ga kitchen ne, ya dinga kallon yanda suka mayar da kitchen din kamar na mahaukata duk da ba girki suke ba, tsintsiyar da ya gani wanda bai ga alamar ana amfani da shi ba ya dauka, ya hau share dinning area din, mai gadi ya juya ya fita daga parlon da sauri jin kamar ana horn. Cikin yan mintuna khalil ya gama gyara area din har da mopping, yana gamawa sai ga mai gadi ya kawo masa wani yakunannen zanin gado, amsa yayi ya shimfida a saman tiles din wajen, sannan ya bude window, ya shiga bandakin dake parlon, still yayi yana bin bathroom din da kallo, ko public toilet is far far better and neater than this, fita yayi ya koma gun mai gadi don ya amshi omo. Abba yayi shiru yana sauraron Mumy, Mumy ta ci gaba tace "Kawai ita Hajiya duk wani abu na cin mutunci da cin fuska shine dai dai a wajenta, ai wannan ba rayuwa me kyau bane, har take cewa ka sallamesa, da yayi me? Ruwa fa ta dauka gun me kayan marmari ta watsa masa a jiki, kawai dai ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, haka ta sa Habibu a gaba daga baya ta gaji ta saukar da kanta, mai aikin gidan nan ba dadin Nihad take ji ba, Nihal kuma ba haka take ba, na rasa wannan baƙin hali irin na Nihad ni kam, ni dai ba haka taga nake mu'amala da jama'a ba balle tace, kai kanka ba haka mu'amalar ka da jama'a yake ba, to halin wa ta yo haka, idan ba shiga hakki ba wllh kar ka fara ce ma bawan Allahn nan komai, a kan me xata ce sai ya bata makullin motata ta tafi gantalinta da yamma sbda rashin kunya ma bata yi shakkar cewar motar tawa bace, kuma naga ai ba ita ta basa makullin ba ni na basa, to a kan me xai bata..." Abba dai yayi shiru bai ce komai ba, ganin ta gama fadin abinda xata fada yace "But that doesn't warrant u to slap her publicly Maryam, why not ki bari idan kuka dawo gida ki hukunta ta?" Mumy tace "Wato na goyi bayanta kenan Yallabai, ai yanda tayi rashin kirkinta a bainar jama'a gwara nima na hukuntata a cikin jama'ar dai dai kenan, ni fa i am not in support of walakanta d'an Adam Yallabai, kuma babu wani da ya fi wani a wajen Allah sai wanda yafi tsoronsa, idan ma xaka share xancen nan ka je ka huta to gwara ka share" Abba bai kuma cewa komai ba, Mumy tace "Can i excuse my self?" Yace "Alright" ta mike tayi masa sai da safe sannan ta fita, Umma ta fito daga bedroom din Abba don duk ta ji yanda suka yi da Mumy, tana ta6e baki tace "Yau ni naga neman suna kiri kiri gun talakawa, ita a neman sunan ma ta rasa inda xata dinga yi sai wajen talaka? Ai kamata yayi ta dinga kutsa kanta cikin manyan mutane ana yi da ita, ta nan ne neman suna xai mata rana, amma ke kice duk abinda talaka yayi dai dai ne, a dole sai kin burge?" Abba ya mike ya fita daga parlon, compound ya fito, dai dai nan khalil ya fito daga dakin mai gadi ya amshi omo, ganin Abba ya nufesa ya gaida shi da ladabi, Abba ya amsa yana kallonsa yace "Ibrahim, a dinga hakuri da yaran nan don Allah, sannan duk sanda Nihad ta sameka da batun amsan makullin mota kana da number ta ka kirani, idan wanda xaka bata ne sai ince ka bata, don ba wai bata iya driving ba, tana driving to where ever she wants to, just sbda security purpose ne bana barin suyi driving din da kansu, so kar kayi zaton bata iya driving din bane, and u gat respect them all kamar yanda xaka yi respecting dina ka ji" Khalil da kansa ke kasa a hankali yace "Toh in sha Allah Alhaji" Abba yace "Sun baka daki a can boys quarters din ko? Don nasan akwai empty room da Habibu ya bari" Khalil yace "Ehh an bani" Abba na kallon omon hannunsa yace "Wanki xaka yi da omo?" Yace "Eh xan wanke bandaki ne" Abba yace "Ohk good, wannan ai yayi kadan, no problem xa a kawo maka daga cikin gida yanxu" Yace "To nagode Alhaji" daga haka Abba ya juya ya koma cikin gida, khalil ya koma can boys quarters din. Abba na komawa part dinsa ya kalli Umma yace "Ki ba ko Sudais ne blanket with some detergents ya kai boys quarters" Umma tace "A kai ma wa a can?" Abba yace "Driver" Umma tace "Aa da dai kaje gun uwar dakinsa ta bada a kai masa, ni kam bani da old blanket, kaji Alhaji da wani xance, shine yace ka basa blanket din?" mikewa Abba yayi ya fita, ya tafi bangaren Mumy, tana daki ya sameta yace "Maryam blanket xaki ba Sudais with some detergents ya kai ma driver din can" Mumy tace "Sudais ai yayi bacci yallabai" Abba yace "To bani" Wani blanket dinta ta dauko, sannan ta dau pack din omo da sabulu with toothpaste ta hada ta ba Abba, Abba ya amsa ya fita dakin, a stairs ya hadu da Nihal xata dakinsu, tace "Abba where are u going with the blanket" Yace "Boys quarters xa a kai ma drivern can" Nihal tace "Ohk, bari in kai Abba" Abba yace "Good" Amsa tayi daga hannunsa don dama da Hijab a jikinta ta juya ta koma downstairs ta nufi kofar fita main parlor, boys quarters din ta nufa, tayi Knocking duk da kofar a bude take, isiya ne ya karaso ganinta ya gaisheta da ladabi xai amshi blanket din yace "Wanki ne Hajiya?" Tace "Aa, ina sabon driver yake?" Jin haka Khalil dake bandaki xai fara wankewa ya fito ya nufi kofar, kallonta ya dinga yi don da farko ya xata Nihad ce, amma sai yaga ba itan bace don wannan fuskarta bai rabo da murmushi, ya amshi abinda take mika masa, yace "Nagode sosai" Juyawa tayi ta sauka chalet din, ya koma cikin parlon yana kallonsu Isiya yace "Ku yi kokari ku bar barin kofar nan a bude sbda sauro" Da ido duk suka bi sa, lkci daya suka kya6e baki, ya ajiye blanket din ganin omo, sabulun wanki da na wanka sannan ga Toothpaste ya kwashe su gaba daya ya wuce bandakin, ya bata fiye da minti talatin yana wankin bandakin don sae da omon yayi rabi, lkci daya bandakin ya dawo hayyacinsa, wanka yyi ya fito, ya kulle bandakin da makulli sannan ya cire makullin ya koma dinning area, ya shimfida babban bargon wanda laushinsa ba a cewa komai, ya bude window dake wajen sannan ya kwanta ya rufe ido, bayan minti sha biyar yaji ana magana, ya bude ido ya ga Saminu tsaye a kansa, shiru yayi yana kallonsa, Saminu yace "Makullin bandaki da ka kulle xaka bada" Khalil yace "Ohk, dama kuna amfani da bandakin kenan?" Saminu yace "Yo me xai hana" Khalil yace "Ohk, shine ku ka bar shi yanda na samesa?" Bai jira Saminu yace komai ba, yace "Amma dai kamar babu bandaki a dakunan naku iya wannan kadai ne ko?" Saminu yace "Akwai mana, amma wannan din muke shiga gaba daya ai" Khalil ya ciro makullin da ya ajiye a aljihun gaban rigarsa ya mayar aljihun wando sannan ya gyara kwanciyarsa ya rufe ido, xuwa yanxu daga Isiya har Shafi'u na tsaye parlon suna kallonsa gaba daya, Saminu yace "Toh wai kai gayen nan me kake nufi tukunna ma dai" Mikewa Khalil yayi ya tsaya sai ga Saminu ɗan tsut a gabansa, Khalil na kallonsa da kyau ya tsaya dab da shi yace "Baxan bada ba nake nufi" Shafi'u ya koma ya xauna haka ma Isiya suna kikkifta ido, sui sui Saminu ya bar dinning area din shi ma yana gwaggwale ido.
Chapter 16 · 0% Book details