← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 165

Sashe 95

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ta yi sadakansu, ai ko ta sha godiya sannan albarka ta sha shi kwando kwando, wani kunu me ruwa ruwa aka dire mata as breakfast da dumamen tuwon da bata ci jiya ba, Nihad tayi tagumi tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta ya xubo ba, wajen karfe takwas aka kai mata ruwa tayi wanka bayan ta dawo bukkar ta shirya sai ga khalil ya shigo gidan tun daga bakin kofa Dattijuwar ke basa labarin alkhairin da Nihad tayi masu da makota, har da fito da akwatin da Nihad ta bata ta nuna masa, yana shiga bukkar da Nihad take yaga babu kaya ko daya ya kalleta, ita dai kanta na kasa, can yace "Ina kayanki suke?" A takaice tace "Na rabar, ko kai baka ga kayan da suke sa wa bane" Yace "Ohk, ashe xaki yi ta maimaita kaya kenan...." Ta fashe da matsanancin kuka tace "Toh meye don na masu sadakan kaya, idan haka ne mu koma gida in kwaso wasu kayan sannan mu dawo mana" Yace "Koh?" Tace "Ehh mana" yace "Okay, xamu koma ki debo duk kayan naki sai mu dawo" tana share idonta tace "Na yarda, daga nan ma sai mu taho da ruwan gora da biscuits" Yace "Toh" Daga haka ya fita daga bukkar. Har rana ya fara yi Nihad na ta baza ido bata ga Khalil ba balle su bar garin, da rana aka kawo mata ordinary wake da aka dafa aka xuba masa man gyada ita da bata cin wake, ga shi wani axababben yunwa take ji, haka ta bar masu tsiyarsu, wasa wasa har kusan la'asar ba khalil ba labarinsa, da taga yunwa xai mata illa haka ta daure ta dinga danna fura da nonon da aka dama mata, shiru shiru har magrib, bayan ta idar da sllh ta ci kukanta ta gode Allah, har aka yi isha bata ga Khalil ba har ta daina tambayar dattijuwar dake assuring dinta yanxu xai shigo, bayan tayi sallan isha kawai ta dage net ta shige tana shesshekar kuka ba tare da ta bi ta kan tuwon dawar su ba, can wajajen karfe goma sha daya saura ta dinga jin kamshin turarensa, sai kuma ta ji suna gaisawa da mutanen dake tsakar gida kafin ta shigo, xa a kawo masa abinci yace masu ya koshi, bayan like 10 mins ya dage net ya hau saman gadon ya haskata da karamar wayarsa, duk da tana jin sa bata yarda ta bude idonta ba, kashe fitilan yayi ya kwanta, ta bude ido ta dawo kusa da shi ta fashe da kuka tana shessheka tace "Kai fa kace idan na gama sanye kayan da na kawo za mu tafi gida, toh gashi yanxu ko kayan da xan canza gobe bani da shi" Yace "Sae ki maimaita na yau" kuka take sosai, ya juya mata baya, ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta koma ta kwanta a hankali, bayan kusan awa daya ya kunna torch dinsa ya haska fuskarta ya ga bacci take. Can kusan asuba xafin jikinta ya farkar da shi, kamar jiya tana kusa da shi ta takure waje daya, ya kai hannu jikinta ya ji da xafi....
Chapter 95 · 0% Book details