Sashe 138
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_SCENTMANIA_💯Khalil bai kuma ce ma Mami komai ba sai kallonta kawai yake lokaci daya duk jikinsa yayi sanyi, juyawa Mami tayi ta fice daga dakin ta zauna second parlonta, a hankali Khalil ya zauna kan kujeran dake dakin yana jin kansa na mugun sara masa, gaba daya he is confuse, dafe kansa yayi thinking of where to start from, where will he begin now? Damuwar Mami ya ninka wanda shi ya ji ya shiga a lkcn, daga karshe taji ta kasa zaman ɓangaren nata, she just can't imagine Khalil ya sake barin gida for the second time saboda wannan issue din, tafi kowa sanin halin mahaifinsa, this time around also he won't take it likely with him, tashi tayi tana jin wani sabon tashin hankali ta fita daga parlon, Nihad na nan zaune yanda take a first parlor din, Mami bata yarda ta kalleta ba amma jin yanda take kuka sai ta kasa fita daga parlon duk da ta bude kofa, kulle kofar tayi gently ta juya ta kalleta, sai kuma ta nufeta walking slowly tace "Kina ji na, ki daina wannan kukan ya isa haka, ga breakfast dinki ki tashi kiyi" Nihad bata iya ta ce mata komai sai kuka take kamar ranta zai fita, sai a yanzu maganganun Aunty Jamila ke dawo mata and it seems this is just the beginning of what she's talking about.... Mami tayi karfin halin cewa "Taso muje can parlon ki karya, kuma nace ki daina wannan kukan haka nan" Daga haka Mami ta daukar mata abubuwan karin ta kai other parlor dinta ta ajiye, bayan ta dawo parlon tana kallon Nihad tace "Baxa ki bar kukan nan haka ba? Taso mu je can parlon" Sai a sannan Nihad ta mike da kyar, har sannan kuma ta kasa daina kukan da take, Mami ta rike hannunta har zuwa daya parlon ta zaunar da ita tace "Eat now" Zaunawa kawai Nihad tayi, her heart is so heavy, and she is now beginning to feel useless, juyawa Mami tayi ta fita daga parlon, Visitor room dake bangaren nata ta shiga kawai ta zauna cike da damuwa. Khalil ya mike daga karshe jin kukan da Nihad take ya fito parlon don Mami a bude ta bar kofar bedroom din nata da ta fita, Zaunawa yayi kan kujeran dake kusa da inda take zaune, he is speechless at first, after few seconds ya kalleta, a hankali yace "It's okay, and...." Sai kuma yayi shiru, Can yace "Kiyi hakuri" Ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, yace "Baki ji me nace ba" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa da idanuwanta da suka yi jajir, ya kasa ci gaba da kallonta ya sauke idonsa yace "Kiyi hakuri, take ur breakfast now" A hankali ta dinga subsiding kukan da take amma tana jin xuciyarta na mata zafi, Ya sauka ya koma inda take without looking at her ya dau cup ya zuba mata ruwan shayi, ya haɗa mata shayin, ya ajiye side dinta, ita dai goge hawayen da yaki tsaya mata kawai take tana kallonsa, Bude kofa yaji anyi a other parlor din, ya dau shayin yace "Tashi mu je ciki kiyi breakfast din" Mikewa tayi da sauri ta bi bayansa zuwa bedroom din Mami, ya ajiye mata shayin sannan ya koma zai dauko sauran abincin, Mami ce ta shigo parlon, ganin Nihad bata parlon ta sauke ajiyar xuciya, juyawa khalil yayi bayan ya dau abincin ya nufi Bedroom da sauri saboda muryoyin wa enda yake ji, Mami ta zauna parlon har Hajiya Amina ta karaso ta zauna, Sai Hajiya Hassana ma ta shigo ta zauna, Hajiya Amina tace "Yanzu tun jiya dama Khalil ya dawo gidan nan aka ki sanar mana? Sai kace wani mugun abu, sannan kuma ya ki zuwa ya gaida mu?" Mami tace "Jiyan ai ba da wuri ya dawo ba" Hajiya Amina tace "Toh ai bai wuce duk mu yi barka ba, mu bama bakin ciki da abun alkhairi, daxu su Farhana ke ce min ya dawo nace to ai haka dama ake so" Hajiya Hassana dake girgiza kafa tace "Yana ina yanzu?" Mikewa Mami tayi ta wuce bedroom dinta, duk suka kalli juna suka ta6e baki a tare, Mami na shiga dakin ta kulle kofar, Khalil na zaune ya sa Nihad a gaba tana shan shayin hannunta da kyar, yana ganin Mami ya mike ɗan yana durkushe a gabanta ne, Mami tace "Ka fito ku gaisa" khalil ya kalleta ya ɗan hade rai yace "In gaisa da wa?" Mami tace "Ka rufa min asiri, minti nawa ne kun gaisa ka juyo" Ya girgiza kai yace "Aa kiyi hakuri Mami, wallahi baxan fita ba" kasa cewa komai Mami tayi tana kallonsa, ya koma saman kujera ya zauna yace "Saboda me xan gaisa da su, sanda xan tafi sallama muka yi da su balle mu gaisa yanzu da na dawo, i am sorry Mami i am not going out" Mami sai kallonsa take, can tace "Toh ko bakin kofa ai sai ka tsaya Khalil, kai baka gudun abun magana ko?" Yace "Aa gaskiya bana gudu Mami, i am not moving an inch from here, ita Aunty Hassana dama a shirye nake da ita na dawo gidan nan, she shouldn't dare cross my part" Mami dai duk jikinta yayi sanyi ta kasa ce masa komai, daga karshe Khalil ya tashi ya bude bandaki ya shige, A hankali Mami ta juya ta fita ta koma parlon tana kirkiran murmushi tace "Shiryawa yake, idan ya gama duk xai je ya gaishe ku" Hajiya Hassana ta daga mata hannu ta dakatar da ita da sauri tace "Aa ba sai kin karesa ba Fatima, ai bamu isa ya fito ya gaida mu ba ne, mu a su wa?" Mikewa tayi tana kallon Hajiya Amina tace "Taso mu je Amina" Hajiya Amina ta mike suka nufi kofa Mami ta bi su da kallo har suka fita, Mami ta sauke ajiyar xuciya ta zauna. Daga karshe ta mike ta fita daga parlon nata, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da kayan Mimi, ta shiga dakinta ta ajiye gefen gado tana kallon Nihad tace "Shiga bandaki kiyi wanka yanzu" Khalil dai na zaune yana kallon Mami, Nihad ta tashi ta shiga bandakin, Mami ta fito parlor, biyota yayi ya zauna kujeran kusa da ita yayi kasa da murya yace "Don Allah ki saurareni Mami" Mami tace "Sauraran me xan maka Khalil" Yayi gathering courage xai yi magana aka bude kofa duk suka juya, Farhana ta shigo parlon tana kallon Khalil tace "Yayanmu wai kaje Abuu yana kiranka" Yayi shiru yana kallonta, Mami ta hadiye abu da kyar tana kallon Farhana tace "Ki je yana zuwa" Juyawa tayi ta bar wajen, Mami ta kallesa da damuwa tace "Ka je kaji kiran da yake maka" Khalil bai iya yace komai ba, can ya mike ya fita, slowly yake tafiya har ya isa bangaren Abba, yayi sallama sai da aka amsa masa sannan ya shiga, Abba na tsaye ya shirya alamar zai fita, Khalil yayi ma Aunty Hassana kallo daya ya zauna kasa, a hankali yace "I am here sir" Abba yana nuna masa Aunty Hassana yace "Who is she to me?" Khalil bai iya yace komai ba, Calmly Abba yace "Tambayarka nake" Khalil ya kallesa yace "Ur sister" Abba yace "Good, kasan da haka ka dawo gidan nan baka je ka gaida ita da Hajiya Amina ba" Khalil yayi shiru, Aunty Hassana tace "Aa yaya, uwar ce ta sa shi hakan ba kowa ba, ita ce xata hanasa ya shigo ya gaida mu saboda ba mu isa ba, sannan still mun tashi mun je har can bangaren nata don ganinsa amma kememe yaron nan ya ki fitowa ta wani fito tana karesa, ita Amina da abu kadan ke sa ta kuka muna fitowa ta kama kuka wai ai wannan cin mutunci ne, ni kuma kasan halina bana daukar nonsense shine yasa ma na zo na sameka yanzu, yaron da a haife na haifesa? Sau nawa nake saka ka a gaba ina cewa kayi hakuri ka bar sa ya dawo gidan nan, shine zai dawo ya saka min da haka?" Abba dai yayi shiru yana safa da marwa a babban parlon nasa, Khalil ya jefa mata wani kallo ta gefen ido, Can Abba ya juyo yana kallonsa da kyau yace "Bata hakuri, sannan duk ka bi su bangarensu ka gaishesu kace masu ka dawo" Khalil ya kalleta a takaice yace "Yi hakuri" Daga haka ya mike ya fice daga parlon, Da ido Abba ya bi sa, Anty Hassana ta saki baki ita ma ta bi sa da kallo, Can ta kalli yayan nata xata yi magana yace "Tashi ki je Hassana, xan nemesa anjima idan na dawo" Aunty Hassana ta dinga kallonsa da mamaki, sai ma taga ya nufi wajen takalmansa ya zauna yana kokarin sa wa, tashi tayi daga karshe ta fice daga parlon kamar xata tashi sama, Khalil na fita ya koma bangaren Maminsa, Mami na tsaye tana kallon Nihad dake sa mayafin Mimi da ta amso mata, Mami ta fesa mata turaren hannunta tana kallonta tace "Baki taho da dankunne ba?" Nihad ta girgiza mata kai kawai, Gaba daya in ka kalleta sai ta baka tausayi, duk ta fita hayyacinta, Khalil dake tsaye bakin kofa kallon Mami kawai yake ya ma rasa abinda xai ce mata, lokaci daya jikinsa yayi sanyi don bai san what she is up to ba, Mami ta dauko ma Nihad wani dankunnen gwal mara nauyi ta mika mata tace "Sa wannan" Nihad ta kai hannu a hankali ta amsa tace "Nagode" sannan ta saka dankunnen, Mami ta dau nata mayafin ta yafa a shoulder tana kallon Nihad tace "Mu je" Nihad ta nufi kofar ta bi gefen Khalil ta fita, Mami na isa bakin kofar ya matsa a hankali ya bata hanya, makullin motarta ta mika masa tace "Mu je" Yayi karfin halin cewa "Where Mami?" Mami tace "Amshi makullin a hannuna ko?" A hankali ya kai hannu ya amsa, Mami ta fita Nihad na biye da ita. Har suka fito compound din gidan babu wanda suka hadu da a hanya kamar dai babu kowa gidan, Nihad ta dinga bin compound din da kallo, it's soo beautiful and big, Khalil ya nufi Ride din