Sashe 146
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
07087865788...Aunty Maryam ta kai hannunta saman shoulder din Nihad ta dafata a hankali tana kallonta don har sannan tunane tunane take with shock written all over her, da sauri Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tana girgiza kai tace "Ni ba wanda ya taba gaya min abubuwan nan, ni ban sani ba, you are just telling me now" Aunty Maryam tace "And hope you've realized what i am saying?" Nihad ta gyada kai hawaye na sauka idonta, sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Aunty Maryam tace "Ni ban san bata so na ba Aunty, Lokacin wani saurayina yace iyayensa xa su xo gidanmu shine na gaya mata sai tace min kar in gaya ma kowa har Mumyna, ita da kanta xata je ta gaya ma Abba, na gaya mata da few days aka saki Video dina a internet shine yayi blocking dina" Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonta and she was speechless, Nihad na kuka sosai don sai sannan abubuwan ke dawo mata, sai yanzu ƙwaƙwalwarta ya fahimci abubuwa da dama, Tana kuka sosai tace "Da Abbana ma ya koreni bata ce komai ba" Aunty Maryam ta dafata da sauri tana kallonta da mamaki tace "Ya koreki daga ina?" Cikin raunin murya Nihad tace "Gidanmu, yace baya son ya sake ganina har abada, she was standing at the door bata ce masa komai ba, and she saw me leaving the house" Sai ta kara fashe da kuka sosai, she is so pained, bata ta6a kallon Umma from this perspective ba, ga dai komai vividly a bayyane amma bata ta6a ganewa ba, Aunty Maryam tayi karfin halin cewa "Kina nufin he sent you away from his house?" Nihad ta gyada mata kai tana kuka, Aunty Maryam ta kasa rufe baki, can ta kalleta da kyau tace "Dalilin kawo ki garin nan da Khalil yayi kenan dama?" Sai a sannan Nihad tayi realizing she just said what she's not suppose to say to her, ta dakatar da kukan da take da sauri ta hadiye abu da ya tokareta a throat, ta kalli Aunty Maryam, sai kuma ta fara kame kame "Aa Aunty kawai dama.... Dama, makaranta...." Aunty Maryam da tuni ta ganota tace "Kar ki min karya" Nihad ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, Jikin Aunty Maryam yayi sanyi sosai, wato dalilin kawota Abuja da Khalil yayi kenan? But ai Mami tace mata Abba ne ya bukaci ya dawo kuma, she became so confuse at this point, Can ta kalli Nihad tace "Ya isa haka, ki daina wannan kukan, ki tafi bandaki ki wanke idonki ki kwanta kafin Asuba ya karasa" Nihad ta kasa ce mata komai, Aunty Maryam tace "Tashi" Tashi tayi da kyar tana jan kafa ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito, Aunty Maryam tace "Ki kwanta, kuma bana son ki sake wannan kukan kin ji me nace?" Nihad ta gyada mata kai ta kwanta saman gadon, Aunty Maryam ta mike ta fita daga dakin ta kullo mata kofar. Kwanciyar da Aunty Maryam bata sake yi ba kenan har gari ya waye, lamarin Nihad ya tsaya mata cak a zuciya, taji tausayinta da mahaifiyarta ainun, ta kuma ji mata takaicin wannan baƙin taɓon da aka mata da xai bibiyeta har karshen rayuwarta, this is soo painful, ta kuma tsine ma Umma ta la'anceta yafi a kirga, ta jima bata ji labarin irin wannan zaluncin da aka ma Nihad ba, ta kara tabbatar da cewa kishiya bala'i ce kuma masifa ce. ƙarfe takwas saura ta kira Khalil, yana bedroom dinsa kwance yayi nisa a tunanin da yake, he is so confused and looking for a way out a kan wannan lamarin, gaba daya kansa ya daure on what next to do, ko jiya da daddare sai da Mami ta sake masa magana yayi kokarin ganin Nihad ta amshi admission letter din nata ko gobe ne kar a shiga weekend, idan yaso idan ta amsa ko ranan sai ta bi jirgi ta koma gida, ita dai duk ta damu ace Nihad ta tafi gida, ga Abba a jiyan shi ma yayi masa maganan business din da zai yi a zanzibar, which he will be leaving Nigeria in 2 days time, that is on Sunday, kiran Aunty Maryam ya kara rikita masa lissafi ya mike zaune da sauri yana kallon wayar, Allah ya sa ba wani maganan Nihad tayi mata ba dai, sai da wayar ya kusa katsewa ya daga ya kai kunne, yayi composing kansa yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau, idan baka komai ka taho yanzu ina jiranka" Nan yaji gabansa ya fadi sosai, Ya dake yace "Hope all is well Aunty?" Tace "Nace dai ina jiranka" Yayi gathering courage yace "Toh" Daga haka ta katse wayar, duk da sanyin Ac dake dakin ji yayi zufa na keto masa ta ko ina, he just can't Imagine ace Nihad tace mata ai an daura mata aure da shi, yayi saurin kawar da tunanin don bai ma son yayi, ya sauka daga saman gadon da kyar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito, cikin few minutes ya gama shiryawa ya dau perfumes dinsa ya fesa sannan ya dau makullin motar Mami dake wajensa ya fita, ko part dinta bai tafi ba ya fita zuwa compound, har Khalil ya isa gidan Small mum dinsa ba shi da nutsuwa babu tunanin da bai zo ransa ba, tunda ya san ba wani saiti gare Nihad ba nan da nan zaka bugi cikinta ta bude maka komai, yana parking compound din Aunty Maryam ya kashe motar ya sauka sannan ya nufi parlonta, xuciyarsa na bugawa ya kwankwasa kofar parlon, mai aikin ta bude, ta gaishesa ko amsawa bai yi ba ya karasa ciki ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, sai ga kiran Aunty Maryam a wayarsa ya daga ya kai kunne tace masa ya hauro sama, ya mike yana kallon mai aikin yace "Ke ina bakuwar da take gidan nan?" Da ladabi mai aikin tace "Tana guess room" Direct can ya nufa da sauri maimakon sama da Aunty Maryam tace ya hau, ya bude kofar dakin ya shiga, tana zaune gefen gado daure da zanin da Aunty Maryam ta bata bayan ta fito wanka tana shafa mai, har sannan idanuwanta a kumbure suke don har gari ya waye bata rintsa ba, Umma tayi mugun tsaya mata a rai, bata ta6a viewing dinta from the this perspective ba sai yanxu with the help of Aunty Maryam, she wish ana iya maida hannun agogo baya, wani tsanar Umma kawai taji take ji a ranta idan ta tuna wasu abubuwan da ta sa ta dinga yi a boye, tunda Nihad ta juya da sauri bayan an bude kofa suka hada ido da Khalil ta dauke kai ta ci gaba da shafa man da take a hankali, ya nufota kirjinsa na heaving yace "Kee, me kika gaya ma Aunty Maryam?" Ta ɗan kallesa, sai kuma ta ci gaba da abinda take taki kulasa, jin bata ce komai ba ya hade rai yace "Magana nake maki" Tace "Toh ba ga ka a gidan ba kaje ka tambayeta mana" Sake baki yayi yana kallonta, ganin yanda ya tsaya mata a kai ta mike ta dau cream dinta xata bar wajen ya fixgota ta dawo dab da shi yana mata wani kallo, ta zaro ido tace "Ni wallahi ka kyaleni, ai ba ni kadai xaka tambaya ba ita ma sai ka je ka tambayeta" Khalil ya dinga kallonta sai kuma ya zaunar da ita gefen gadon strictly yace "Ina me tabbatar maki cewa in har kika gaya mata anything pertaining to relationship dina da ke, ko kuma dalilin da ya sa muka zo garin nan tare dake, i have no choice then to divorce you right in front of her, a nan take a gabanta xan sakeki" Nihad ta wani kyabe baki tace "Toh kayi ta saki na mana, dama ni ai ban san ina da wani aure a kaina ba, sannan Alhamdulillah tunda duk iskanci na ba a ta6a ganin ina rungume rungume ba, kawai dama in ka gama sakin nawa ka kai ni tasha ka saka ni a mota in tafi gun dangin mamata tunda ina da su kuma suna so na" Kallonta ya dinga yi babu ko kiftawa, kawai ji tayi magana da Aunty Maryam ya sa mata courage da tayi loosing few days ago, taji ta kara samun kwarin gwiwa sosai, because at least tayi magana da warce ta fahimceta ta yarda da ita, sannan warce ta ganar da ita abubuwan da duk bata sani ba bata kuma ta6a kawowa a kai ba a baya, Tashi tayi ta koma can daya bangaren gadon ta zauna tana shafa cream din a kafa, Wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya kalli screen din sai kuma ya nufi kofa ya fita daga dakin, direct sama ya haura yaga Aunty Maryam zaune parlornta, ta dinga kallonsa ya kasa barin su hada ido har ya karaso ya zauna, yace "Ina kwana Aunty?" Aunty Maryam na kallonsa a hankali tace "Lafiya lau" Sai a sannan yayi karfin halin daga kai ya kalleta, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Ka gaya min gaskiya Khalil, dama saboda ka kawo Nihad garin nan ne ka dawo gida ko da gaske kiranka Abbanka yayi?" Khalil yayi karfin halin cewa "Aunty ai da Abba bai min izinin shiga gidansa ba kema kinsan babu ta yanda xan shiga, kawai coincidentally ne...." Sai kuma yayi shiru ya sauke kansa kasa don bai ma san me xai ce mata ba tunda bai san abubuwan da Nihad ta gaya mata ba, he don't want to say something different, bayan few minutes yaji Aunty Maryam tace "Me ka fahimta game da kishiyar Mamarta tunda kace ka zauna a gidansu" Da sauri Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma yayi kasa da murya yace "A wolf in sheep's clothing, a green snake under the green grass...." Aunty Maryam ta girgiza kai cike da takaici tace "I was shock at Nihad's story Khalil, nayi matuƙar girgiza da labarinta, kishiyar Mamarta bata mata adalci ba, ta cuceta ta gurbata mata rayuwa" Khalil ya lumshe ido ya bude bai dai ce komai