← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 165

Sashe 114

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Nihad tace "Aa Umma ba haka bane gaskiya" Umma tace "Toh shikenan, ina sauraronki zuwa anjima" Nihad tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, Husnah na kallonta tace "Wai me ya faru?" Nihad tace "Aa ba komai, abubuwan da zata kawo min ne take tambayata" Husnah tace "Ohk" Komawa tayi ta kwanta, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta ta daura kan kayan baccinta ta nufi kofa Husnah ta bi ta da kallo har ta fita, Nihad na murda kofar dakin Khalil taji an sa makulli, ta fi minti daya tsaye bakin kofar, can ta juya ta tafi parlor ta zauna, tana fitowa da minti biyar sai ga Husnah ma ta fito ta zauna parlon, jan Nihad ta dinga yi da hira, daga karshe wajen karfe tara Khalil ya fito daga dakinsa, babu warce ya kalla a cikinsu ya fita daga gidan, Husnah na ji ya fita da mota ta kalli Nihad tace "Lallai ke me hakuri ce da har kika kai warhaka da mutumin nan a gidan nan, Dubi fa yanda ya wani zo ya wuce mu ko gaisuwa babu, kai kana talaka da kai kayi ta yin abu isa isa?" Nihad ta kyabe baki tace "Ke ma kika lura da mutum ya zo ya wuce ta nan, ai ni ban ga kowa ba" Husnah ta kyalkyale da dariya tace "Ahh lallai kam" Nihad tace "Tashe mu je ko irish ne mu soya da kwai, ni dai na fara jin yunwa" Husnah ta mike suka wuce kitchen din, har kusan la'asar Khalil bai dawo gidan ba, kiran Umma uku duk sai Nihad tace mata ai bai dawo ba, kiran karshe da Umma tayi mata da ta kara sanar mata har sannan bai dawo ba, Umma tace "To kar ki yarda ki bari Husnah ta bar gidan, don tana tafiya babu ta inda xa mu yi communicate" Nihad ta kalli Husnah da ita dama bata ga alamar xata tafi ba tace "Toh Umma" Labari har da na kauyensu Khalil sai da Nihad ta ba Husnah dake ta kyalkyalewa da dariya har da faduwa kasa, tace "Kice ke kika ga asalin dreba ganin idonki?" Nihad tace "Hmm... I wish xaki ga kauyen nan Husnah, wllh with millons baxa ki yarda kiyi minti sha biyar a garin nan ba, it's hell on earth" Husnah dai sai dariya take, sai ga Naf ta kira Husnah, Nihad da wayar ke kusa da ita tayi saurin dagawa ta kai kunne, Naf na jin muryar Nihad tace "Amma Husnah munafuka ce shine bata gaya mana ba tayi tafiyarta ita kadai" Nihad tace "Wallahi nima ban ji dadin da baku zo gaba daya ba, gashi throughout today I wasn't lonely, muna ta hira da Husnah" Husnah ta fixge wayar tace "Toh ai naga xaku fita ne shi yasa bance maku mu taho ba Naf, amma meye a ciki next time idan xan zo ai sai mu taho gaba daya, ba wani tashin hankali bane" Naf tace "No but like seriously kinsan indai kince mana wajen Nihad xa ki babu abinda xai hanamu binki, kuma banji dadin abinda kika mana ba, yanzu ma kawai xa mu iya tahowa da zully tunda babu abinda muke" Husnah ta dinga cewa Hello hello, daga haka ta katse wayar tace "Ji shegen network din ya dauke" Hirar da take ma Nihad ta ci gaba da yi mata, Nihad tace "Kinga lokaci na wucewa me xa mu ci da daddare Husnah?" Husnah tace "Ni yanzu xan fita in amso wani sako na, ko indomie ce ma ci da daddaren, Hijabi kawai xan sa in je in dawo" Nihad na kallonta tace "Kar fa ki ki dawowa Husnah" Husnah ta zaro ido tace "Me xai hanani dawowa kuwa, cabb ai kamar na dawo kinsan yanda nayi kewar ki kuwa, to a nan ma xan bar wayata, amma kar ki cire min a flight mode har in dawo" Nihad tace "Toh" daga haka Husnah ta sa hijab ta dau handbag dinta ta bar gidan, ko da ta dawo bayan kusan awa daya Nihad ta dinga kallon hannunta ganin ba leda tace "Ina sakon?" Husnah ta ja tsaki tace "Wai ashe sai gobe, shine suka bari naje nayi asaran kudin motata na dawo" Daga haka ta shiga dakin Nihad. Sai after Magrib Khalil ya dawo gidan, Husnah da fitowarta daga wanka kenan ta dauki mai zata shafa ta rike ha6a tace "Dama haka yake yi ya fita tun safe sai dare kamar me siye da siyarwa a kasuwa" Nihad ta kyabe baki tace "Ohk ya dawo ne" Dariya kawai Husnah tayi bayan ta gama shafa cream dinta tace "Ke baxa ki yi wankan bane" Nihad ta mike tace "Zan yi" Daga haka ta shiga bandaki, mikewa Husnah tayi da sauri ta bude kofar dakin tana leka parlor, ba kowa parlon sai leda da ta gani a ajiye na eatry, ta dawo daki ta dau handbag dinta sannan ta fice tana waige waige kamar munafuka ta shiga kitchen ta bude handbag dinta ta dau allura me cike da wani liquid a ciki ta bude murfin syringe din, ta dawo parlor har tana tuntube ta tafi gun ledan ta bude ta ciro drink din kwali da ta gani ta tsira masa alluran ta sama ta juye duk content din ciki sannan ta mayar da shi ledan hannunta na rawa, sbda rudewa maimakon ta koma daki sai ta shige kitchen, ta fi second talatin a kitchen din kafin ta leko parlon a hankali still taga ba kowa da sauri ta wuce dakin Nihad ta kulle kofa ta zura doguwar rigarta ta dau wayarta ta kwanta saman gado tana danne danne tana ɗan murmushi.....
Chapter 114 · 0% Book details