Sashe 4
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
sauka stairs Umma tace "Farooq" ya juyo yana kallonta, tace "Naga kamar so kake ka ja ma kanka bakin jini gun Kakarku da Engineer, sannan nima hakan ya shafeni, kawai so kake ka ja min maganan da ba shi da ranan mutuwa gun tsohuwar nan, don haka kar ka sake tofa komai a kan lamarin nan, ita kanta uwar da ta haifeta taki cewa komai har yanzu, me magana dama daga ni sai kai, kuma a hakan ma haushinmu ake, don Usman ma bai tsoma kansa ba balle a ga nasa, to ba Uba daya ba, ko ciki daya ku ka fito da Nihad ni dai nace ka janye bakinka daga issue din nan domin a samu masalha, daxu Abban naku ma ya kirani wai ya tafi karkara neman wanda xai hadata da, to idan ana son asiri ya rufu ai sai dai hakan dama, to wa xai yarda ya aureta a nan dai cikin gari? don haka nake kara gargadinka, kar ma ka fara cewa a fasa aure" Faruq yace "Karkara kuma?" Umma tace "Ehh nan fa, ko ka ga alamar Nihad xata samu miji cikin gari ba karkaran ba nace, da wannan mummunan abin da ta aikata wa xae yarda nasa ya aureta?" Yace "Ah haba, karkara kuma, noo ba dai karkara ba, waye ya ba Abba wnn muguwar shawaran? Karkara fa kike ce Umma" Strictly Umma tace "Farooq" ya daga kai ya kalleta tace "I am giving u this serious warning, kada ka kuskura ka sake tofa naka a wannan lamarin, kaji abinda nace maka??" Bai ce mata komai ba, tace "To na dai gaya maka" daga haka ta bar wajen ya bi ta da ido.