← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 165

Sashe 165

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

yana danna waya, so yake ya maida Nadeeyah gida kafin ya je inda yake son zuwa, wayarsa dake hannunsa ya fara ring, ya dinga kallon number wanda ke kiransa, ya dai yi picking daga karshe yakai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace "Dama wani aiki ne ya shigo da ni Abuja yau, so gobe da safe in sha Allah xan koma kd, shine nake son inji wani wajen ku ke a Abujan?" Khalil ya sauke idonsa yace "Ohk, maa sha Allah, goben za ka zo kenan?" Farooq yace "No, na gama abinda nake yi yanzu, goben da sassafe nake son tafiya" at first khalil ya rasa abinda xai ce masa, Farooq yace "Hello" Khalil yace "Eh ina jin ka, xan tura maka address din yanzu" Farooq yace "Toh ina jira" Daga haka ya katse wayar, Daga nisa ya dinga kallon Nadeeyah har ta iso inda yake, ta dauke kai tace "Xan tafi gida" Ganin mood din ta yace "What happened Nady? Are you okay?" Ta ki ce masa komai, ya mike yana kallonta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, da damuwa yace "Talk to me plss, me ya faru?" Cikin rawan murya tace "But you neva told me ba kai kadai ka dawo Abuja ba" Yace "Shit... Toh menene tsakanina da warce na dawo da? There is nothing Nady kawai karatu ta zo yi a garin nan, and she have no where to stay shine take zaune gidan nan, bayan nan babu wani abu kuma trust me" Ta goge Idonta tace "Naji, I want to go home" yace "Noo, not in this manner pls, but ta maki wani abu ne?" Nadeeyah tace "Kawai shigowa tayi ta hararemu ta fita babu sallama balle gaisuwa" Khalil yayi wani sigh yace "But you guys shouldn't have taken it personal, she is a sociopath...." Nadeeyah ta tabe baki dai bata ce komai ba, khalil ya kalli wayarsa dake ring da sauri, ganin Farooq ne ya daga yace "Ina tura maka ne" Farooq yace "Ohk" Daga haka ya katse wayar, Khalil yace "Look Ki koma ciki yanzu, i will be having a visitor immediately, idan ya tafi sai muje ki sha ice cream sannan in maida ki gida" Murmushi kawai tayi ta juya ta fara tafiya, yea dama murmushin kawai yake son yaga ta yi which means komai ya wuce kenan, ya sauke ajiyar zuciya ya zauna ya shiga sending ma Farooq address.....

*Nihad* is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence of payment via 07087865788
Chapter 165 · 0% Book details