← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 165

Sashe 64

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

gaisuwan mai gadi da khalil da ke gaisheta, Nihad kuwa tafiya take cike da isa ta nufi entrance din parlor, tayi wani kyau ta kara haske, kana ganinta kasan bata da damuwar komai, ba komai ya haddasa mata kara haske ba sai cream me shegen tsada irin nasu Husnah da take shafawa yanxu, ga sabulu ga shower gel, Khalil ya bi ta da kallo, suna shiga parlor Aminu yayi kasa da murya yace "Kaga yanda tayi wani haske tayi kyau uwa warce ta tafi duniyanci?" Khalil bai ce komai ba, but he really felt sorry for Abba and Mumy, ya jima bai hadu da mutane masu kirki da karamci irin tasu ba, a watanninsa kusan shidda a gidan Abba ya ja sa jiki kamar nasa, ya kai ya kawo yanxu hatta Atm card Abba na basa ya ciro masa kudi wanda ko Habibu baya ba Atm card dinsa, shi ko Abba ya ya6a da hankali nutsuwa da girmamawa irin ta Khalil, ya sha gwadasa ya aikesa ya siyo masa abu sai ya linka kudin sau uku ya basa yace haka ake siyarwa amma in sha Allah sai Khalil ya kawo masa canjinsa, ya gwadasa ta fanni daban daban wanda shi khalil bai ma san yana yi ba, duk gidan babu wanda yake da matsala da warce ta zama second Nihad sai Umma, gaba daya ta dau karan tsana ta daura masa tun da Nihad ta fesa mata yana waya da Nihal, to uban me Nihal dinta xata yi da shi, duk abinda take yi kuma baya damun khalil, Usman ma dai in ya zo basa wani gaisawa, amma Farooq idan yana gari mayar da bakin gate wajen zamansa yake yi sbda Khalil, xaka yi tunanin ya ta6a saninsa, kawai he enjoys gisting with him sbda yana magana kamar wanda yayi ilimi me zurfi, gashi he knows almost everything that's happening in the world wato he is current, suna dadewa sosai suna hira.... Sai kuma Hajiya Inna da takanas sai ta aiki dreban gidansu Hamid ya zo ya kira mata khalil xata aikesa don hankalinta yafi kwanciya ta basa dukiyarta a kan yaran gidan, kuma aiken baya wuce na dari ko dari biyu. Tun da Nihad ta shiga bangaren Mumy bayan ta fito daga bangaren Umma Mumy ke kallonta, ita dai tana xaune tana ta danna waya, Mumy tace "Wani mai kike shafawa Nihad?" Nihad ta daga kai tace "Mumy cream din Aunty Kamila ne tace in dinga shafawa" Mumy bata ce komai ba, bayan few seconds tace "Ina sauran kayanki?" Nihad tace "Mumy Aunty Kamila tace in bar su a can gidanta" Mumy tace "To tashi driver ya kai ki ki kwaso yanxu" Nihad ta marairaice tace "Mumy ni fa ba abinda nake bukata a cikin kayan" Tsawa Mumy tayi mata tace "Baxa ki tashi ba" Tashi Nihad tayi kamar xata yi kuka, sai kuma tace "Toh Ai Aunty Kamilan na nan ki bari idan ta koma gida Mumy" Mumy tace "Ba dai gobe za ku fara lectures ba?" Nihad ta gyada mata kai a hankali, Mumy tace "Toh dama ki tabbatar baki dawo gidan nan ba tare da akwatunan ki ba" Mumy na fadin haka ta wuce dakinta, Nihad ta turo baki ta mike ta fice daga parlon, ita har ta mance yaushe rabon a harareta balle a mata fada sai yau... Washegari bayan ta shirya xuwa makaranta sai da Mumy ta kara jaddada mata kwaso akwatunan ta, har da guntun hawayenta, bayan ta fito compound ta ji ranta ya kara baci da ta tuna cewar shegen mutumin nan ne har yanxu Driver din gidan, kuma ita wllh baxata wani je ta hau adaidaita Sahu ba, tana isa gate suka hada ido da shi don kallon sama har kasa yake mata, wani matsiyacin kallo tayi masa tace "Da bashi ne kake kallona haka?" Aminu dai sai gwaggwale ido yake, Ta wani ja tsaki ta ma gwammace taje ta hau adaidaitan sbda ganinsa kadai na kona mata rai, ficewarta tayi daga gate Aminu yace "Ohh fitina ta dawo ni Aminu, wllh har na manta da ita a duniyar nan" Khalil dai bai ce komai ba. Bayan kwana biyu da komowar Nihad gida tana kwance bedroom din Umma tana bata labarin yanda suka yi da Aliyu jiya da daddare, Umma dake xaune gefen gadon ita ma ta mike da sauri tace "Kice wllh" Nihad na Murmushi tace "Wallahi Umma" Wani guda Umma ta saki tace "Alhamdulillah, Allah na gode maka... Yaushe yace xa su xo?" Nihad tace "Nan da sati biyu" Umma tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, amma in ji baki gaya ma kowa ba?" Nihad tace "Aa ke kadai da Husnah na fada ma" Umma tace "Kin ji ki, wacece kuma Husnah, meye na gaya mata xa a kawo kudin ki? Duniyar nan da ta lalace yanxu ai kowa boye kansa yake, kar ki sake gaya ma kowa" Nihad tace "Har Mumy?" Nihad tace "Aa ba dai kin gaya min ba ai shkkn, ni xan mata magana sannan inyi ma Abbanku magana, amma sai xuwa next week" Nihad tace "Toh Umma" Wani gudar Umma ta kuma saki tace "Allah nagode maka diyata xata xama surkar Janar jikamshi" Dariya kawai Nihad tayi, Umma tace "Toh sai ki kula ki kama kanki kar ki sake kula kowa tunda dai kina da tsayayye yanxu" Nihad tace "Toh, amma Umma yana wani ce min xai rabani da su Husnah" Umma tace "Ahhh!!! shi kuma ya haka??" Nihad tace "Wallahi, kuma ni banga abinda xai sa ya rabani da su ba" Umma tace "Toh ke dai kar ki musa masa ku samu matsala, kiyi ta bin sa duk abinda yace kice to, su kuma ko a hankali ai xa a rabu, ke da kasar waje xa ku xauna? Ko ba haka ba" Nihad tace "Haka yace min" Umma tace "Toh kinga, su Husnah da ba kasar wajen xa su bi ki ba" Nihad tace "Ai shine" Umma tace "Kai amma nayi farin ciki da wannan labarin Nihad, Allah Ubangiji ya nuna na yan baya haka" Nihad tace "Ameen, Umma bari in dauko wayana" Umma tace "Toh je ki dauko" Daga haka ta fita daga dakin. Ko da wasa Nihad bata sanar ma Mumy ba, tana ta sabgar gabanta throughout the week, kuma har tambayarta Aliyun yayi ko ta gaya ma Mumy tace masa eh. Duk da warning din da Umma tayi ma Nihad na kan cewa kar ta sake gaya ma kowa Aliyu xai turo sai da ta gaya ma Farooq, kamar yanda take favourite din Abbanta haka take favourite din Farooq a gidan, a WhatsApp suke chatting ta gaya masa sai ga shi ya sauka ya kirata, tana dagawa yace "Are you serious?" Tace "Ehh ya farooq" Yace "Tohh maa sha Allah, Amma Abba bai sanar min ba" Nihad ta zaro ido tace "Yaya Umma tace xata gaya masa" Farooq yace "Ohk, toh Allah ya kai mu next week din, though xan shigo kano jibi" Tace "Toh Allah ya kai mu" Sallama yayi mata ya katse wayar, Tana komawa saman chatting taga message din Nihal tana congratulating dinta, wato har Umma ta gaya mata, murmushi Nihad tayi tace "Thanks twinny" Washegari da Nihad ta fito xata school khalil ya bi ta da kallo disgustingly as usual, sarai jiya Nihal ta gaya masa xa a kawo kudinta next week ta kuma gaya masa daga familyn da xa a kawo kudin, and he really pity the well reputable family, da shi kansa wanda xai aureta din, ganin irin kallon da yake mata ta tsaya tana kallonsa tace "Wai kai Allah ya tsine maka ne da xaka dinga min wani irin kallo idan kaga na fito? Ko da wani abu da muka hada ne ban sani ba? Toh wllh wllh wllh duk ranan da na sake fitowa ka min kallon walakanci Allah sai na gaura maka mari, kaji har na rantse" Khalil na kallonta yace "Ki mari wa?" Cike da rashin kunya tace "In mareka nace, ko uban waye kai da kake tunanin baxan iya marinka ba? Ni fa wallahi bayan na bar gidan nan na mance an halicce wani mutum me kama da kai a duniya? Toh akan me daga dawowa ta xaka dinga bi na da kallon raini?" Khalil bai ce mata komai ba cause the sight of her is making him feel feverish, ga wani tafarfasa da zuciyarsa yake, jin bai ce mata komai ba ta ja wani tsaki tace "Banza kawai" Daga haka ta fice daga gidan, Aminu dake lekosu ta dakinsa ya fito yace "kaii, Allah ya wadaran wannan yarinya"
Chapter 64 · 0% Book details