Sashe 46
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Yace "Toh" Da sauri ya fita gate din, ta wuce ta gaban khalil xata fita kofar gida ba tare da ta damu da cewa babu gyale a jikinta ba, sai a sannan Khalil ya bi ta da kallo, tana fita waje ta kulle gate din ruf, tana kallon Aminu ta gaya masa pin din tace "Saura kuma kaje ka min wasa da Atm a titi, dama kana dawowa ko tsayawa kar kayi a bakin gate ka kawo min Atm card dina kada aje a min sata" Yace "Toh Hajiya" Daga haka ta bude gate ta shigo gidan, tana tafiya kamar baxata taka kasa ba tana yi tana yatsine fuska ta wuce khalil, juyawa tayi xata kallesa suka hada ido ta galla masa wani shegen harara ta rike kugu tace "Da bashi ne?" Yace "Ke xan tambayi wannan" Buda baki tayi tana kallonsa da mamaki, can ta dawo fuska daure tace "Kace me???" Shiru yayi yaki cewa komai yana kallon sky, tace "Aa in ka isa da ka maimaita ai tunda kai baka da kunya fitsararre kawai" Ya kalleta yace "Me kike son in maimaita wai" Tace "Ban sani ba" Yace "Ohk, amma tunda har kika ga ban saci abubuwan ki masu muhimmanci dake jakarki shekaranjiya ba, ba kuma wani satan da zan maki, ko duk cikin muhimman kayanki akwai abinda kika nema kika rasa, har kwalban nan ban ta6a ba ai" Tayi masa wani kallo tace "Wani kwalba??" Tashi yayi, yayi mika ya nufi gate ya fita ya bar ta nan a tsaye, ta bi sa da wani irin kallo, sai kuma ta juya ta bar wajen. Xama tayi parlor ta jira har Aminu ya kawo mata sakonta da Atm card sannan ta xuba su a fridge ta wuce sama. Har bayan kusan minti talatin Hafsah bata dawo ba, Nihad da har ta gama kwalliya ta kashe dauri ta fito parlor ganin Umma a xaune tana kallon wani film tace "Umma ya fa kirani 30 mins ago yace xa su taso" Umma ta kalleta daga sama har kasa don ba karamin kyau tayi ba, kamar wata balarabiya, atamfar yayi mugun amsar jikinta, ga make up din tayi sa very light, she look so beautiful, Umma ta tabe baki tace "Toh gantalaliyar bata dawo daga kasuwan ba har yanzu, ni ma har na gaji da jira abinda ya sa na xauna parlon kenan ina jiran dawowarta, don ma ai ba wahala cikin lkci kankani xa a gama..." Nihad ta kalli agogo tace "Toh Umma bata tafi da waya ba in kirata?" Umma ta nuna mata wayar a kan kujera tace "Kin ga inda nace ta ajiye wayar don ma kar taje wani yace mata su hadu a wani waje, kinsan gantalaliya ce, opportunity din fita kawai take jira" Nihad ta nemi waje ta xauna ranta a bace, sai kuma ta tashi ta tafi parlon baƙi ta kunna turaren wuta ta fito ta xauna, har bayan wani minti sha biyar din babu Hafsah babu alamarta, Nihad taji kamar ta fashe da kuka, Umma dai is so engrossed a kallon da take a parlon, wayar Nihad ya fara ring ta xaro ido ganin Aliyu ne, ta daga ta kai kunne, yace "Na kusa shigowa layin ku fa... In 2 mins time" Nihad ta mike tace "Ohk toh" Katse wayar yayi, Umma ta kalleta tace "Ya aka yi?" Nihad kamar ta fashe da kuka tace "Wllh Umma babu abinda xai hadani lakada ma Hafsah shegen duka yau, kin dai ga har gashi ya iso bata dawo ba ko, ni yanxu don Allah me xan basa??" Umma ta xaro ido ta mike tace "Haba dai har ya iso?" Nihad ta wuce sama a fusace, make up din fuskarta ne kawai yasa take danne hawayen da yake son ya taru a idonta, Umma ta rike ha6a tace "Amma Hafsar nan anyi yar iska yarinya, shegiya kawai, nan nan kasuwa taje ta dawo amma kamar an aiki bawa garinsu? To ai da na sani na bari ta tafi da wayar, kuma ni ma banyi dubara ba da naji shiru ko kaji ne sai in dafa ayi masa pepper chicken" Khalil na xaune kofar gida da Aminu tare da mai gadin gidan dake kusa da su, Kallon motar da ya shigo layin tun daga nisa yake with full interest, lkci daya ya gane motar from the other day, ya mike ya juya xai shiga cikin gidan, Aminu na tambayarsa inda xa shi yace "Ina xuwa" karo suka kusa ci da Nihad da xata fito gate din ita ma, ya koma baya da sauri, ta hade rai still inhaling his strong enchanted perfume, k'in basa hanya ya wuce tayi.....