← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 165

Sashe 118

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

sauri ta saka takalminta luckily taga lock kawai aka sa ma gate din babu key ta bude ta fice daga gidan. Nihad ta koma dakin Khalil da gudu ta kulle kofar, kan darduma ta gansa sallan ma ya kasa tashi tsaye, ta durkusa nan kusa da gado tana kallonsa kana ganin idonta kasan ta tsorata sosai, har ya idar taga ya fada kan darduman ya kwanta ya kulle ido, ita dai tana ta zaune maganar Husnah na mata yawo a kai, can ta mike a hankali ta nufi bandakinsa, a bude ta bar kofar, bayan ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito da sauri... Tana idar da sallah ta juya tana kallonsa, tashi tayi ta koma inda yake ta duka hucin zafi take ji a jikinsa, ta dinga kallonsa, a hankali ya bude idanuwansa jin ta a gefensa, ta 6ata fuska tace "Toh kuma kace kar in kira Abba" Wayarsa da ta hango gefen gado ta kai hannu ta dauka, yayi karfin halin kwace wayar a hannunta ya lumshe ido, tagumi tayi tana kallonsa, a hankali tace "Toh ni ya zan yi?" Tana ta zaune gefensa har gari ya waye gaba daya, tun da ya amshe wayarsa a hannunta bai sake bude idonsa ba, duk da baccin da take ji amma bata yi ba tana gefensa a zaune, lkci daya taga ya yunkura ya mike zaune, ta zaro ido ta koma baya tace "Amai zaka yi" Ya sunkuyar da kansa bayan few minutes ya koma ya kwanta ya kulle ido, a hankali ta kai hannu forehead dinsa taji har sannan da xafi, ya bude ido yana kallonta, tace "Toh safiya yayi yanzu ka bani wayar in kira Abbana" murya can kasa taji yace "Dauko takarda da biro" Tace "Takarda da biro kuma??" Jin bai ce komai ba ta mike har ta nufi kofa sai ga ta ta dawo da gudu ta tsugunna kusa da shi kamar xata yi kuka tace "Wallahi Husnah tace min akwai Aljanun dare a gidan nan, duk sun mata duka bakinta ya canxa yayi wani iri"
Chapter 118 · 0% Book details