← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 165

Sashe 136

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

abinda xai ce, Mami ta hade rai tace "Ko baka ji abinda nace bane?" Yayi kasa da murya yace "Mami bata gama ba, bata samu amsan admission letter din ba ma" Mami tace "Toh me kake nufi? Ka gaya min me kake nufi Khalil?" Ya marairaice yace "Mami karki manta gidan babanta fa nake all this while, bai san ni ba ya yarda da ni, yayi accomodating dina na zauna cikinsu for almost 10 months now" Mami tace "Yanxu ya kake son ayi khalil? Me kake son in fada a wannan issue din? Sai kace baka san mutanen gidan nan ba ko mance halinsu ne? wait first... Wai ma ita ce a video din nan ko ba ita bace?" Ya sauke idonsa kasa bai iya yace komai ba, Mami tayi masa tsawa tace "Baka ji na ne?" Cike da karfin hali yace "Ita ce" Mami tace "Nawa ne kudin jirgin, zan tura maka yanzu" Yana girgiza kai hankali tashe yace "Mami mun yi magana da mahaifinta kan cewa ta zauna nan gunki har ta karbi admission letter din tunda bai fito ba, Mami we can't repay him this way, he is one of the nicest person i have met in life, kawai ka haifi yaro ne baka haifi halinsa ba, but her mother and father are down to earth, sun min abinda baxan mance su a rayuwa ba, sannan Mami duk yaran gidan mahaddatan qur'ani ne, kawai dai ita...." Sai kuma ya kasa ci gaba don ya rasa me xai ce, Mami ta fashe da kuka tace "Magana kake son ja min yanzu fisabilillah Khalil? A ina kake son in ajiyeta har ta zauna a gidan nan bayan kana gani duk yan matan sun shaida ita ce a videon nan kuma sun je su idar, sannan har shi Abbanku sae da ya tofa nasa a lokacin da ya ga video din nan kwanaki, he was so disappointed yayi ta addu'an Allah ya shirya mana zuri'a, sai kawai yau a ganta a gidan nan ba kuma kowa ya kawota ba kai?? Kai da kake da ta6o ta ko ina a gidan nan shine zaka kara shafa ma kanka kashin kaji? Check this out khalil, yaushe har Abban naka ya bukaci ka dawo da har zaka dawo tare da wannan issue din? Kayi min gata kayi ma kanka gata ka fitar da ita daga gidan nan kafin wani ya kara noticing dinta bayan kanninka, Plss take her out of this house Khalil"
Chapter 136 · 0% Book details