Sashe 110
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
jiya wllh, har cewa Nihal ta kai maki waya gida nayi amma er nan taki, Amina kuma kinga tunda ana hutu islamiyya take safe da yamma ita ma baxata yarda tayi fashi ba don in aikota wajenki" Nihad ta marairaice tace "Nima babu ta inda xan kira ki Umma" Umma tace "Kina ji na?" Nihad tace "Ina ji Umma" Umma tace "Kullum nayi sallah ina saka wannan tsinannen dreban a addu'a kan cewa Allah Ubangiji ya rabaki da shi cikin aminci, to sunansa kawai na sani ban san sunan mahaifinsa ba ko uwarsa" Nihad tayi shiru, sai kuma tace "Nima wallahi ban sani ba Umma" Umma tace "Yo ai nasan baki sani ba, ke baxa ki iya dubara irin na mace ba ki tambayesa sunan ya gaya maki, sai kace ba wayayyar Nihad dita ba, ai cikin salo irin na wayayyun mata zaki bi masa har ya gaya maki" Nihad tayi Murmushi tace "Toh shikenan Umma" Umma tace "Yauwa zuwa yaushe xan saurareki?" Nihad tace "Gobe" Umma tace "Amma number waye wannan?" Nihad tace "Na Husnah ne" Umma tace "Au tana can shegen ya bar ta ta shiga kenan" Nihad tace "Wallahi kuwa Umma" Umma tace "To yaushe xata tafi?" Nihad tace "Kamar fa kwana xata yi naga kaya kala biyu a jakarta" Umma tace "Madallah dai dai kenan, kinga gobe sai ki kirani kawai ta wayar nata" Nihad tace "Toh Umma" Daga haka Umma tayi mata sallama Nihad ta katse wayar, dai dai nan taji Husnah tayi wani kara, ta mike da sauri ta fice daga dakinta, Tana fita parlor Khalil na shiga kitchen din, ita ma ta nufi kitchen din da sauri.