Sashe 86
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma tace "Ai ba shi ya haifeki ba da xai hanaki xuwa makaranta, kanki tsaye gobe ma ki shirya kiyi tafiyarki duk inda xa ki ba ma makaranta kadai ba, ki kyaleni da shi kawai xan yi maganinsa" Nihad tace "Toh" Umma tace "Kar ki sake asaran hawayenki a banza, kinji abinda nace maki" A hankali Nihad tace "Na ji" Umma tace "To sai da safe" Daga haka ta katse wayar, mikewa tayi direct ta tafi dakin farooq, luckily ta samesa xai fita Masallaci, strictly tace "Farooq daga yau sai yau in har ba baki kake son in maka ba bana son in sake kara ganin ƙafafuwanka a hanyar gidan Nihad, kuma babu ruwanka da harkarta da abinda take yi, in dai ba so kake in ce maka je ka ka gani, kai ko a waya na haneka da kiranta" Da mamaki Farooq ke kallonta, tace "Ni dai na gaya maka, kana kiranta ko da a waya ne Allah ya isa, balle har ya kai ka taka har gidanta, daga yau bana son magana ya sake hadaka da ita ko a ina kuwa" Tana gama fadin haka ta juya fuuu ta fice ya bi ta da kallo, a parlor ta tadda Amina xata fita, tace "Ke kuma ina xa ki?" Amina tace "Umma kati xan amso" Umma tace "Ban hanaki fesa turare haka ba idan xa ki fita? Kuma ba nace maki wannan hijabin bana son kina sa shi ba? Meye amfanin hijabi da xai dinga nuna surarka? Maza koma ki dau wani hijabin" Amina ta juya tace "Dama kyautar da hijab din xan yi Umma, kawai bana son daukan gogagge ne shi sa na sa shi yanxu" Umma tace "Maxa ki bayar idan ba haka ba in kona, bana son sake ganin ɗan iskan hijabin nan a gidan nan" Amina ta juya ta koma daki, Umma ta wuce ɓangarenta. Karfe tara da wani abu Nihad ta gama shirinta xata kwanta, har sannan taki daina kukan maganganun da Khalil ya gaya mata, wai er titi, sannan har da cewa tayinta Abba ya basa, takaici kamar ta hadiye xuciya, can ta mike ta fita daga dakin nata, a parlor ta gansa xaune yana kallo, tana harararsa tana huci tace "Ba dole ka sa tv a gaba ba tunda babu a house" Shi dai bai ko kalleta ba, tace "Kuma da kake cewa Abbana tayina yayi maka, in ka cika ɗan halas ka sakeni yanxu yanxu mana..." Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta maka masa wani harara tace "Idan kuma baka da takarda da biro ni ina da su" Bayan few seconds yace "Ohk ashe dai kinsan da aurena a kanki?" Ta wani kyabe baki tace "Oho dai" Ya gyada kai yace "Kar ki damu akwai lokaci, kawai mu jira lokacin, ina son sai sanda kika fahimci ni ba sa'an aurenki bane sannan xan sake ki...." Tace "Aikin banza kenan, yanxu ya kamata ai, don tun yanxu nasan ni ba class dinka bace, kuma baxan ta6a xama class dinka ba" Khalil bai sake tanka ta ba, ta juya fuuu ta koma ciki, wayarta ta dauka a karkashin pillow tayi dialing number Aliyu, amma ta kasa samunsa sbda ba shi da number, Naf ta kira tace "Naf don Allah ki kira Aliyu kiyi mashi sending wannan number nawa yayi saving i want to talk to him" Naf tace "Ohk" Daga haka ta katse wayar, bayan wani lkci Naf ta sake kiran Nihad tace "Nihad na tura masa number taki yace xai kiraki" Nihad tace "Toh nagode sosai" Nihad na kwance tayi lamo kan pillow tana ta jiran kiran Aliyu, sai ga kiran nasa, farin ciki ne ya cikata ta mike xaune da sauri ta daga kiran, a hankali tayi masa sallama, ya amsa yace "How are you?" cikin sanyin murya tace "Alhmdlh" Yace "Are okay?" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace "No" Da damuwa yace "Me kuma ya faru?" Tana girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Baxan iya jure xama waje daya da wannan drivern din ba, Har xagina sai da yayi daxu fa" Aliyu yace "Ya zage ki?" Cikin kuka tace "Ehh, wai ni ya ce ma er titi, er tasha, har da cewa Abbana tayina ya basa" Aliyu yace "Shi Drivern?" Tace "Ehh" kasa cewa komai Aliyu yayi, can yace "Wait u mean driver ne ya gaya maki wa ennan maganganun?" Nihad tace "Wallahi" Rai bace yace "Har ya kira ki da er titi?" Cikin rawan murya tace "Haka yace" Aliyu ya fuzar da iska yace "Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki, xan dawo Nigeria soon, and everything will soon come to an end in sha Allah" Tana share idonta tace "Nagode" Yace "Kar ki sake xubar da hawayenki, sai yayi da ya sanin zagin nan da yayi maki wallahi" Nihad tace "Sannan nace ya sakeni ya ki" Aliyu yace "He just have to, cause u are not meant for him...." Ɗan murmushin jin dadi tayi, yace "Are u on WhatsApp?" Tace "Aa xan bude yanxu" Yace "Idan kin bude, ki kirani" Tace "Ohk" Daga haka ya katse wayar, sosai hankalinta ya kwanta da abubuwan da Aliyu ya gaya mata, bayan ta bude WhatsApp din Video call suka yi da Aliyu har kusan karfe dayan dare, tun bayan da Video dinta ya tafi viral sai ranan tayi bacci cikin dadin rai. Cikin dare taji kamar ana daga pillow din da ta daura kanta, ta bude ido da sauri, bata ga kowa ba banda duhu dake dakin, gabanta ya dinga faduwa don da gaske taji kamar ana daga pillow dinta, ta mike xaune tana bin ko ina da kallo duk da duhun dake dakin, hannunta ta kai xata yi switching wutan dakin taji ta daura a kan hannun mutum, wani ihu ta fasa a mugun tsorace xata sauko daga kan gadon taga an kunna wutan dakin haske ya gauraye ko ina, yana jingine jikin bango kusa da bed side drawer, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa a mugun tsorace kuma da mamaki, ya daga pillownta ya dau wayar dake ƙarƙashi, xaro ido tayi ta taho da sauri tace "Wallahi kar ka kuskura ka ta6a min...." Wani mugun kallo yake mata yace "Kar ki matso kusa da ni" Ta fashe da kuka sosai tace "Wallahi ka bani wayata, kaga ba kai ka siya min ba, ba kuma da sisin ka aka siya ba" Kofa ya nufa ta koma gefe tana kuka tana kallonsa har ya fice daga dakin, da sauri ta bi sa dakinsa tana cewa "Wallahi ka bani wayata" Bude kofar bandaki taga yayi tana kallo ya tara ruwa a bucket sannan ya cilla wayar a ciki ya fito ya sa ma bandakin makulli, saboda shock kasa ce masa komai tayi ta tsaya tana kallonsa ko kiftawa babu, bai ko kalleta ba ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa saman gado.... Har gari ya waye Nihad bata yi wani bacci ba, ta ci kuka har ta gode Allah, ta sake tabbatar da cewa bata ta6a tsanar mutum a duniya irin khalil ba, karfe takwas saura taji kamar ana welding a bakin gate, ta mike da kyar ta fito parlor ta tafi kofar fita parlorn, tsaye ta gansa a compound, ga kuma me welder da me canza lock din gate suna ta aiki a bakin gate, juyawa tayi da sauri hawaye cike idonta ta koma dakinta, ta xauna gefen gado tana shessheka, ta shi tayi ta tafi dakinsa ta bude kofar bandakin ta duba bucket din da ya jefa wayarta taga babu wayar a ciki, ta fito ta ga karamar wayarsa a gefen gado, da sauri ta dauka ta fito ta shige dakinta, Call logs ta shiga taga number anyi Saving da Nadeeyah with love Emoji, kallon Number ta dinga yi sai kuma tayi scrolling xuwa kasa taga number Nihal wanda ko jiya ma sun yi waya, shiga tayi taga maganar minti nawa suka yi taga kusan minti goma, dialing number tayi yana fara ring Nihal ta daga, Rai bace Nihad tace "Ban san ke munafuka bace kuma algunguma sai yanxu Nihal, kuma in sha Allahu ke abinda xai sameki sai ya fi wanda ya sameni ki rubuta ki ajiye, don naga kamar farin ciki kike da condition din da nake ciki, banda kina farin ciki da abinda ya sameni wayar me xaki dinga yi da enemy din nan nawa? Me yake gaya maki, me kike gaya masa?" Nihal tace "Haba Nihad, what is this u are saying? Da kinsan wayar da nakeyi da shi da baki kirani kina gaggaya min wa ennan maganganun ba, kema kinsan baxan ta6a farin ciki da bakin cikin ki ba..." A fusace Nihad tace "Babu abinda xa ki gaya min da xai gamshe ni, kuma xan ga ta inda xaki sake waya da shi" Nihal tace "Toh shikenan, amma ki sani ko na kirasa ke nake cewa ya ba waya sai baxai baki ba" Nihad tace "Oho wannan ke da shi ya shafa" Nihal tace "Jibi xa mu yi hutu, and we need to talk idan na dawo Nihad" Nihad bata kuma sauraronta ba tayi ending call din, Yanxu tasan xamanta da kowa a duniya, Abba ne oo, Mumy, Ya farooq, Nihal, duk ashe ba sonta suke ba, kuka sosai ta saki, sai kuma tayi blocking number Nihal a wayar sannan ta bi duk calls din ta goge, Kallon Number Nadeeyah ta dinga yi ganin how special the line is with multiple 2's, can ta ja wani tsaki ta danna masa block sannan tayi deleting shi ma gaba daya a call logs, sai kuma ta tuna cewar she needs to tell Aliyu cewar ya amshe mata waya incase zai yi ta nemanta, dialing number Aliyu ta fara yi, ko digit hudu bata sa ba sai taga number ya fito barau barau amma ba tare da suna ba, still tayi tana ta kallon screen din karamar wayar baki bude da mugun mamaki, to ko dai jiya da ya dau wayarta ne ya kwashe number??? lkci daya ta juya da sauri jin taku, wani irin faduwa gabanta yayi ganinsa a bakin kofar dakin yana kallonta, cikin rikicewa ta ajiye wayar hannunta gefen gadon gabanta na faduwa, shigowa dakin taga zai yi, ta marairaice ta koma can karshen bangon dakin xuciyarta na bugawa tana