Sashe 3
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
edge din gadonta ta kafa ma agogon dake manne bangon dakinta ido, xuwa yanxu kam ta hakura da kukan da take, but she is so weak, har ta mance rabonta da wani abinci, babu wanda ke bin ta kanta a gidan banda Umma dake shigowa dakin nata lkci lkci, she still don't have the courage to go to her mother, Bude kofar dakin aka yi ta daga kai da sauri, Husnah ce ta shigo dakin da sallama fuskarta dauke da damuwa, ta karasa kusa da ita ta xauna gefen ta amma ta kasa cewa komai, Nihad din ma dai bata ce mata komai ba, Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace "Kar ki sa ma kanki wani ciwon kawata, duk abinda ya faru da mutum a rayuwa dama Allah ya tsara hakan, kiyi hakuri da kaddaranki, kiyi hakuri kiyi accepting with good faith" Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad, Husnah da ita ma har hawayen ya cika idonta tace "Pls have faith don Allah Nihad, koma waye yayi maki wannan abun Allah baxai bar sa haka ba, tun a duniya Allah xai bi maki hakkinki, ya saka maki" Nihad ta mike xaune ta fashe da kuka tace "Ji nake kamar in kashe kaina Husnah" Husnah ta rufe bakinta da sauri tace "Kiyi istigifari, who are u not to be tested by Allah?? Kar ki kuma fadin hakan, kowa da irin tasa kaddaran a rayuwa, ki dau naki with good faith nace maki, in sha Allah xaki cinye wannan jarabawan, muna nan muna maki addu'a, Allah ya rufe abun cikin gaggawa a daina yawo da shi a media" Nihad ta share idonta a hankali tace "How will i mend this damage?" Husnah tace "Allah will, ke dai ki ci gaba da addu'a, wllh kawata tunda naga abun nan Allah ya sani baccin kirki for the pass 3 days ban yi ba, amma koma waye yayi mana haka xai ga sakkaya daga wajen Allah, sai Allah ya saka mana" Nihad ta sunkuyar da kai a hankali tace "Kuma fa wai aure Uncle dina da Inna suka ce xa ayi min" Husnah ta xaro ido tace "What?? Aure?? Which of ur uncle are u talking about? Abbansu Hamid??" Nihad ta gyada mata kai, Husnah ta rike ha6a tace "But sorry to say Nihad yanxu duk rashin jin da su Zeenat da Pinky ke yi bai gani ba sai naki? Duk runz din da suke yi babu wanda ya hango nasu sai naki? Lallai kam ance laifi tudu ne, Kawai sbda wani axxalumin yaje yayi posting dinki halve naked shine xa ace xa a maki aure? Wa enda ma aka saki hotunansu fully naked ba ace xa a masu aure ba sai ke da naki nafila ne, Tabdi... to wai wa suka ce xa su aura maki?" Nihad tace "I don't even know, but i am thinking of running away" Husnah tace "Nima nayi wannan tunanin, kada ki wani tsaya a cuceki a...." Bude kofa aka yi duk suka yi shiru suka juya suna kallon kofar, Yaya Farooq ne ya shigo dakin, Nihad sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don bata mance dukan tsiyan da yayi mata shekaranjiya ba, banda ma Umma ta masa jan ido ta kwaceta a hannunsa, Ya wani murtuke fuska yana kallon Husnah cikin daga murya yace "Ke, Uban wa ya baki permission din shigowa gidan nan, ta ina ma kika shigo don uwarki??" Husnah ta mike tana sissinne kai jikinta na 6ari, Ita dai Nihad banda faduwa babu abinda gabanta yake har ta fara kallon bandaki ko can xata shige ta kulle, Ya daka ma Husnah wani raxanannen tsawa yace "Xo ki fita kar in karya ki in karya banza" Jakarta ta dauka ta nufi kofa da sauri har tana tuntube, Tana fita ya doka ma Nihad wata harara yace "Kin ga result din bin ire iren kawayen nan ai..." Cikin rawar murya tace "Yaya ita Husnah ai babu ruwan..." Haureta ya kai kafa xai yi ta kauce, ta fashe da matsanancin kuka dai dai shigowar Umma, Umma na ganinsa, tana tafe hannu tace "Wato duk warning din da na maka bai isheka ba ko Farooq? Duk jan kunnen da nayi maka kar ka sake dawowa hanyar dakin nan watsi kayi da shi sbda ban isa ba ko?? To uban naku ma da ya ga abun nan ko nunata da yatsa bai yi ba balle ya kai mata hannu, kai ko zagi bai hadasa da ita ba, to wai shin ma ina ruwanka farooq? Meye naka? To wllh ka shiga hankalinka ka fita harkarta a gidan nan, ka shiga hankalinka nace, Shi Usman da yake ba mahaukaci bane ai nasiha kadai ya hadasa da ita, tun daga sannan ma a ina ta sake saka sa a ido, abun nan dai naga ba yaki bane, kai iskancin da kake sani ake yi balle a tsawatar maka?? To ahir dinka farooq kar ka kuskura in nuna maka bacin rai na wllh" Ita dai Nihad shessheka kawai take, shi kam banda kallon mahaifiyarsa babu abinda yake, ji yake kamar ya karya Nihad ko xai ji sauki a ransa, juyawa yayi ya fice daga dakin kamar xai tashi sama, Umma ta bi sa da harara, sai kuma ta ja tsaki tace "Rabu da shi, ba kanki farau ba ai" Daga haka ita ma ta fice daga dakin. Bayan magrib Nihad ta dake ta fita dakinta for the first time tun da gari ya waye, part din mum dinta ta nufa, duk gaba daya jikinta a sanyaye yake, ta bude kofar parlon a hankali Mumy na xaune parlon da sisters dinta biyu, tun jiya suke gidan amma ko bin ta kanta su ma basa yi, abun duniya duk ya ishesu barin da suka ga damuwar da yayarsu ta shiga, Nihad dai tunda Umma ta kwace ta a hannun Aunty Jamila rabonta da su sai kuma yanxu, banda faduwa babu abinda xuciyarta ke yi, Mumy ta nuna mata kofa alamar ta fita, kuka ta sakar mata ta xube nan bakin kofar cikin rawan murya tace "Don Allah Mumy kiyi hakuri ki yafe min, wllh i don't know how all this happen, i don't know who did this to me, mumy ba halina bane don Allah ki saurareni" Mumy tace "Fita nace Nihad" Kallon Aunties dinta tayi tana girgiza kai wasu sabbin hawayen na sauko mata tace "Aunty Jamila don Allah ku ce Mumy ta yafe min" Ganin Mumy ta mike, ta tashi da sauri ta fice daga parlon xuciyarta na bugawa, kuka take sosai bata da option ta nufi dakin yayanta farooq, bata tadda shi a dakin ba ta rakube jikin kofa tana shessheka, ba a dau lkci ba ya shigo dakin daga masallaci, yana kokarin kulle kofar ya ganta, kan yace komai ta hade hannunta with tears tace "Ya farooq don Allah ka saurareni, only u will understand and listen to me, wllh i knew nothing about that video, ban san wa yayi min ba, ban san yaushe aka min ba, ban kuma san wanda ya fitar ba" Kuka take sosai, ya daure fuska yace "Shaye shaye kika fara da har baki san when and where aka maki video din ba Nihad??" tace "Believe me yaya Farooq, wllh ban sani ba, yanda ku ka gansa haka nima na gansa" Yace "Na rabaki da bin kawaye barkatai Nihad, na rabaki da yawace yawace da xuwa parties, har night party nasan kina xuwa don Sadeeq saw u, na maki magana kika karyatasa kamar bai san me yake ba, u are just different from every other child in this house, just look at the disgrace u have caused to our family, u have tarnished the reputation of our home, how will i face my frnds da suka sanki, my own blood with such act? Oh no, Subhanallah" Ta dinga girgiza masa kai tace "Don Allah ku yi hakuri yaya, i wish my life can end now because of all this, i regret everything" Xaunawa yayi gefen gado ransa a dagule, ita dai ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Yaya farooq i need one favor from u plss" Yace "U don't deserve that favor Nihad" tace "Plss yaya abu na karshe da xa ka iya min a rayuwa shine don Allah kar ka bari Abba su yi min auren dole, wllh xan iya mutuwa kaga har na gaya maka" Yace "What did ur boyfriend say about the video?" A hankali ta sunkuyar da kai tayi shiru, ya hade rai yace "Tambayarki nake" Cikin rawan murya tace "Yayi blocking dina...." Farooq ya gyada kai yace "Good" ta hade hannunta tace "Don Allah yaya, kasan consequences din auren dole kar ku bari ayi min, na yarda a min ko wani hukunci amma banda auren dole, idan ma xa a ce for the rest of my life baxan sake fita waje ba, sannan babu ni babu karatu har abada i agree but kar ayi min auren dole sbda wannan mistake din nawa, ka taimaka kayi ma Abba magana" Umma ce ta shigo dakin duk suka daga kai suna kallonta, tace "So kike ki kara tunxura Abbanki Nihad? Duk shirun da yayi maki bai isheki ba sai kin tunxurasa, Ba na baki shawaran kar ki ce komai a kan batun auren nan ba, so kike ki fusatar da Abbanki yayi maki abinda bai ta6a maki ba?" Faruq yace "Noo wannan ba magana bace Umma, we don't even know da wanda xa a hadata, ko ma me tayi ai da gatanta and she still have her right, su gani suke auren shine way out, whereas it's not" Umma tace "Toh tunda kai ka haifesu ai sai ka gaya masu way out" Ya girgiza kai yace "Umma idan ma auren ne ba sai a bari komai ya lafa ba, ta yaya abu na xafi xafi a shigo da maganar aure, waye xai aureta? Noo bata yi deserving wannan auren ba gaskiya" Umma tace "Ko ma wa xai aureta wannan ba damuwarka bane sai ka xuba ma iyayenka ido, su ai sun san abinda ya kamata, ko so kake ka nuna masu goyan bayan abinda tayi kake?" Ya dinga kallon Ummar tasa, Mikewa yayi ya fice daga dakin, ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo, sai da suka