← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 165

Sashe 29

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri khalil yace "Ka tambayi Habibu a can garinmu akwai wani likita da ya bude Kemist na siyar da magunguna, na fi shekara takwas ina jire masa shago yana bani wani abu duk wata, Allah ya bunkasa masa shagon sosai, rasuwa Allah yayi masa shine yaransa suka rufe shagon bayan sun bada sarin duk magungunan da ya bari, wannan dalilin ne ma har yasa da Habibu yayi min tayin wannan aikin na taho kano don ina xaune babu abinda nake, don haka babu wani magani da ban sani ba yanxu haka sai abinda ba a rasa ba..." Abba yace "Allah ya rufa asiri.... Yau kuma me ya hadaka da Nihad?" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Bani da masaniyar na mata wani laifin yau, kawai dai abinda na sani saurayinta ya zo zai bani kudi yau da na kai ta babban shago xata yi siyayya, sai na nuna baxan amsa ba, shkkn abinda na sani kenan Alhaji" Abba yace "Kaje xa mu yi magana gobe" Daga haka Abba ya nufi cikin gida, Khalil ya koma gun mai gadi ya zauna letting out a deep breath. Washegari da safe Nihad ta leka window ya fi sau goma wai taga ko driver ya fara harhada kayansa xai bar gidan, amma sai taga ya kai su Sudais da Amina school, kuma da ya dawo taga ya ci gaba da zama bakin gate, kasa samun sunkuni tayi, ta dau wayarta tayi dialing number Inna, yana fara ringing ta daga, tace "Ina kwana inna" Inna tace "An tashi lafiya" Nihad tace "Inna wai jiya ya ku ka yi da Abba da kika xo ne?" Inna tace "Yace xai yi masa koren kare, ai shi bai san haka yake ba, da kyar ma in ya kwana a gidan ki bincika ki ga" Nihad tace "Wani bincike bayan ga mutum can a zaune ina kallonsa" Inna tace "Atoh, Kilan sai yau xai tafi, ai na gaya ma Ibrahim maganganu masu ta6a xuciya jiya, yace min in sha Allahu xai sallamesa, ina jin sai yau din xai koresa don jiya kinga ai dare yayi kar ace mutum bai da imani yayi kora cikin dare" Nihad tace "Sai anjima" Katse wayar tayi ta bude kofar daki ta fito, a parlor ta hadu da Nihal, Nihal tace "Kinsan in two days time xan koma school" Nihad ta tsaya ta kalleta tace "Toh ai baki gaya min ba" Nihal tace "Toh yanxu na gaya maki" Nihad tace "Toh yanxu da Habibu baya nan waye xai kai ki Zaria?" Nihal tace "Ni ma ban sani ba, sai Abba yayi magana" Nihad tace "Don kinga wannan drivern sallamarsa xa ayi yau" Nihal dake ta kallonta tace "Okay" Nihad tace "Ko dai har kinyi shopping din ki?" Nihal tace "Aa probably today or tomorrow, sai yanda Abba yace" Nihad tace "Okay ki min magana sai mu je har da ni" Nihal tace "Okay, baki da lectures yau?" Nihad tace "Toh ko ina da lectures ai babu driver da xai kai ni, but karfe tara nake da lectures" Bata jira cewar Nihal ba ta nufi kofar fita parlon ta fito compound, Backyard din gidan ta nufa kai tsaye gun tsuntsayenta su Saminu na gaisheta duk tayi kamar bata ji su ba, tsaye tayi bata motsin kirki tana kallon cages din birds din da duk suke a bude kuma babu birds din a ciki sai roban abincinsu da ruwa, duk cages din guda hudu a bude suke har na parrot dinta, Dawowa tayi da gudu cikin gida tana kallon Saminu dake shara Shafi'u na watering flowers din gidan cikin tashin hankali tace "Saminu ina tsuntsaye na aka kai min?" Saminu ya mike da sauri haka Shafi'u da yayi dropping watering can din hannunsa, Saminu yace "Suna can cikin kejinsu Hajiya" Ta gwalo ido tace "Wani cage din??" Duk suka nufi inda birds din suke, sai ga su sun dawo suna wuri wuri da ido, Saminu na in ina yace "Wllh Hajiya ko jiya sai da muka xuba masu abinci da ruwa...." Da sauri ta juya ta bar wajen ta nufi gun mai gadi cikin rawan murya tace "Aminu ina aka kai min tsuntsaye na?" Aminu yace "Suna can keji Hajiya" Cikin daga murya tace "Wani Cage din, abinda naje na tarar a bude babu komai ciki" Mai gadi ya mike da sauri yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, babu komai ciki?" Shi dai Khalil na xaune yana danne danne da torchlight phone, Aminu ya nufi inda birds din suke da sauri, Nihad da har kanta ya sara mata ta bi bayansa gabanta na faduwa, can ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo tsakar compound ta rusa wani uban ihu ta daura hannu a ka uwa warce aka yi ma mutuwa, Nihal ce ta fara fitowa a guje ta nufota tace "Nihad what happened?" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Wani yaje ya bude min cage din birds dina duk sun gudu, wayyo Allah na na shiga uku, wllh har sun saba dani Nihal, Parrot din har kiran sunana yake yace good morning" Su Aminu da Saminu dai na can gefe a tsaye sai wuwwurga idanuwa suke, Umma ce ta fito compound din Mumy na biye da ita a baya, Hankali tashe Umma tace "Lafiya Nihad, me ya faru?" Nihad ta nufeta tana kuka sosai ta kamo hannunta tace "Umma wani yayi releasing din min birds dina duk sun gudu babu ko daya" Umma ta saki salati tace "Waye da wannan danyen aikin, yanxu babu ko daya wa ennan tsadaddun tsuntsayen da Abbanki ya siya maki" Nihad na gyada kai cikin kuka tace "Wllh duk sun gudu, bude masu cage din aka yi don su gudu" Mumy dake kallonta tace "Shine xa ki 6ara baki haka ki daga mana hankali Nihad?" Umma ta kalli Mumy tace "Haba Maryam, ko don ba ke kika bada kudin siyan tsuntsun ba, kinsan yanda dabba ke da shiga rai kuwa" Mumy tace "Toh waye ya budesu har suka gudu? Sannan ita me yasa bata xuwa dubasu a kai kai yaushe rabon da taje inda suke" Cikin kuka Nihad tace "Wllh ina xuwa dubasu ki tambayi Aminu, kullum sai naje dubasu" Nihal tace "Toh ko da aka basu abinci ne aka mance ba a kulle cage din ba" Nihad ta durkushe wajen tana kuka kamar ranta xai fita tace "Ni wllh ko ma wa yayi min haka Allah ya isa ban yafe ba, Allah ya tsine ma koma waye, Allah ya isa, shi ma sai an nemasa an rasa wataran yanda na rasa tsuntsaye nahhh" Juyawa Mumy tayi ta wuce cikin gida, Umma ta dagota tace "Ai ba Allah ya isa xa kiyi ba, koma uban wa yayi wannan aika aikan dole a ganosa a hukuntasa, ki bar komai a hannuna kawai" Nihad na shessheka tace "Umma wanda yayi mun haka ya tsaneni ne shi sa yayi haka kuma sai Allah ya tsine masa albarka ya daidaice, Allah ya isana" Nihal tace "Ki daina cewa haka baki san ko..." A fusace Nihad ta mike ta hankadeta har sai da ta kusa faduwa, tace "Shut up plss if have nothing good to say" Bude baki Umma tayi, sae kuma ta kalli Nihal tace "To wuce ciki" Nihal ta ta6e baki ta juya ta koma ciki, Umma ta juya ita ma ta bar wajen, Nihad ta hade rai ganin yanda ma'aikatan gidan ke kallonta, cikin tsawa tace "Uban meye kuke wani kallona munafukai yan iska, ai har da hadin bakin ku aka sakar min tsuntsaye suka bi duniya, to ku sani wllh daga yau sbda ku ni xan dinga shiga kitchen sai in ga d'an iskan da xai xubo maku abinci ya kawo maku, for one week ba ku da abinci wllh a gidan nan tunda har aka sakar min tsuntsu suka gudu" Tana fadin haka ta juya fuuuu ta wuce ciki. Da yammacin ranan Farooq ya shigo gidan daga Abuja, Nihad da abun duniya ya isheta don har sannan Aliyu isn't picking her calls, ga kuma har yanxu bata ga Driver ya bar gidan ba, kuma babu ma wata alamar da ta nuna xai bari, yana nan a xaune tare da mai gadi, ko makaranta bata je ba sbda damuwa gashi har test Husnah tace mata anyi, ta mike daga xaman da take ta yi a parlor ta fito compound jin motar Farooq, tamke fuska tayi ganin Khalil da Aminu sun nufi Farooq, Khalil ya fara basa hannu da ladabi, suka gaisa, farooq dai sai kallonsa yake, Aminu dake ta rawar kafa yana washe baki yace "Ae shine sabon dreban gidan tun bayan tafiyar Habibu, yau kwanansa biyar ina jin a gidan nan" Farooq ya kara kallon Khalil daga sama har kasa, sai kuma yace "Driver??" Sai kuma yayi saurin cewa "Ohk maa sha Allah, ya sunanka?" Khalil yace "Ibrahim" Farooq ya gyada kai yace "Maa sha Allah...." Tuni Mai gadi ya dau jakar Farooq ya nufi cikin gida da shi, Nihad dake tsaye balcony ta hade rai tace "Toh ajiye kayi tafiyarka ko ka aikesa ne??" Aminu ya ajiye jakar ya juya sui sui ya bar wajen, Farooq ya amsa gaisuwan da Nihal ke yi masa ya nufi Nihad yace "What happened Nihad?" Kamar jira take ta fashe da matsanancin kuka, yace "Meye haka?" Cikin kuka tace "Ya Farooq wani axxalumin da baya tsoron Allah ya bude ma tsuntsaye na cage duk sun gudu har parrot din" Bude baki Farooq yayi yace "Garin yaya?" Ta karasa ta rungumesa tana kuka sosai, ta gefen ido khalil ya kalleta kafin ya juya ya bar wajen, Farooq ya dago kanta yace "But how did it happen" Tace "Kawai yau da safe naje basu abinci naga ba komai cikin cage din" Yace "Ow that's bad, bari anjima sai mu je ki siyo wasu" Ta marairaice tace "But how will d parrot get to know me just as the old one?" Yace "Yanda wancan din ya sanki sabon ma haka xai san ki" Daga haka ya kama hannunta suka shiga gidan tana share idonta. Bayan ta amshi nata tsaraban da farooq ya kawo mata ta wuce sama xuwa dakinta, wayarta ta dauka ta sake kiran Inna, yana fara ring Inna ta daga, Nihad tace "Inna har yanxu fa driver din na nan
Chapter 29 · 0% Book details