← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 165

Sashe 74

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wannan kalmar gwara a nuna mata bindiga kawai a harbeta, Aunty Jamila bata damu da kukanta ba ta bude cup din da ta gani a rufe ta ga shayi ne a ciki, tace "Me kika ci yau?" Ta girgiza mata kai hawaye caba caba a fuskarta tace "Ban ci komai ba" Aunty Jamila ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta fada kan gado tana rera kuka, Khalil na ganin Aunty Jamila ya mike yace "Za a dauko maki wani abun ne Aunty?" Aunty Jamila tace "Aa, so nake ko shinkafa da miya ne a samu a dafa, inji akwai kayan miya a gidan?" Yace "Aa xan fita in siyo yanxu" Aunty jamila tace "Toh shkkn" Daga haka ta shiga kitchen don daura ruwan shinkafa, Nihad ta hadiye kukan da take ta jawo jakar Aunty Jamila ta zuge zip din, Wayarta ta ciro tayi dialing number din Nihal, sai ga number ya fito da suna, aika kiran tayi ta kai kunne, Nihal na dagawa tayi sallama hade da cewa "Ina yini Aunty?" Nihad ta wani kyabe baki tace "To ni ce nan ba ita ba" bata jira Nihal ta saurari Nihal ba tace "Kin ga Number Husnah xa ki turo min ta nan yanxun nan ba wani magana na kira ki min ba" Nihal tace "Ke me xa ki yi da number Husnar nan ne?" Nihad tace "Wannan bai shafe ki ba, kawai ki turo min abinda na tambaye ki" Magana Nihal take amma Nihad ta katse wayar kawai, ba a wani dau lkci ba sai ga number Husnah ya shigo wayar Aunty Jamila, Nihad ta mike da sauri ta tafi gun jakarta ta bude ta dauko biro da jotter, A hankali ta dawo ta zauna sbda har sannan bata gama dawowa dai dai ba tana dan jin jiri, bayan ta kwashe number ta tura takardan cikin pillow case dinta, sannan tayi dialing number Husnah, yana fara ring Husnah ta daga, Nihad tace "Ni ce Husnah" Husnah dake cikin kasuwa ta nemi wani shago ta shiga da sauri ta zauna tace "Nihad ina ta kiran wancan layin da kika kirani da shi jiya naji kamar anyi blocking, line busy kawai yake sa min, har dare ina trying wllh, to ni kuma na rasa ta inda xan sameki" Nihad tace "Ai wayar wancan wawan yaron ne, wato blocking din ki yayi ko?" Husnah tace "Wallahi kuwa, wai yanxu kina nufin daga ke sai shi a gida daya?" Nihad ta fashe da kuka tace "Wallahi the thought of this na sa inji kamar in kashe kaina Husnah" Husnah tace "Ki kashe kanki a kan wa?? Aa wallahi turo min address din gidan yanxu" Nihad tace "Toh ai ban san ko ina ne nan din ba, amma bari in kira Umma in tambayeta" Husnah tace "Toh maza kirata ko ki turo min numberta ni in kira" Nihad tace "Toh" Katse wayar tayi ta hau kiran Umma, yana fara ring Umma ta daga, Nihad tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Jamilan na can kenan yau?" Nihad tace "Ehh" Umma tace "Toh anjima Amina na nan xuwa maki da wayar anyi rijistan layin" Nihad tace "Toh, Umma su Husnah ne ke son xuwa kuma ni ban san address din nan ba" Umma tace "Gaskiya baxa ki sani ba, kinsan me xai faru?" Nihad tace "Aa" Umma tace "Kice kawai su taho nan gida sai su biyo Amina tunda ita ta san gidan" Nihad tace "Toh Umma" daga haka Nihad tayi mata sallama ta katse wayar, ta kira Husnah ta sanar mata yanda suka yi da Umma, Husnah tace "Hakan ma yafi sauki wllh, turo min number Aminar" Nihad tace "Toh, amma kar ki kira layin nan na kanwar Mumy ce" Husnah tace "Toh shkkn, kawai sai mun zo anjiman" Nihad tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, tayi deleting duk calls din da tayi ta goge message da tayi ma Husnah na number Amina, sannan ta mayar da wayar cikin jakar. Bayan la'asar Aunty Jamila ta gama girka shinkafa da miyan, A plate ta xubo ma Nihad ta fito parlor tana kallon khalil tace "Ga can abincin an gama" Yace "Toh sannu da aiki Aunty, Mun gode" Dakin Nihad ta wuce ta ajiye abincin a kasa, Nihad ta fito daga bandaki daure da towel, ta xauna gefen gado tana kallon Aunty Jamila tace "Sannu da aiki Aunty" Aunty Jamila tace "Yauwa sannu, kiyi maza ki ci abincin" Nihad tace "Toh nagode" nan ko ta rasa ta yanda xata tambayeta yaushe xata tafi don bata son su Husnah su zo tana gidan nan, ganin bata da niyyar tashi Aunty Jamila tace "Toh tashi ki fiddo kayan da xa ki sa mana" Nihad ta mike ta bude jakar ta dauko riga da skirt, bayan ta shafa mai ta sa turare sannan ta sa kayan, Aunty Jamila ta dauko abincin ta mika mata, amsa tayi ta fara ci, gaba daya taji bakinta babu dadi tura abincin kawai take, Aunty Jamila ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idar da sallah tace "Aunty ke baxa ki ci abincin ba?" Aunty Jamila tace "Aa na ci abinci kan in fito gida" Nihad bata kuma cewa komai ba, Aunty Jamila tace "Toh ni xan tafi Nihad" Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve don abinda take ta jiran ji kenan ganin hudu da rabi yayi tasan kilan ma su Husnah na hanya yanxu, Aunty jamila tace "Ki bude kunnenki ki saurare abubuwan da xan gaya maki da kyau" Nihad ta sauke idonta a hankali tace "Ina ji Aunty" Aunty Jamila tace "Ki nutsu ki dawo hankalinki, kinga wancan mutumin dake parlor??" Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya har hawaye ya cika idonta tun bata ji abinda xata ce ba, Aunty Jamila tace "Toh mijinki ne shi yanzu...." Nihad ta rushe da kuka tace "Don Allah Aunty ki daina cewa haka, wayyo ni a daina ce min haka gaskiya" Aunty jamila tace "Ba shakka, to rufeni da duka sai in daina ce maki haka, ke ba taimakonki yayi ba da ya rufa maki asiri ya aureki?" Kuka kawai Nihad take, Aunty Jamila tace "Toh wllh idan ba fushin Ubangiji kike son ja ma kanki ba ki bi mijinki kiyi masa biyayya ki zauna lafiya a duniya, naga kamar baki saduda ba har yanzu baki dau darasi daga abinda ya sameki ba, ni iyakar abinda xan gaya maki kenan idan kin ji yayi maki amfani idan kika yi watsi da shi kuwa kuka bai kare maki ba a duniya" Daga haka Aunty Jamila ta mike ta dau mayafinta ta yafa, ta dau handbag dinta, kuka kawai Nihad take ganin ta nufi kofa sai kuma ta mike ta bi bayanta cikin rawar murya tace "Toh Aunty karatuna fa?" Aunty Jamila ta juyo ta kalleta tace "Wannan kuma sai ki tuntubi mijinki ki ji, mu kam ai bamu da iko da wannan, in ya amince sai ki ci gaba" Nihad na girgiza kai tace "Aunty don Allah kice masa ran monda xan tafi makaranta ni dai" Aunty Jamila tace "Ohk ni ce ma xan gaya masa, ashe shkkn iyakar karatunki kenan a duniya in har ni xan gaya masa" Fita Aunty Jamila tayi daga dakin tayi ma Khalil sallama a parlor, ya mike yace "Aunty har za ki koma" Tace "Ehh wllh na bar yara a gida" Yace "Toh bari in ajiye ki" Tace "Aa da kayi zamanka kawai Nagode, ina fita xan samu adaidaita sahu" Yace "Aa bakomai, xan ajiye ki yanxu" daga haka ya dau makullin mota ya fita, sai taji dadin yanda ya karramata sosai, kuma ko ba komai xata samu enough chance tayi masa magana a mota a kan Nihad, Nihad ta bi sa da wani harara, Aunty Jamila ta kalleta bayan ya fita tace "Wa kike harara Nihad?" Kin cewa komai Nihad tayi, Aunty jamila tace "To ki sani yau shine ganina na karshe da xaki yi a gidanki, indai baxa ki kwantar da kai ki zauna lafiya da mijinki ba" Nihad ta fashe da kuka har da bubbuga kafa tace "Ni Aunty ki daina ce masa mijina don Allah, wayyo Allahna na shiga uku" Kofa Aunty jamila ta nufa ta fice daga parlon, sai da suka fita daga gidan Nihad ta koma dakinta tana share idonta, Allah ya kiyaye wannan ya zama personal driver dinta balle kuma wai miji, suna fita ko minti goma ba ayi ba taji ana kwankwasa gate, da sauri ta mike ta fice daga dakin ta tafi compound don ta san su Husnah ne suka iso, tana isa gate din taji muryarsu kuwa, sosai wani farin ciki ya lullubeta amma kuma lkci daya fara'ar fuskarta ya bace da ta ji ta kasa bude gate din, kuma kamar ta waje aka kulle, Naf tace "Gate din ya ki buduwa ne kin bar mu tsaye cikin rana?" Nihad tayi narai narai da ido tace "Wllh kamar ta waje ya kulle" Husnah ta bude baki haka Zully, Naf tace "Amma dai wannan a yan iskan ma A ne shi, ta waje ya kulle gate? To a saboda me? Akuyarsa ya ajiye a gidan yake tsoron kar ta gudu da xai kulle ki cikin gida?" Nihad bata san sanda ta fashe da kukan takaici ba shkkn da gaske kulleta yayi, Husnah tace "Ke kuma matsalarki kenan, to meye na wani kuka" Amina dai na tsaye rike da ledan waya a hannu, Naf tace "Toh wai ina yaje?" Nihad tace "Wai fa Auntyna ya kai gida shine sabida bashi da hankali ya kulle min gate ta waje kamar gidan ubansa" Husnah tace "Kuma wllh makulli ya sa, ni ko har na kagu in ga wannan me ido da kwallin" Nihad ta goge idonta tace "Kawai ku ɗan jira a nan yanxu xa ku ga ya dawo" Haka suka yi ta jira a bakin gate din, ita kuma ta zauna kan dakalin dakin da aka tanadar don mai gadi a compound din, tun daga nesa khalil ke kallonsu a bakin gate din, yayi parking ɗan nesa da gidan, Amina tace "Yauwa gashi can, motar gidanmu ce wannan" Su Naf duk suka kafe motar da ido ana jiran aga fitowarsa amma bai fito ba, Husnah tace "Ji gantalalle ya ki saukowa a motar" Zully
Chapter 74 · 0% Book details