Sashe 15
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da Nihad ta kwara masa ruwan bai dago kansa da ya sunkuyar ba, lkci daya kamanninsa suka sauya, sae kuma dai ya daga kai ya kalleta, Tana hararansa tace "To wllh kaji ka sani, ka rasa aikinka a karkashin mu daga wannan moment din, yau ba sai gobe ba xan sa Abbana ya dau wani sabon driver din ya sallameka, baka yi deserving aiki a gidanmu ba..." Mai fruit din na girgiza kai rai bace yace "Amma baki da mutunci, baki da kirki, baki san darajan da Allah yayi ma d'an Adam ba, kuma uwa uba baki da tarbiya wllh..." Tayi masa wani matsiyacin kallo tace "Kai kuma wa ya sako da kai Malam? Kai a wa xaka sako min bakinka cikin lamarina? Ina ruwanka? Ko xaka tilasta ni in san darajan d'an Adam din ne??" Wani tsaki ta ja tana harararsa, Wani mutumi a wajen ya karbe a fusace yace "Xa ki samu dai dai dake a duniya wllh, ke yanxu irin tarbiyar da aka maki a gidanku kenan? Tir kuwa da tarbiyan gidan nan naku, tir da tarbiyan da iyayenki suka maki, idan haka arxikin ke sa mutane a hanyar halaka Allah ya hanamu..." Nan kowa na wajen yayi mata caaa, ko wanne na gasa mata magana son ransa har da masu xaginta, abun da tayi ya basu mamaki sosai ya kuma ta6a su, barin yanda suka ga khalil yayi shiru yaki ce mata komai, har da masu ce mata arxikin ma sai sun nemesa sun rasa, da surutunsu ya isheta ta ja dogon tsaki tace "Duk ku ji da abinda ya dame ku malamai, bani da ikon hukunta driver din gidanmu aka ce maku, ina ruwanku da abinda na masa banda sa ido irin na mutane" Tana fadin haka ta juya, sai ta kara jin ranta ya wani baci, yanxu ya xata yi da xuwa wajensu Husnah, kwata kwata bata son hawa adaidaita, duk k'uran duniya ya kare ma mutum, kuma ma ai ba girmanta bane taje Tahir guest palace a adaidaita Sahu, bata sake bi ta kan mutanen wajen ba ta tsallaka titi abun ta, bin ta da kallo kawai Khalil ke yi, mutanen wajen sai hakuri suke basa, wani dattijo dake tsaye shi ma wajen a kan idonsa aka yi komai ya dafa khalil cike da jimami yace "Kayi hakuri yaro, rayuwa ce, amma bari in baka shawara wannan aiki ba shine xai kai ka aljanna ba balle ka ji shakkun barinsa, ka ajiye masu makullinsu, da dai wannan axababben walakancin gwara ko dako ne kayi ka ci abinci, balle siffarka bai yi kama da ta rago ba, ga ka namiji har namiji, ka nemi wata sana'ar sai Allah ya dubeka, ni ko duk arxikin duniyar nan xa a tattara min amma a hada min da walakanci to wllh na hakura da arxikin gwara inyi ta xama da talauci na, balle irin wannan walakanci da cin fuskar da yarinyar da aƙalla xaka bata shekaru sha uku ko sha hudu tayi maka a kan titi a bainar nasi babu kunya babu tsoron Allah, sannan babu ladama a tattare da ita, aa gaskiya ka sake duba lamarin nan dai, Allah Ubangiji ya saka maka wannan cin xarafi da cin mutuncin da tayi maka" Wani matashi ne da gidansu ke nan bakin titin ya fito da wata jallabiyarsa yana kallon khalil yace "Ga wannan mu shiga wancan shagon sai ka canxa, Allah ya saka maka abinda tayi maka" Mikewa Khalil yayi ya amshi rigar yana kallon mutumin yace "Nagode sosai" shagon da ya gwada masa ya nufa, duk mutanen wajen suka bi sa da kallo cike da tausayi barin ma da suka ga ya ki cewa komai, ya shiga shagon, me shagon ya basa waje ya canxa kayansa, wayarsa dake aljihunsa ya fara cirowa ya dinga jujjuya wayar kafin ya ajiye gently a saman bench, canxa kayan yayi, me shagon ya taho masa da babban leda don ya linke tasa kayan ya sa a ciki, amsa yayi ya masa godiya sannan ya linke ya saka a ledar yana rike da ledar ya fito shagon, mai shagon ya kalli wayarsa da ya bari kan bench, ya d'an bude ido yana sake kallon wayar sannan ya kalli khalil da har ya wuce, da sauri yace "Malam ka bar wayarka" Dawowa Khalil yayi da sauri ya dau wayar, ya zira a aljihun jallabiyar, yana ɗan murmushi yace "Nagode kwarai" daga haka ya fita me shagon ya bi sa da kallo kamar me naxari. Mumy ce tsaye bakin gate ta dalilin kiranta da aka yi ganin Nihad can tsallake ga jama'a a tsattsaye sun taru an sa ta a tsakiya, Mumy na kallon Nihad tace "Lafiya Nihad, me ke faruwa?" Nihad ta rungume hannunta tace "Mumy ko ba wancan driver din bane, wllh bashi da kunya ko kadan" Mumy tace "Me yayi maki?" Nihad tace "Wai fa Sajida ce tace min tana anguwan nan, dama akwai wani textbook da nake son amsa a wajenta, shine nace ya d'an ajiye ni, can gaba ne ba nisa, shine fa yake gaya min maganar banxa, shi wai baxai je ba" Mumy tace "Sai aka yi yaya?" Nihad na yatsina fuska tace "Shikenan, su kuma wa encan bansan me yasa suka taru haka ba" Mumy tace "Ina drivern?" Nihad ta kalli tsallaken titin ta ga ya fito wani shigo da jallabiya, Kafin ta ce komai Mumy tace "Mu je wajen nasa" Da sauri Nihad tace "Aa Mumy kyalesa kawai, ni ai ban biyesa ba, haka yayi min daxu ma a gidan Baffa, aa kawai dai ki bar sa" Mumy tace "Tsallaka mu je nace, bana son surutu" Nihad tayi shiru ganin Mumy ta tsallaka ta bi bayanta, amma gaba daya she isn't comfortable, Mumy ta nufi driver, yana ganinta yace "Hajiya har kin fito?" Tace "Aa ya sunanka?" Yace "Ibrahim" Tace "Ohk, ya ku ka yi da Nihad?" Gaba daya mutanen wajen kallonsu suke, Nihad dai na tsaye ta ki karasowa ta wani sha kunu, Mumy ta kalleta tace "To karaso mana Nihad" tana tafiya a hankali ta karasa inda suke tsaye da Umma ce baxa ta ji wani shakku ba xata biyo amma Mumy bata da tabbas, Mumy na kallon khalil tace "Ina jin ka" Nihad ta amshe tace "Na fa gaya maki abinda ya faru Mumy, nan nan wajen Sajida xai ajiye ni in amso textbook shine yake min maganar banxa har sa zagina, ni ko biyesa ban yi ba" Mai fruit dake tsaye shi ma ya saki salati yace "Wllh karya take Hajiya, ba haka aka yi ba, ai ina nan a xaune, bokiti guda na ruwa ta dauka ta kwara masa kawai ba laifin tsaye balle na xaune, baki ga ya canxa kaya ba, duk a kan idonmu aka yi komai" Mumy bata bari me fruit ya rufe baki ba ta tsinka ma Nihad mari, Nihad bata gama recover ba ta kuma sauke mata wani, wanda hakan ya ba mutane da yawa dake wajen mamaki, dama ashe ana hukunta 'ya yan masu kudi, hakan ya kuma mugun burgesu, fuska daure Mumy tace "Wuce ki basa hakuri" Nihad da tunda aka haifeta tana jin ba a ta6a marinta ba ta dinga ganin dishi dishi, ta dafe kuncinta, wani tsawa da Mumy tayi mata sai da ya dada hargitsa ta, Mumy tace "Tafi ki basa hakuri nace kar 6allaki a nan" Bata san sanda ta nufesa ba ta tsaya a gabansa hawaye cike idonta cikin rawan murya tace "Kayi hakuri" Shi dai kallon Mumy yayi yace "Hajiya kiyi hakuri duk bai kai haka ba" Mumy ta bude handbag dinta fuska a murtuke ta fiddo dubu biyu ta jefa mata nan kasa tace "Ki tsayar da Tricycle ki kama hanyar gida yanxun nan, kuma ina nan biyo ki a baya, dama don kiyi displaying bad altitude dinki kika biyo ni kenan, xan yi maganinki" Kuka kawai Nihad take tana jin kamar ta kwanta nan kasa tayi ta birgima ko xata ji sanyi, ko damuwa da mutanen dake kallonta wajen bata yi ba, Mumy na kallon khalil tace "Kayi hakuri don Allah Ibrahim, ita kuma xa mu hadu a gida" Daga haka Mumy ta tsallaka ta koma cikin gidan rasuwa. Nihad ta bude jakarta tana kuka sosai ta ciro wayarta tayi dialing number Abba, yana fara ringing Abba ya daga ta kara rushewa da kuka me karfi tace "Abbaa" Sai ta xama abar kallo a wajen, Abba yace "Subhanallah what happen Nihad?" Kin cewa komai tayi banda kuka babu abinda take rera masa, Abba ya katse wayar ya kira Mumy, tana dagawa yace "Where is Nihad?" Mumy tace "What about her?" Abba yace "Ta kirani yanxu tana kuka, and she is not responding to my questions" Mumy tace "Ka rabu da ita, ai muna tare, sai anjima" Daga haka Mumy ta katse wayar. Sai bayan magrib Mumy ta dawo gida, Khalil yayi parking ya sauka daga motar, Mumy ma ta sauka, da ladabi ya mika mata makullinta, ta amsa tace "Nagode, kuma kayi hakuri da abinda yarinyar nan tayi maka ka ji" Ya d'an yi murmushi yace "Ba komai Hajiya, nagode" Juyawa tayi ta shiga cikin gidan, shi kuma ya nufa gun mai gadi. Umma na jin shigowar motar Mumy ta shigo main parlor, Tana tsaye tana jiranta har ta shigo, Umma tace "Kin bani mamaki Maryam, yanxu a kan wani shegen driver xaki kama yarinya a titi cikin mutane ki doka sbda rashin sanin ciwon kai?" Bata ba Mumy space din magana ba ta ci gaba rai a bace, "Wallahi kin ban mamaki da gaske, ke a dole sai kin xama me kirki me mutunci a idon duniya? yanxu menene amfanin abinda kika ma Nihad a bakin titi a kan wani matsiyacin talaka ɗan iska can? To wllh in dai ba Ibrahim ne ubansa ba sai ya bar gidan nan yau, aikinsa ya kare a gidan nan, idan yayi ma Nihad ya ci bulus har kuma da tsaraban mari da duka da ya ja mata to wllh babu er da xai ma hakan a gidan nan ya kwana kalau, ba a haifi Ubansa yace xai ma Nihal ko Amina haka ba, don haka yau ba sai gobe ba xai kama gabansa, mu bama hulda da yan iska, sau biyu kenan duk a yau ta