Sashe 30
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
babu inda ya tafi don ma in gaya maki" A fusace inna tace "Ke raba ni da wani shegen dreba an shigo an kwashe min yan canjina wai barin gidan da nayi jiya da magariba, kowa sai ce min yake ba shi bane, to ni na saci abina koko?" Nihad ta tabe baki ta katse wayarta, sai kuma ta ja tsaki tace "Dama ba a abun arxiki dake..." Da daddare tana dakin farooq dake kallonta yace "Toh sai in ce masa me idan na kirasa?" A hankali tace "Kawai hakuri xaka basa a kan abinda driver din yayi masa" Farooq yace "Ba kince layinsa a kulle yake ba?" Tace "Aa ya ta6a saving numberka a gabana ai, ka tuna sanda ya kiraka da baka da lafiya?" Yace "Oh, ohk" Daukar wayarsa yayi ta kira masa number Aliyu yayi dialing, a kashe suka ji wayar, yace "It's switch off" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ki je kawai, gobe sai in kirasa" Mikewa tayi tace "To sai da safe yaya....."