Sashe 126
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
tayi tana kuka sosai ta nufi kofa Khalil ya ajiye makullin motar dake hannunsa saman kujera ya bi bayanta har suka fita daga parlon, Juyawa Mumy tayi tana share hawayen dake ta zuba idonta ta koma bangarenta, Abba ya shige parlonsa a fusace Umma ta bi bayansa da damuwa. Har suka kai gate Nihad ta kasa daina kukan da take, tun da suka fito dama Aminu ke kallonsu, don duk wanda ke compound din nan ranan sai ya jiyo muryan Abba, Aminu dai ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, a karo na farko ya ji tausayin rayuwar Nihad, xuciyarsa ya karaya sosai, Khalil ya dafa sa a hankali yace "Xa mu yi waya" Daga haka ya fita gate din Aminu dai ya bi su da kallo ya kasa cewa komai, har suka isa titi Nihad bata daina kukan da take ba.