← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 165

Sashe 77

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Then u show ur evidence via👇🏻 07087865788Husnah suka kalli junansu da sauri ganin Khalil ya juya motar xai bar layin, Amina ta dawo fuska a daure tace "Wai wani zai je ya yanko wani makullin" Husnah ta rike kugu tace "Tashin hankali, lallai wannan mutumin dan iska ne, karya fa yake yi wllh, mu din dai ne baxai bude ma gidan mu shiga ba" Nihad ta taso da sauri ta tsaya jikin gate din tace "Me ya faru?" Naf dai ta kasa cewa komai tun da ta bi motar da ido baki bude, Zully tayi wani dariya ta rike ha6a tace "Kan uban can... Amma gayen nan daga ɗan iska sai shi, but don Allah ku baku ji kun kagu kuna son ganinsa ba? It's the gut for me" Nihad dake ta zaro ido ta kasa fahimtar abinda suke cewa tace "Don Allah ku min magana mana, ya dawo ne?" Husnah ta sauke wani uban ajiyar zuciya ta koma bakin flower ta zauna tana girgiza kafa, Naf da wani bakin ciki ya isheta tace "Amma idan ban tara yan sara suka da yan da6a sun ma drivern nan mugun bugu ba ku ce bani bace, don kaza kazansa da uwar me yake takama xae walakanta mu haka da girman mu, wa ye shi xai dinga feeling kansa haka yana fama da talauci..." Tuni Nihad ta fara fahimtar abinda ya faru hawaye ya cika idonta, ita dai ta shiga uku da abinda wannan yaron ke yi mata, Husnah ta kara sauke wani axababben ajiyar xuciya ta mike tace "Nihad mu xa mu tafi, ashe da gasken gaske tsinanne ne mutumin nan sai yau na sake tabbatarwa, wato tantirin ɗan iska ne na bugawa a jarida, har mu zai walakanta ya juya kan mota ya bar mu uwa yan iska a tsaye bakin gate? Who the hell did he think he is" Nihad ta sakar masu kuka tace "Ba ina gaya maku ba kun zata exaggerating nake, ai wallahi zai iya yin abinda ya fi haka, ina Amina?" Amina tace "Ga ni" Nihad tace "Ki kira Umma da wayarki ki gaya mata abinda dan iskan yayi maku" Amina ta fiddo wayarta a jaka ta hau kiran Umma, Umma na dagawa ta larabta mata abinda khalil yayi masu a bakin gate, Umma ta rike ha6a bayan ta gama sauraron Amina tace "Yau ga shegen mutumi, kuna nan har yanzu bakin gate din kenan a tsaye?" Amina tace "Wallahi" Umma tace "Ina wayar Nihad din?" Amina tace "Ya karɓe wai xai ajiye mata" Umma ta wani mulmulo zagi ta lafta mata tace "Uban wa yace ki basa? Wajensa na aiko ki xaki basa waya? To wallahi duk inda xaki nemosa ki nemosa ki amsar min wayata, kaji min doluwar yarinya kawai" Amina ta turo baki tace "To wai ba karbewa yayi a hannu na ba, ni me xan ce masa" Umma ta kara kunduma mata zagi tace "Ubanki ne ya siya min wayar da xa ki ba wani ɗan iska can? Na dai gaya maki kar ki kuskura ki dawo min gida babu wannan ledar wayar, shashashar banza kawai doluwa" Daga haka umma ta katse wayar tana huci, Nihad tace "Ban gane ba, wayar kika basa Amina?" Amina tace "Toh wai ba amshewa yayi a hannuna ba yace xai ajiye maki" Nihad ta kunduma mata zagi ita ma tace "Wallahi maza ki bi sa ki amso min wayata, meye hadina da shi da har xai amsar min waya yace xai ajiye? Munafuki kawai" Amina tace "Ni dai wallahi ku daina min masifa tunda ba ni na mika masa ba" Husnah tace "Toh wannan takadirin ai ko bata basa ba xai iya fizgewa a hannunta, don naga kamar ya ta6a dabanci, ni dai wllh bai walakanta banza yau din nan ba, xai san ya ta6a Clique dinmu..." Naf duk ta fi su shiga takaici a wajen, she really wants to meet with Khalil ya ga karshen rashin mutunci da tijara, Zully tace "Ni anya ma ba shi yaje ya samu Abban yace a basa auren Nihad din ba kawai don ya samu hanyar dinga walakantata?" Nihad na tafe hannu tace "Ai ko da kansa xai tafi ya samu Abban yace masa yayi hakuri ya fasa auren, i am going to make life miserable for him, xai san cewar ni ba sa'ar zama waje daya da shi bace balle uwa uba aure, shi har ya isa ya aureni? Wallahi da wuri wuri zai koma gun Abba yace ya fasa" Husnah tace "Atoh, duk wannan koke koken da kike yau kwana da kwanaki babu abinda xai tsinana maki sai ma 6ata lokacin ki da kike ki ji in gaya maki, yanzu kamata yayi ace kin zauna kin nutsu kin fara nazarin ta yanda zaki fara musguna ma shege, kar ki kuskura ki raga masa daga cikin tijara da iskanci da muka iya a Clique dinmu, In his next life ko million daya xa a dinga basa ya zo gidan masu kudi yayi driving wallahi baxai zo ba, shi din banza shi din hofi" Sosai hudubar Husnah ke shigar Nihad da taji daga wannan moment din ta daina kuka, baxata kara asaran hawayenta ba akan Halilu, sai dai ta fara daukan action a kansa, kuma da ƙafafuwansa xai gudu ya bar mata gidan ya koma kauyensu na har abada, Husnah tace "Kuma gidan nan ko da uban wa yake yawo sai mun shiga gobe, balle daga shi sai talauci yake yawon ma, wallahi kamar mun shiga gobe, Allah ya kai mu goben, kuma ina fatan Allah Ubangiji ya hada mu da shi face to face goben" Nihad ta sauke ajiyar xuciya saboda sosai ta samu kwarin gwiwa, tace "Amina ki ɗan ara min wayarki mana zuwa gobe" Amina tace "Toh ni sai in yi amfani da wanne?" A fusace Nihad tace "In za ki ara min ki ara min malama, banza kawai ba ke kika je kika mika ma wawan can wanda Umma ta baki ki kawo min ba? Dallah bani wayarki ai ba cinyewa xan yi ba" Amina tace "Ban ga xan iya ba, ni islamiyya ma xan yi tafiyata daga nan, duk an bata ma mutum lokaci ansa na makara kawai a banxa, sai da nace ma Umma ni islamiyya xan tafi amma ta ki" daga haka ta juya fuuu ta bar su wajen a tsaye, Husnah tace "Ke rabu da wani aran waya, gobe ni da kaina xan kawo maki waya, screen touch kuwa" Nihad tace "Toh ta yaya, bayan kina ganin abinda yake yi da gidan kamar na ubansa" Husnah tace "Baki yi trusting dinmu ba kenan?" Naf tayi wani Murmushi tace "Ai kamar mun shiga gidan nan gobe idan Allah ya kai mu, ki saurare mu idan mun tashi test" A hankali Nihad tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu" Zully tace "Toh wai ya sunan wannan tatattcen mutumin ne?" Nihad tace "Halilu naji ana kiransa" Duk suka kwashe da dariya Husnah tace "Za mu haliro masa gobe kuwa" Daga haka suka yi mata sallama, tana jin suka shiga motarsu suka bar layin, ta sauke wani ajiyar xuciya ta juya ta koma cikin gidan. Sai bayan magrib Nihad ta ji shigowar Khalil gidan, nan da nan taji bacin ranta ya ninku a kan na da, tana jin sa ya shigo parlor ta mike ta fito parlon, bai ko kalleta ba ya ajiye ledan hannunsa ya zauna saman kujera ya dau remote yayi powering tv, a fusace ta karaso cikin parlon ta fixgo ledan da ya ajiye don a tunaninta wayarta ce, da ido ya bi ta har ta gama bincika ledan ganin fruits ne ta cillar a gefe, tana tafe hannu cike da tsiwa tace "Ka buda kunnenka da kyau ka saurareni, yau ya zama first and last day da xaka sake kulleni a gida idan xaka fita don ni ba akuyarka ko tinkiyarka bace, kuma ka bani wayar da Ummata ta aiko min" Kallon Tv kawai khalil yake, tayi masa wani tsawa tace "Baka ji na ne ina maka magana?" Still bai kalleta ba balle ta sa ran xai amsa, a mugun fusace ta tafi ta kashe socket din gun Tv din gaba daya tana kallonsa tana huci, Khalil ya kalli karamar wayarsa dake ring, dagawa yayi ya kai kunne yace "Idan na gama abinda nake xan kira ki Hajiya" Huci kawai Nihad take tana kallonsa, yana katse wayar ya mike ya nufi bedroom, wani bakin ciki ya kara rufeta ta bi sa da sauri ta shige gabansa tana cewa "Ni ce ma zan dinga maka magana zaka tashi ka bar wajen, to wallahi baka isa ba...." zata cakumosa kamar yanda ta saba ganin kallon da yake mata sai ta fasa kai hannun nata kwalarsa, Cikin kakkausar murya yace "Matsa ki bani waje" Duk da yanda gabanta ke faduwa tace "Baxan matsa ba, ka bani wayata tunda ba kai ka siya ba...." Irin kallon da taga yake mata yasa ta fashe da matsanancin kuka ta durkushe wajen don can kasan xuciyarta a tsorace take da shi, ya bi gefenta ya shige daki abunsa ya kulle kofar. Mikewa tayi tana kuka tana bubbuga masa kofa tace "Ni wallahi ka bani wayata tunda ba da kudinka aka siya ba, ina ruwanka da sakon da aka kawo min da xaka sa hannunka ka amsa" Banza yayi mata, ita kuma bata fasa bubbuga kofar ba, bayan kusan minti biyar taji ya bude kofar sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri amma kuma bata fasa fadan abinda take fada ba, taga ya sa ma dakin makulli ya cire sannan yayi hanyar kitchen ya shiga, bin sa tayi har bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kuka tace "Wallahi idan na maka Allah ya isa sai ya bi ka har generation dinka, ka bani wayana nace" Gas ya kunna ya dau karamin tukunya sabo ya dauraye ya sa ruwa a ciki ya daura saman gas din, bata fasa masa fitsaran da take ba a bakin kofa, ya juya ya ɗan kalleta, ta wani maka masa harara tace "In kuma siyarwa kaje kayi sai ka gaya min in cire rai" Shi dai bai ce mata komai ba ya rungume hannunsa yana jiran ruwan ya tafasa, ta rushe da kuka ta hade kanta da kofa tace "Wayyo Allahna
Chapter 77 · 0% Book details