← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 165

Sashe 34

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

zan samu katin waya?" Aminu yace "Inaa, Hajiya ai sai an fita can supermarket" Tace "Ohk" Da gefen ido ta dinga lekan cikin flowers din dai dai inda ta buya amma bata ga alamar jaka ba, nan hankalinta ya tashi sbda wayarta na ciki, bata san lkcn da ta karasa wajen ba tana kara dubawa da kyau, Aminu yace "Wani abu kike nema ne Hajiya?" Wani shegen kallo tayi masa tace "Toh ina ruwanka?" Khalil dai na ta danna er karamar wayar hannunsa, ta saci kallonsa.
Chapter 34 · 0% Book details