← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 84

Sashe 9

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda ran Baba ya ɓaci sosai ne ya sanya kawai Ya Musbah ya haƙura….
Sannan ya ba shi haƙuri, daga nan ya juya ya nufi hanyar gidansa.
Bai shiga ba!
direct masallaci ya wuce,
ana idar da sallar ɗan uwan Nafi’u ya kawo kuɗin kamar yadda ya alƙawaranta.

Ya Musbah, ji ya yi kamar ya cewa
ɗan uwan Nafi’un kawai ya bar kuɗin ya fasa ranta….
Dan ya san idan ya sa Hannu ya karɓa kuɗin
ya baiwa Baraka
To fa
bai san ranar biya ba,
gashi yana tsananin jin kunyar Nafi’u wanda ya ke bin sa bashin kusan dubu ɗari kuma bai san ranar biya ba…..
Gashi yanzu na ɗan uwansa shima ya fara hawa kan shi.
Dama saboda ya ga na asibitin Mahaifiyar sa ne Shiyasa kawai ya rufe ido zai karɓa……

Kamar Nafi’un ya san me Ya Musbah ya ke tunani.
A hankali ya dafa Abokin nasa wanda suka taso tare tun ƙuruciya ya ce
‘’Ka kwantar da hankalinka.
Kar ka damu!
Ko yaushe ne in ka samu kana iya biya.”

Sai da ya ɗan sauƙe ajiyar zuciya
tukunna a hankali ya sa Hannu ya karɓi kuɗaɗen, waenda ko bai ƙirga su ba ya san ba su fi naira dubu goma ba!
Ya so ace sun ɗan fi haka
da sai ya bawa Baraka dubunta goma ragowar kuma a yi hidimar asibiti da shi…

Godiya Sosai ya yi har sai da ya bawa ɗan uwan Nafi’un kunya ma.
Daganan Mutumin ya yi musu sallama ya burga mashin ɗin sa ya wuce, ya barsu anan tsaye.
Kafin suma su ka juya a tare su ka nufi ƙofofin gidajen su….
Har su ka ƙarasa ƙofar Gidanjen nasu guda biyu..
Ya Musbah tunani kawai ya ke ta yi…
Tausayin sa Nafi’u ya ke ji sosai dan ya san in ba matsalar Baraka ba tou matsalar rashin lafiyar Mahaifiyar su ce ta sanya shi a damuwa haka.

Yana shirin yi masa magana ya ji Ya Musbah ya ce
“Nafi’u kuɗin nan fa Baraka zan bawa‘’.
A ɗan fusace Nafi’un ya ce
‘’Saboda ka zama Mijin ta ce?’’

Ya Musbah, bai ɓoyewa Abokin nasa komai ba haka ya zaiyyane masa abunda ya faru…
Sannan ya ƙara da cewa
‘’Ba wata maganar ƴan sanda,
Biki ne take da shi!
tsabar bala’i wai ankon super za su yi!
Me sunan Baba kan sa ta yi masa kaya masu kyau da tsada sama da kala uku!
Amman saboda
Allah ace wai Mahaifiyata bata da lafiya amma sam Baraka ta kasa mini kara, kwata-kwata ba ta damu ba….’’
Ya ƙarashe maganar hawaye su na silalo masa.

Da kyar Nafi’u ya iya danne fushin sa, gudun kar ya sake tunzura Abokin nasa.
Sai da ya ɗan daidaita kan sa
daga takaicin Baraka, tukunna a hankali ya dafa shi sannan ya ce
Ka yi haƙuri Musbah!
Komai in ya yi zafi to maganin sa Allah.
Tunda ta yi maka haka kuma Baba ya ce a bata to kawai a bata ɗin.
Ita ta sani, in dai duniya ce, dai dai ta ke da ita.
Kawai yanzu matsalar ita ce inda za mu nemo wasu kuɗin.
Saboda nima Wallahi babu a waje na, da ace ina da shi da na baka.
Ka san lokacin biyan kuɗin gida ya yi,
Mutumin nan sam ni baya taɓa ɗaga min ƙafa,
har gara kai ma ya ce
ai ya san baka aiki….
Gashi wannan term ɗin Khairat ta shiga makaranta
shiyasa nima duk na zama a matse, ba ni da shi.”
Shiru ya ɗan yi kamar me tunani kafin ya ci gaba da cewa
‘’kuma kaga yaya na guda ɗaya tak a duniya na tambaya maka shi shima
amma bara muga ko akwai….’’

Da sauri Ya Musbah ya katse shi ta hanyar cewa
“Nafi’u kar ka damu.
Na gode wallahi ban san da wanne Baki zan yi maka godiya ba.
Ba na jin akwai Aboki irinka har yanzu
a duniyar nan in har kuma akwai
tou tabbas ba ku da yawa.
Nagode nagode.
ka kwantar da hankalinka,
bara inje in bata kuɗin.
dole haka zan haƙura in leƙa Innar babu ko sisi!
Idam na je ɗin sai a san yadda za a yi’’.

‘’Ok’’
Nafi’un ya ce, cikin
rashin Jin daɗi.
Kafin ya sake cewa
‘’Nima bara in duba gida,
Idan komai normal sai mu tafi wajen Innar tare…..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*04*

Ba kunya ba tsoron Allah haka Baraka ta sanya Hannu ta amshe kuɗaɗen nan, duk da kuwa ragowar kwallar da ta gani a Idanun Mai Gidan nata wanda hakan ya tabbbatar mata da kuka ya yi!
Dan hatta ga jijiyoyin gaban Kansa sun fito raɗau! Ga kuma farar Fuskarsa itama ta yi jajawur gaba ɗayanta. Ka na ganinsa ka san
yana cikin tsananin tashin hankali.
……
Tana amshe kuɗaɗen ta shige cikin parlournsu mai ɗauke da ɗakuna biyu, dama fitowarta daga banɗaki kenan ta ganshi tsaye da kuɗaɗen yana jiran ta.

Ya daɗe tsaye a wajen, kafin ya samu ya iya jan
Ƙafafuwansa ya juya ya fice daga cikin gidan, gabaɗaya.

Sai a sannan ta bar bakin windown inda ta laɓe tana kallon sa tana mai taɓe Baki! A fili ta ce
‘’Haka kurum in bada kuɗaɗena a kai uwar wani ba tawa ba asibiti, bayan ga biki a gabana….
Idan na biye maka Musbahu naga alamun sai na gagara shiga cikin ƙawayena watarana wallahi.

Da mutunci na da kyalli na ka auro ni
amma iyakar inda ka ajjiye ni da suturun da ka jere mini a lefe ya sanya yanzu ko hamshaƙiin taro idan za a yi ƙawayena basa gaiyyata ta! Yo ina dalili fisabilillahu.’’
Hakanan tayi ta mita ita kaɗai daga ƙarshe ta shiga kasafta mai da me zata siya da kuɗaɗen……

Tun lokacin da suka rabu da Ya Musbah, ‘Baba’ ya ke tunanin ta Ina zai samo kuɗi , duk inda ya duba ya zaga ya zagayo babu hanya!
Hakan ya sanya gaba ɗaya hankalinsa ya sake tashi!!!

A haka suka yi alwallah su ka yi salla shi da Muhsin daganan suka fito daga masallacin suka zauna akan ɗan dakalin ƙofar gidan.

Yana cikin tunani ya ji wasu zafafan hawaye suna zuba akan kyakkyawar tsohuwar Fuskarsa…
Sai da ya faki idon Muhsin wanda ya yi shiruu shima ya sunkuyar da Kansa ƙasa tun ɗazun da su ka zauna
tukunna ya sanya Hannu ya share Hawayen nasa kafin a hankali ya faɗa duniyar wani tunanin na daban ..
<<<<
Yanzu haka, a tsakiyar ƴan uwansa yake!
Babban yayansu
BABA HABU da Matansa guda biyu
Umma DIJE da Umma KULUWA
Umma dije Ƴaƴanta mata uku
Zainab, Hauwa sai Maryam,
gaba d’ayan su sun yi aure.
Sai Umma Kuluwa
tana da Yaro ɗaya Namiji
‘Ya Yusuf’ wanda ya girmi Ya Musbah da shekara ɗaya amma shi bai yi aureba.

Sai ɗayan Yayan nasa
UTHMAN
Wanda kowa yake kiran sa da
UNCLE
Uncle yanada mata uku
Kasancewar yana aiki a banki ya sanya duk ya ɗan fi su rufin asiri
Matarshi ta farko FATIMA
Umma Fati
Yaro ɗaya tak ta Haifa
Ya iliya (yayi aure)daganan ta samu matsala bata sake haihuwa ba
ta biyun sunanta Khadija
Ita kam ko ɓatan wata ma bata taɓa yi ba.
Sai ta ukun Anty RUMASATU
(Anty amarya)
tanada Ƴaƴa biyu mata twins
Shamsiyya da Salaha masu shekaru goma a duniya.

Sai Yayarsa
Anty Umma (Binta), wadda Mijinta ya rasu ta komo gidan da zama
Ƴaƴanta biyu Mata ta farkon sunan ta Fiddausi tana aure a illorin sai autar ta wadda ta ke tare da ita ‘Siyama’
Siyama ta girmi Jidda Manubiya kuma ta bata shekara ɗaya.

Sai shi Baba (MUSA)
Matarshi ɗaya Aminatu (Inna)
Da Ƴaƴansa huɗu!

Na farko Musbahu mai shekaru 27
Sai
Manubiya mai shekaru 22
Sai
Maijiddah mai shekaru sha bakwai
Da auta Muhsin wanda bai ƙarasa rufe shekaru sha ɗaya ba.

Duk a cikin ƴan uwan nan nasa(Baban) da suke zaune tare a gida ɗaya babu wanda zai tambaya kwandala a cikinsu yau ace ya ɗauuka ya basa!

Idan ana maganar asalin rashin haɗin kai
Tou shine definition(ma’anar) rayuwar Baba da ƴan uwansa!.
Babu hassada babu faɗa babu hayaniya a tsakaninsu amma fa kowa na sa kawai ya sani, hatta Anty Umma, kaff cikin yayun nasu Maza babu mai ciyar da ita kuma sunada rufin asiri ba wai babu ba amma sai dai ta ci da kanta ta ci da ƴarta (Siyama)
Da taimakon ƴar sana’ar siye da siyarwar da take yi, sai kuma Yayar Siyaman itama tana taimakawa ba laifi.

A taƙaice dai kowa ta kansa yake yi a gidan…kowa nasa kawai ya sani, sannan babu ruwan kowa da kowa. Yanayin zaman sam babu daɗi. Ga baki ga hanci..compound ɗaya amma idan ba su Manubiyan ba babu me leƙawa ya ga ɗan uwansa idan wani abun ya faru domin a ji ko a ga halin da yake ciki.

Mai ƙananun maganganu, rigima da son haɗa faɗa a gidan Mutum ɗaya ne
‘Kaka Malan’
Wani ɗan uwan Mahaifinsu da Allah bai ba shi haihuwa ba
suka ɗauko suka bashi ɗaki mai banɗaki a cikin compound ɗin nasu.
Wanda shima sai ya yi da gaske tukunna ake kula shi ake zuba masa abinci, dan Kaka Mallan irin tsoffin nanne masu tijara, gulmace-gulmace, shishshigi da zalama.

Su kam ragowar Mutum gidan a tsakanin su babu jita-jita!
Sai dai sam basa tausayin juna,
basa kuma taimakawa juna…
A yanayi da tsarin gidan
‘Idan ɗan uwanka zai kwana bai ci ba!
Babu ruwanka, ba abunda ya shafeka bane ba.’.

Tun suna Yara, su uku. Mahaifinsu ya zaunar da su ya tambaye su ‘abun da kowa ya ke son yi a rayuwa….’

Ƴan uwan Baba (Yayyunsa Maza su biyu) Uncle da Baba Habu suka zaɓi karatu
Shi kuma Baba ya zaɓi Sana’a.

Kamar yadda Mahaifin nasu yayi alkawari kuwa
Karatu har sai da Uncle da Baba Habu su ka ce “sun gaji!”
Shi kuma Baba aka damƙa masa maƙudan kuɗaɗe aka ce ya je ya yi Sana’a.

Sai dai kuma abun nashi kamar sa Hannu!! Dan duk sana ‘ar da ya soma bata albarka!
A haka har jarin na sa ya ƙare tass!!.
Chapter 9 · 0% Book details