← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 84

Sashe 27

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba,
Kaka Mallan ya kalla kafin ya ce
‘’Ka gani ko?
kalli ka ga!!
Wannan ƴar sai ta gagare ka wallahi’’
ya fad’i hakan yana nuna Manubiyan kafin ya d’aura da cewa
‘’Babu yadda ba a yi da kai akan ka aurar da ita ba amma ka nace akan karatun da aka kwad’aita maka tun farko ka k’i yi,shi za tayi.
Ita da take y’a mace wadda ya ci ace yanzu ta yi Yara biyu ko uku ma, amma ka ja mata har ta yi kwantai…
tunda ni dai rabon da in ji sallamar zance da sunan ta har na manta,
ta d’auki shegen girman kai ta azawa kanta bata kula waenda suke zuwa mata ai gashi duk sun gudu, ba fata nake miki ba Amman da wuya ki auru sai ki je ki rungumi littafi.’’
Shiruu kowa ya yi baka jin maganar kowa sai ta Kaka Mallan ta inda ya d’aura da cewa
‘’Duk da ka nuna ban Isa da kai ba dole zan saka baki a maganar Jidda wanda dalilina na biyu kuma shine
ba zai yiu ka tara Yara da kai kanka ku na ta kurmutsa a d’aki a takure kuma kak’i d’aukar shawara sannan ka yi tunanin za mu yi shiru ba.

Ba zan zuba ido Yaranka mata har biyu su tagaiyyara ba.!
Ita Manu yanzu ta riga ta zama sai an had’a da addu’a, shiyasa tun kafin Jidda itama ta yi kwantai na riga na gama yanke shawara kowa ya saurara ya ji..
Nan da sati biyu dama za’a kawo kayan sa ranar Siyama dan haka a tare a kuma rana d’aya Yusuf shima zai bada na Jidda, in Allah ya kaimu nan da wata uku za ‘a had’a a d’aura auren tare da nasu Siyama a mik’a ta d’akinta, in kuma anan cikin gidan ma zai zauna shima sai a ware ma sa nashi fannin.

Sai maganar kud’in Matar senator, Ummaa da Uncle sun bada dubu bibbiyu Habu ya bada uku nima zan bada uku a had’a a bata kai kuma sai ka nemi cikon ka cikata mata, Allah ya rufa asiri.

Akwai mai magana?’’.

Ahankali Anty Umma ta ce
‘’A’a Kaka’’.
Tana mai jin takaici a ranta, ita da take Mace kuma za’ayi auren y’arta, babu wanda a cikin su ya bata ko sisin kwabo, Yayar Siyaman sai ita ne kawai suketa fafutukar komai, hatta lemukan da za’a tarbi bak’i ita ce zata siya, an sakar mata komai an zuba mata ido kuma ta sab ba bayarwar za su yi ba daga nan har akai siyama d’akinta,amma yanzu ita an hura mata wuta sai da ta bada dubu biyu…

A hankali Baba ya ce
‘’Kaka Mallan,Ina da magana’’

Sai da Kaka Mallan ya d’an k’ura masa ido tukunna ya ce ‘’Muna jin ka’’.
Sai da ya fara yin godiyar karo karon kud’ad’en da suka yi masa tukunnna.
Cikin rashin jin dad’in maganar da zai fad’a ya ce
‘’Ka yi hak’uri Kaka, ba wai jayayya zan yi da kai ba amma Ina ganin maganar auren Jidda da Yusuf
gara kawai a barta’’

Ba tare da Baba Habu ya ce komai ba kawai ya mik’e ya fice daga parlourn gaba d’aya.

Cikin fushi Uncle ya kalli Baba ya ce
‘’To ai shikenan, gata nan sai ka kwad’ata ka cinye, amma wallahi idan ta sake janyo magana kar a kuskura a sake involving d’ina a ciki’’.
Daga haka ya juya ga Ya Yusuf wanda ya sunkuyar da kansa yayi shiruuu
ya ce
‘Yusuf dan Allah dan Annabi ka hak’ura da Yarinyar nan, kana da degree d’inka da sana’arka babu gurin Yarinyar da zaka je ta k’i ka’’.

Anty Umma dai bata tanka musu ba hakanan ta jaa Bakinta kawai ta yi gum, tana kallon kowa.

Da dakakkiyar murya Kaka Mallan ya ce
‘’Musa, inaso ka gaya min laifin Yusuf kwara d’aya tak’’.
Ba tare da shakkah ba Baba ya ce
‘’Yusuf bashi da laifi Kaka kawai dai na ga a halin da Jidda take ciki na damuwa da rashin lafiyar Mahaifiyarta bai kamata a yi mata auren dole ba, kuma ni ban shirya aurar da Jidda ba har sai mahaifiyar su ta samu lafiya, InshaaAllah.’’

Sai yanzu Anty Umma ta ce
‘’Ita Jiddan ta ce maka bata son Yusuf d’in?’’

Tun kafin Baba yayi magana Jidda ta yi k’arfin hali da sauri ta ce ’’Eh,Umma’’ a hankali.

‘’Uhm, to ai shikenan’’
Anty Umma ta ce, daganan ta ja bakinta ta sake yin shiru.

Tabbas ran Kaka Mallan ya b’aci dan haka kawai ya ce “kowa ya tashi ya tafi’’
Yanayinsa kad’ai ya sanya kowa ya fahimci tabbas in ba da kyar ba to kuwa sun d’aura gaba kenan da shi da Baba har abada..

Hakanan taro ya watse zuciyar kowa da k’unci, dan shi kansa Baba saboda yaga ba yadda zai yi ne shiyasa yayi magana bayaso ya sako karatu su yi masa chaa amma yanaso Jidda ta fara ko da level one ne ta d’an saka k’afarta a jami’ar tukunna a yi auren, ga kuma damuwar da suke ciki ga rashin lafiyar Inna, abubuwan da yawa!! Ya san dama ba lalle su fahimce sa ba.
Shiyasa washegari ya bi Kaka Mallan anty Umma Baba Habu da Uncle,
dan yana so su sasanta a tsakaninsu su manyan sannan ya fahimtar da su.
Amman sai abun bai yi masa dad’i ba sam dan Anty Umma ce kawai ya samu ta d’an saurare sa ya gama bayanin sa, ta ce
‘Ba komai’ kawai.
Dama ita ƴar i don’t care ce.
Uncle kuwa tun a masallaci ya ce masa yana son ganin su shi da Baba Habu in an fito amma suna fitowa ya shiga gidan da yake parking motarsa ya zari mota yayi gaba gashi ranar lahadi ne bare ace aiki ya je.
Baba Habu kuma ya ce masa bacci zai yi, lokacin siesta d’insa yayi.
Kaka kuwa tun kafin ya k’arasa shiga wajen nashi ma ya kore sa.
Tun daga ranar kuwa kan y’an gidan ya sake tarwatsewa, da farko lamarin nasu rashin had’in kai ne kawai yanzun kuwa abun ya had’a har da jin haushin juna da fushi.
….
Satin Manubiya d’aya da fara zuwa aiki gidan Ammi.
most atimes (mafi yawanci) exams ɗin nata da safe suke yi shiyasa take zuwa gidan tun kafin gari ya fara haske saboda ta samu ta yi ta gama ta tafi on time,ranar na Sir Najeeb ne kawai ta rok’i Ammi,
tun ana i washegari exams ɗin ta ce mata ’Dan Allah ta yi mata hak’uri
10 za ta taso InshaaAllah zuwa 11 za ta iso gidan ta yi aikin nata.’
Allah ya taimake ta a lokacin da ta je ta na neman alfarmar
Mama tana d’akin Ammin
tana shirya mata wardrobe d’inta,ai kuwa tashi d’aya Maman ta saka Baki…
Dan haka ba dan Ammin ta so ba sai dan girman Maman a idanunta ya sanya ta hak’ura ta yardar ta amince…..
Itafa so take ta maidawa su Manubiya rayuwar su living hell (mafi ƙololuwar azaba) amma ta lura Yarinyar ita da k’aninta (Muhsin) kamar waenda ake jona musu charji, duk kalar uban aikin da ta tula musu kafin ace kwabo sun kammala shi tsaf.

A b’angaren Manubiya kuwa sam aiyyukan da Ammi take tula mata basa damun ta, ita babban tashin hankalin ta a gidan ita ce’Mama’, kamanninta da wannan Mutumin sun yi yawa sannan in dai ta kalli fuskar Mama tou sai ta tuno shi kuma indai ta koma gida ta kwanta barci tabbas sai ta yi mafarkin shi maimakon ta yi mafarkin Mama tunda ita ta ke gani,
A’a
Mafarkin Mutumin take yi
kuma kullum kamar sake ingiza mata tunanin sa ake yi.
Hakan ya sanya a ko da yaushe take k’ok’arin ganin ta yi nesa da Mama. Wanda zuwa wannan lokacin Hatta ita kanta Maman ta fahimci Manubiya wasan y’ar b’uya take yi da ita, bata san dalilin Yarinyar na guje mata ba gashi ita kuma har ga Allah Yarinyar ta shiga ranta, sosai………
•••••
Amaryar Daddy tana cika sati biyu da tarewa rana tsaka ya ce ’ta had’a kayanta za su koma main house d’insa,’.
*Ummi*
Mace ce mai sauk’in Kai da fahimta ga hak’uri, shiyasa tun kafin auren ma da ya ce mata ta ajjiye aikinta tashi d’aya ta ajjiye, sam bata yarda ta yi jayayya da shi ba shiyasa yanzun ma da ya ce su koma main house ɗin nasa tashi d’aya ta ce ’’to’’,
Kuma ita har ga Allah bata ji komai ba dan by then (zuwa wannan lokacin) sun saba da Mommy da Ƴaƴanta saboda bata yi k’asa a guiwa ba sai da ta amshi numbers d’in su kaf su ke gaisawa,
sam
bata damu da yadda a ko da yaushe ita take kiran su ba.

Basu samu dawowa ba sai
washegari, dama gado da set d’in kujeru kawai ta yi amma hatta kayan kitchen a gidan ta je ta tarar dan haka aka kunto mata iya gadonta da kujerun
aka zo nan mansion d’in aka kafa mata a side d’in da Daddy ya nuna mai d’auke da parlour mini kitchen dining area da two bedrooms, k’ofar side d’in nata yana kusa da na Kausar na Yasira kuma kusa da na Mommy.

Tare ta zo da Ƴarta Munirat, mai kirki sosai da hankali ga nutsuwa
Ga ta kyakkyawa sosai
doguwa dirarriya black beauty, ga gashi tubarkallah.
Ummi ta so Munirat ta zauna
a d’ayan d’akin gefenta(na cikin fanninta)
amma sai Mommy ta yi insisting
akan itama a ware mata nata d’akin a gefen na su Yasmeen, hakan kuwa aka yi,
aka ware mata d’aki anan side d’in nasu su uku
Ita, Yasmeen sai Yadira
kowa da d’akinta amman suna sharing parlour….

Lamarin Yasir ya ishi Mommy
gashi gidan an dawo kamar komai bai faru ba dan hatta Kausar ta ware sosai ta ci gaba da shiga mutane…
Daddy shima ya d’an sak’k’o yana d’an wasa da yaran
Shi da Mommyn ne dai har yanzu daga gaisuwa shikenan
shima sai in a gaban yaran ne ya ke amsawa amma
Idan iyaka su biyu ne ko kallonta baya yi.
Chapter 27 · 0% Book details