← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 84

Sashe 67

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin katseshi ta ce ’’yi maza ka je shagon
Audi ka karb’o mata madara,
Idan ta ce ’Manu’ to madara take buk’ata.
Bari in je in kawo maka
kud’in”
Baraka ta fad’i hakan tana mai juyawa da niyyar fita.

Shiruu Muhsin ya yi, tana shirin fita ya ce mata ’’A’a fa,bata ma tab’a
cewa Manu ba sai yau!
Adda Manubiya take nufi,
kuma ai yanzun nan muka bata madara ni da anty Aisha.”

Cikin d’an fushi ta ce
‘’Muhsin za ka yi abunda nace ko kuwa??’’

‘’Tam’’
Ya ce mata,
sai kuma ya sake cewa
‘’Akwai madarar da Ya Musbah ya siya mata me yawa a gida, bara in je in d’auko’’.

Shiruu ta yi, kafin ta nufo sa, tana zuwa ta kama kafad’unsa ta ce
‘’Muhsin su ya Musbah sun rufe d’akin naku kafin su tafi, ka wuce ka je ka siyo mata a shagon Audi yanzu-yanzun nan, bara in kawo maka kud’in.
Kana sakani yawan magana, kai na ciwo ya ke yi.”

Ahankali ya ce ‘’tou Anty’’
a ransa yana tunanin nisa da tafiyar shagon audin.
Kamar ya ce mata ‘ba zai iya siyowa a shagon kusa ba?’
sai kuma kawai yayi shiru dan ya san halinta
yanzun in ya cika ja-in-ja da ita tsaf sai ta makesa!
Dan haka ya ja Bakinsa yayi shiru, ya tsaya ya jirata har ta je ta kawo masa naira d’ari ta ce ’’gashi, ka yi sauri’’.
Da ‘’to’’ya amsata, tukunna ya sa hannu ya karb’i kud’in ya fita…har ya kusan kai k’ofa kamar wanda ya tuna wani abun sai kuma ya koma d’akin ya ce ’’Anty in je in kira Anty Aisha? Ta ce idan zan fita in je in kirata, saboda kar a bar inna ita kad’ai.”

Wannan karon cikin fushi sosai Baraka ta yi masa dak’uwa tukunna ta ce’’ ungo naka Muhsin!
Innar ita kad’ai ka gani anan? ni ba mutum baceba?.
Za ka wuce ka je min aike ko sai jikinka ya gaya maka?”

A hankali ya kamo hannun me sunan Baba ya ce ‘’zo ka rakani’’
Daganan ya juya kawai ya fita
ba tare da ya sake cewa komai ba.

Yana fita ta kalli Inna tana raya abunda za ta yi, kafin ta kalli k’ofar da Muhsin d’in ya bi ya fita a ranta tace “sai dai kawai ka dawo ka gani, na san in kana nan tsaf za ka kawo min cikas!
Ba k’aramin aikinka bane ba ma ka tara min jama’a shegen Yaro mai shegen surutu…”
Tana gama fad’in haka ta nufi inda innar take.
…
Tana zuwa ba tare da shayi ko tantama ba ta yaye zanin da aka lullub’ewa innar k’afafu da shi, ta d’auki pillown da ke ajjiye a gefenta ta fita waje…

A nan tsakar gidan da sumintin duk ya farfashe ta yi shimfid’a ta zanin da pillown tukunna ta koma d’akin.

Da kyar, da mugun kyar ta samu ta kinkimi Inna, k’arshema da ta ga baza ta iya ba janta ta yi ta fitar ta shimfid’eta anan tsakar gidan
Inda ta shimfid’a zani ta saka pillow.
Tana ganin lokacin da hawaye suka shiga sintiri a kan kumatun Inna amman ko d’ar Baraka ba ta ji ba!idanunta sun riga sun rufe..
Ita babban tashin hankalinta shine
‘Manubiya ta yi aure kuma da alamun wani wajen za’a tafi da Baba tunda an riga an kama shi wataƙila shikenan ya tafi har abada, ko me ma yayi oho musu!
Dan haka dole dole ta san gidanta Muhsin Jidda da Inna za su dawo kenan da zama’…
Dan haka
Wallahi ita kuma ba za ta yi k’asa a guiwa ba wajen nuna musu ba su Isa ba…tun wuri ma su nemi gurin zama! yau za su yi ta ta k’are!garama idan suka dawo su gani sannan su tabbatar da cewa uwar tasa ma bata da wajen zama a cikin gidan ballantana kuma k’annensa.

Dama tun d’azu a k’ule take….saboda da ya tashi kawo Innar ma ko shawartarta bai yi ba
haka nan kawai sai ganin su ta yi.
Ai kuwa yanzu zai gani kuma zai san itama ta Isa wallahi!! taga alama idan ba nuna masa ta yi ba tou ba lalle ya tuno ‘waccece Baraka ba’.

Hakanan ta yi ta zancen zuci tana huci ita kad’ai!!!.
Ko bi ta kan inna bata sake yi ba, ta fad’a band’akin da ke nan a tsakar gidan tana jin nauyi da zafin da zuciyarta ta yi yana raguwa kad’an-kad’an…..
A ganinta rainin wayon su ya ma yi yawa! A barta taji da hak’urin zaman auren ma da takeyi da shi ba sai an k’ara mata da wani takaicin ba, yau za’a yi ta ta k’are
Wallahi
dan bata tsoron uban kowa a cikin su.
…….
Su Ya Musbah suna tsaye a d’akin da Abbakar ya ke, su Jidda suka shigo. a take wani irin tausayin su ya lullub’e ya Musbah, dan haka ya kalli ya Nafi’u ya ce ’’bara in duba Reception, in ji ragowar bill d’inmu dan a samu a biya…”
Daga haka ya sa kai ya fice…
Sun san su Yash sun biya d’azu amma basu san duka suka biya har da na Abbakar ba.

Yana fita ya Nafi’u ya d’auki wayar Abbakar,
Manubiya ta bud’e musu password d’in shi kuma ya kira maman Abbakar.

Ko mintuna ashirin ba ayi ba kuwa suka k’araso cikin asibitin a hargitse ita da maman Baraka.
A reception suka had’u da ya Musbah wanda yake ta faman sak’a da warwara, sam ya kasa komawa cikin d’akin bayan ya je an ce masa “ai su Yash sun riga sun gama biyan komai’’.

Hangosu ya yi a hargitse suna tambayar wani cleaner, dan haka ya k’arasa ya yi musu iso har cikin d’akin.

Dama shima d’in da kyar suka amsa gaisuwar shi yanzu kuma ko kallon baba da yake kwance ba su yi ba haka suka wuce shi suka d’aga labulen da ya ke tsakaninsu da Abbakar
Inda ya Musbah ya nuna ya ce musu yana ciki…
kawai suka afka ciki.

Shi kuma Ya Musbahn ya tsaya a wajen Baba da ya Nafi’u wanda bai dad’e da fitowa daga wajen Abbakar ɗin ba, yake sanar musu
‘’ su Yashjub sun riga sun biya komai’’
Baba yana shirin yin magana suka jiyo maman Abbakar ta kurma wani irin ihu….

Da sauri su Ya Musbah suka nufi inda suke suna addu’ar Allah dai yasa ba wani abun ne ya samu Abbakar d’in bayan fitowar su ba.

A durk’ushe a bakin gadon suka hangeta tana wani irin masifaffen kuka.
Kafin daga baya ta (maman Abbakar) mik’e ta nufi Manubiya gadan-gadan, tana zuwa ta shak’o ta ta mik’ar da ita tsaye tukunna ta cikata, cikin fushi da kuka ta ce ‘’ai duk ke ce kika janyo komai!
munafuka! muguwa! kawai, haka kurum kin maidamin Yaro kamar wani boyi-boyin ki…’’

‘’Haba mama, baki yarda da
k’addara bane?’’
Ya Nafi’u yayi mata tambayar cikin rashin jin dad’i.

Cikin fushi ta ce ’’ai dama na san ba za ku ga laifinta ba, to wallahi ku jirani a kotu dan ba zan yarda ba sai mun yi shari’a da ku.
Amman kafin nan inaso in ja miki kunne!….
Manubiya in dai har kin haifu cikin Musa da Amina tou kar in sake ganin ki a kusa da d’a na.

Kalli cikin azabar da kika jefa sa da ke da y’an uwanki da iyayenki…masifa ce ku wallahi!!!
shiyasa duk wanda ya rab’e ku sai ya shafa, na yi k’ok’arin nunawa Abbakar ba so d’aya ba ba sau biyu ba amman dayake kin riga kin shanyemin Yaro kalli sai da kika kusan kai shi lahira…’’
Kukan da ya kufce mata ne ya sanya ta d’an dakata, kafin ta sake d’agowa a zuciye ta ce ’’na gaya miki yanzu zan sake maimaitawa ‘in dai kin haifu cikin tsinannun iyayen k…’’

Nufar matar Ya Musbah yayi da niyyar kai mata duka amman sai maman Baraka ta shiga tsakiya ta rik’e sa, zafin zuciyar da ta ciwo sa ne ya sanya cikin rashin sani ya yi cilli da ita, ya sake yin kan maman Abbakar ɗin…

Ganin yana shirin yin b’arna ne yasa ya Nafi’u ya taresa ya ce
‘’Musbahu ka yi haƙuri ka kyaleta ba dan itaba, ka duba fa Abbakar shi ne ya kira su Yashjub, ka rabu da ita, ta ci albarcin d’anta.’’
Daga haka ya juya ya ce mata
‘’mu za mu wuce yanzu.
Ga Abbakar nan, zan dawo in duba shi inshaaAllah zuwa anjima…muna buk’atar mu yi mishi godiya.
An biya duk wasu charges,
abinci kawai zaki dinga basa,
Allah ya basa lafiya.’’
Daga haka ya cewa su Manubiya “su wuce su tafi’’.
Sai da kuwa yayi da gske tukunna shi da Jidda suka samu suka janye Manu dan ta tsaya kawai tana kallon maman Abbakar ne, so take yi ta maida mata da martani amman kuma darajar d’anta ya sanya ta kasa yin magana.

Aikuwa har suka fice maman Abbakar ba ta yi shiru ba…babu kalar zagin da batayi musu ba…
Maman Baraka itama tana tsomo Baki
A cewarta ‘’sirikinta ya hankad’eta, ta fad’i kuma ko
kallon inda take bai yi ba
kamar ba y’a ta d’auka ta basa ba!!!!
‘Saboda shi ɗin d’an marasa tarbiyya ne…shiyasa bai san darajar ta ba’.”

Hakanan Baba ya tsawatar musu yace ‘’kar wanda yace uffan, su rabu dasu’’
dan haka suka tartara yanasu yanasu suka fice bayan ya Musbah ya je ya karb’i magungunan Baba.
K’arfe shida dai-dai suka bar harabar asibitin suka nufi gida.

A gida suka fara tsayawa
suka ajjiye Baba, tukunna Baban ya ce musu “su duka su je su d’auko inna, kar su damu ba komai zai iya zama shi kad’ai’’.

Da ‘’to’’ suka amsa shi, daga haka suka nufi gidan Ya Musbah gaba d’ayansu domin su je su d’auko Innar. ce ’’dalla ni cikan….’’
*MANNUBIYA*
*41*
Chapter 67 · 0% Book details