← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 84

Sashe 66

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyin jiki Baba ya ce’’mutumin nan ya gudu, basu kama shi ba. ku bar ni in aurar da su Jidda tun kafin wani abun ya sake faruwa, na san inshaaAllah idan sunada aurensu darajar aure da kariyar ub…..”
Shiruu ya yi sakamokon shigowar da su Manu sukayi.
cikin nutsuwar su, suka k’arasa suna zuwa wajen ya Musbah ya juya da sauri yace ‘’bara in duba jikin Abbakar!”
Ya fad’i hakan yana nufar labulen da aka saka a tsakanin baba da abbakar d’in.
Doga jin haka ya Nafi’u ma ya biye masa baya.
Ya Musbah na gaba ya Nafi’u na biye da shi a baya yana tafe yana dialing number Aisha dan sai yanzu yaga misscalls dinta birjik, haka suka shiga inda Abbakar d’in yake a kwance.
Suna shiga ya Musbah ya naushi iska da k’arfi, jikinsa har wani irin karkarwa yake yi tsabar takaici.

Dasauri ya Nafi’u ya rik’e shi yace’’haba Musbahu! kayi hak’uri a bi komai a hankali, lokaci zai sa komai ya yi daidai inshaaAllah.’’

Kamar zai fashe da kuka ya ce
‘’Astaghfirullah, Nafi’u wacce iriyar rayuwa ce wannan? kalli family d’ina! kalli halin da suke a ciki!
amma wai ace banida yadda zan yi in taimakesu?
ka duba kaga yadda ake shirin aurar da su Manubiya kamar wasu Kaji?
kuma a yadda Baba yayi bayanin nan tabbas yana da gaskiya ta wani fannin tunda daga ni har shi ɗin ba za mu iya karesu ba..

amma dukda haka bai kamata Jidda ta auri Yusuf ba, kuma ya kamata ace na yi wani abun amma banida……’’
Kukan da ya kufce masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana.

Ya Nafi’u ji yayi kamar shima ya fashe da kuka, dan haka cikin sanyin jiki ya matsa kusa da ya Musbahn ya rungumesa, sannan
cikin sigar rarrashi ya ce ’’kuka da k’unci ba shine mafita ba
Musbahu, kar ka dasa ayar tambaya a kan k’addararka ka je garin hakan ka kauce hanya, sannan kar ka karaya ka ce wai dan baka da k’arfi ba za ka
Iya yin komai ba. inshaaAllah za mu fahimtar da Baba kuma zai fahimcemu, dan ko da ace za’a aurar da su Jiddan to ni
kaina ba zan goyi bayan a aurar da su da wuri haka ba kuma ba zan bari Jidda ta auri Yusuf ba inshaaAllah.
kawai dai yanzu abunda nake so ka fahimta shine ‘Baba ya d’au zafi!. Sannan hankalinsa a tashe yake!’
Dan haka ka bari nan da kwana biyu inshaaAllah idan ya d’an sak’k’o mu ka lallab’a shi na san zai fahimce mu.
Ubangiji yana tare da mu, komai zai yi dai-dai inshaaAllah’’.

Cika shi Ya Musbah ya yi, ya je jikin window ya dawo ya sake komawa…yana yi yana share hawayensa, kafin da kyar ya samu ya tsayar da kukan nasa
tukunna ya ce ‘’Allah ya dafa mana. Allah ya tsaya mana. Nafi’u na san zafin rashin dace da Abokin rayuwa, idan akayi rashin sa’a Baba ya k’i amincewa da mu ya je garin neman mafita ya ɓurma su Jidda a Hannun mugaye shin ya kake tunani kenan?
Kar mu je duk mu ukun mu k’are da…..’’

Da sauri ya Nafi’u ya ce ‘‘Musbahu, ka kyautata zato dan Allah…think positive!.
inshaaAllah hakan ba za ta faru ba’’.

Shiruuu, ya Musbah ya d’anyi da farko!
yana me sauk’e ajiyar zuciya a
jere a jere, kafin ya jinjina kai kawai, daga haka ya k’arasa bakin gadon da Abbakar ya ke nan a kwance ya zubawa guri d’aya ido ya yi shiruuu.

Numfashi Ya Nafi’u ya fesar, kafin ya d’ago wayarsa da sauri dan shi sai yanzun ne ma ya tuna ya yi dialing number Aisha tun d’azu,
yana d’ago wayar kuwa ya ga timer tanata tafiya alamun ta d’auka kenan tun d’azun.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya kara wayar a kunnensa ya ce ’’lab’e kika fara kenan!’’

Murmushi ta yi, sannan ta ce ’’na d’auka sai su khairat suka fara fad’a ita da mai sunan Baba, shine na ajjiye wayar na je raba su da ke hankalina ya yi gaba a tunanina na kashe. amma kuma dukda haka da na d’auka d’in da farko kafin in ajjiye na ji maganar da ta d’an kid’ima ni shiyasa ma na manta ban kashe d’in ba tsabar kid’imar da na yi’’….shiruu ta d’an yi kafin ta ce ’’da gaske Manubiya aure ta yi???”

Dafe Kai ya Nafi’u ya yi kafin yace’’kinga irin ta ko, baki tsaya kin ji kan zance da k’arshen sa ba kawai daga kin ji ance aure shikenan ke har kin je ga ƙarshen zancen.’’

Fahimtar da Aisha ta yi kamar ran maigidan nata a d’an b’ace yake ne yasanya cikin kwantar da murya tace ‘’Allah ya huci zuciyarka, ba zan k’ara ba.

Dama na ga kamar Inna tana jin yunwa ne shine na kira inaso in tambaya a bata madara ne ko abinci, to kuma sai baka d’auka ba, a lokacin kuma wayar Manu bata shiga amma na same ta ma har ta yi min bayani tun d’azu mun gama magaana.”

‘’Okay, sannu Aisha, Allah yayi albarka’’ ya Nafi’u ya fad’i hakan cikin sanyin jiki.

Ahankali tace ‘’ameen’’ daganan suka yi sallama bayan yace mata ‘ai sun ma kusan dawowa’
Dan haka ta bari akan idan sun dawo sai ta ji koma mene ya kaisu suka dad’e har haka.
………….
Tun lokacin da Ya Musbah ya kai Inna gidansa ya fita!
Baraka ta kumbura, ta rasa Ina za ta saka ranta. Tashi d’aya ta ji gaba d’aya
duniyar ta yi mata zafi…ita fa dama tun farko abunda take ta tsoro kenan, dan ita babban tashin hankalinta kar rikon Inna ya dawo hannun Ya Musbah! Dan wallahi ita bazata tab’a iya jurar ganinta a cikin gidan ba!….dad’in dad’awa kuma gata liability, saboda Allah in banda rashin adalci ta yaya ma za’a had’ata da jinya, ai ba dan haka aka aurota ba!.

Takaici da bak’in ciki ne ma suka saka ta kasa tab’uka komai a cikin gidan, dan haka ta fito tsakar gidan ta zauna akan y’ar kujerar tsugunno tanata faman cika tana batsewa, ko d’akin da aka ajjiye Innar bata lek’a ba tunda su ya Musbah suka kawo ta suka fita…
Muhsin ne da me sunan Baba wanda tunda ya gansu yaketa murna ya shige d’akin shima
suke ta yiwa innar hira.

Baraka kuwa tana tsakar gida ta d’aurawa kanta bala’i in banda tafarfasa babu abunda zuciyarta takeyi…a haka Aisha ta shigo ta same ta.

Sama-sama suka gaisa da Aishar daga haka ta tambayeta d’akin da innar take, ta nuna mata,
Aishar ta shige.

Tana shigewa Baraka ta mik’e tsaye dan zuwa wannan lokacin ta ma kasa zama kwata-kwata, kamar wata wadda aka aikowa da rikitaccen sak’o haka ta shiga safa da marwa a tsakar gidan ta kasa tsaye ta kasa zaune….itafa ba zai yiu a maida mata gida asibiti ba wallahi!
Tunda gashi y’an dubiya har sun fara zuwa, wannan ya shigo wanchan ya fita shikenan ita ba ta da sirri a cikin gidanta kenan?
Gashi har yanzu su Ya Musbah shiru, ta kirasa kuma ya k’i d’agawa,
Itafa wallahi Inna ba za ta kwanar mata a cikin gidanta ba yau.!.

Sama-sama ta fara jiyo muryar
Aisha kamar tana waya da ya Nafi’u dan haka ta je ta lab’e…..
wani irin gumi ne ya shiga keto mata sakamokon kunnuwanta da suka jiyo mata lokacin da Aisha take cewa “da gaske Manubiya aure ta yi???’’.

Tashi d’aya Baraka ta shiga cikin maɗaukakin tashin hankali, a ranta ta ce
“Manubiya ta yi aure!
Abunda suka je yi kenan?
To ina batun
Baba kuma dan d’azu maman Abbakar ta kira ta take gaya mata cewar “kamasa akayi!
Shiyasa suka kawo innar suka tafi gaba d’ayansu, itama ta so ta
tsaida Abbakar amma yana gaya mata an kama Baban ya fice a gigice har yanzu shiru babu shi babu labarin shi tanata kiran wayar sa kuma baya d’auka’’
…
“Wato Shiyasa aka kawo mata inna da Muhsin tun yanzu kenan…
Manubiya tana tarewa a gidanta ta san jidda ma nan za ta dawo!
Kut!ai wallahi bazaiyiu ba, wannan abu ba zai tab’a sab’uwa ba, ba za ta zauna a gida d’aya da su ba wallahi!
Sannan
yanzu haka ma ya aka k’are,
tayaya ya Musbah yake iya ciyar da su biyu kawai
Ina kuma ga in nauyi ya sake yi masa yawa.’
Waennan sak’e-sak’en da Baraka take ta yi ne ya sanya ta fara jin jiri, dan bala’i har wani dishi-dishi ta fara gani!
dan haka ta koma ta zauna a kan y’ar kujerar ta tana ji kamar zuciyarta zata kama da wuta.

Bata dad’e da zama ba, Aisha ta fito ita da khairat ta ce mata ‘’ta d’aura girk, bara ta je ta duba’’

‘’To’’
Kawai Baraka ta iya ce mata shima kuma da kyar, dan wani irin tafarfasa zuciyarta takeyi.

Aisha tana fita Baraka ta mik’e.
Ta ma rasa me yakeyi mata dad’i! ta rasa Ina zata saka ranta ta ji sanyi…

Tabbas idan fa ta yi sake tou wallahi ruk’on inna ya dawo hannunta kenan har abada tunda ko
da ace daakwai Jiddah ai
Jiddan in dai ta ci post utme d’inta to makaranta za ta fara zuwa!!!
Muhsin yarone ya Musbah kuma aiki zai ce ze dinga fita, shikenan ita a barta da inna kenan….
Ita kam a barta da talaucin da ya Musbah ya tsundumata a ciki ma mana
ba sai an k’ara mata da zama gida ɗaya da dangin miji ba!.

Tsulum!
Haka Muhsin ya ga Baraka ta afko cikin d’akin da suke a ciki shi da inna…
Da sauri ya mik’e yana cewa “anty, kin ji yanzunnan
Na ji inna ta ce ‘Manu’ wallahi!
Ki matso ki tambayeta ki ji’’
Ya fad’i hakan cikin tsananin farin cik, yana Jan hannun Baraka yana dariya…

Wafce hannunta ta yi da k’arfi ta...

*MANNUBIYA*

*40*

Wafce Hannunta ta yi ta k’arfi
ta ce ’’dalla ni cikani”

A hankali Muhsin wanda duk jikinshi ya yi sanyi ya ce
‘’Da gaske nake fa’’

Da kyar Baraka ta d’an k’ak’alo murmushi sannan ta ce
‘’Na yarda mana, nima ai tun daga waje na ji lokacin da ta fad’a’’

Da sauri ya ce
‘’au haba! bara mu kira su……”
Chapter 66 · 0% Book details