Sashe 6
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aikuwa har bakin ƙofar toilet ɗin ya je ya yi ta faman knocking
Ya na rarrashinta ta amman sam ta ƙi ta tanka shi.
Ya jima a wajen kafin da kyar ya jaa ƙafafuwansa ya bar ɗakin yana mamakin abun da ya ke damun Ƙausar….
Tun suna da shekaru 14 a duniya su ke soyayya
ya kuma san ta na tsananin ƙaunarsa, kawai dai bai san mai ya faru kwana biyun nan ba, gaba ɗaya ta hargitse, kamar ma ko kallon sa ba ta son yi…..
….
Sai da ta ji fitar sa,
tukunna ta sauƙe wata nannauyar ajiyar Zuciya ta buɗe ƙofar ta fito…
Ba wai ba ta son Yassir kwata-kwata bane a yanzu.
Tabbas akwai ragowar burbuɗin soyayyar sa a cikin Zuciyar ta har kawo wannan lokacin.
Tun suna Yara ta san YASHJUB ya na burgeta amma ba ta taɓa sanin
soyayyarshi za ta iya yi wa zuciyarta mahaukacin kamu ba
sai da ta ganshi after 10 years!!.
Sannan bayan soyayyar ta gare shi, babu ta inda za a haɗa Yashjub da Yassir…
Kyau, Ilimi, class, haɗuwa! Uwa uba kuɗi duj
Yashjub ya fi Yassir komai, ta koina.
Tabbas ta san za ta sha fama.
Ta san dq wuya Yassir ya haƙura cikin sauƙi sannan da wuya shima Yashjub ya yarda cikin sauƙi, ga kuma Iyayensu waenda ta san ba ƙaramin rikici za fa kunno a tsakaninsu ta hanyar yin hakan ba! To amma ya ta iya?!
Dan har ga Allah ba ta jin ta na da sauran numfashi a gaba
muddin rayuwarta babu Yashjub a ciki….
Duk yadda Yassir ya so daurewa kasawa ya yi!
A yadda ya ke jinshi tsaf zai fashe da kuka, shiyasa bai kula kowa ba haka nan ya zo ya wuce taron jama’ar wajen ya shige cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki a nan jikin parlourn….
Yana shiga ko ida rufe ƙofar bai yi ba!
Hawaye su ka wanke mishi fuska!.
Duk wani abu wanda ya ke za a iya fasawa a cikin ɗakin sai da ya fasa shi!
Wanda hakan ne ya janyo hankalin jama’ar da ya bari a waje! bari
Har ta kai ga Abokanan shi guda biyu shigowa….
Dama a yadda su ka ga ya sauƙƙo ɗin sun san ba lafiya ba.
Da kyar ɗayan ya iya kwace kwalbar Hannu shi wadda ta yi masa jina-jina…
Ya yar da ita
Cikin ɓacin rai ya ce
‘’Haba Yassir!!
Kana hauka ne?
Wai duk akan Mace ne ka ke wannan jahilcin?
A haka kana mata naci zata soka ne an gaya maka?.
In bata sonka ka haƙura mana
A Ina aka taɓa yin so dole.”
Cikin tsananin fushi
Yassir ɗin ya shaƙo wuyan shi
Wanda hakan ya sanya ɗayan Abokin nasu ya matso ya fara lallaɓa shi da bashi haƙuri, dan ya
lura ba ya tare da hankalinsa…
Da kyar kuwa ya samu
ya cika shi, Abokin nasu ya juya yana wani irin huci da sauƙe ajiyar zuciya a jejjere…
Cikin tsananin ɗacin zuciya Yassir ya cewa ɗayan
“Ka shirya komai.
Kowa ya watse.”
•••••••
B U K
Kano
Bayani tuƙuru lecturen ya ke yi, wanda ya yi tsaye a gaban whiteboard na lecture hall ɗin.
Gaba ɗaya hankulan ɗaliban ya na a kan shi ne, ajin ya yi tsit kowa ya nutsu wanda hakan ke tabbatar da Ana jin tsoron lecturer din…
Kowa ya nutsu kalli ɗaya za a yi musu a fahimci babu mai buƙatar yin laifi.
Tunda ya shigo ajin ya lura da ita da kuma yanayinta…..
Farar budurwa ce,
sai dai ba ƙal ba
amman yanayin farin na ta mai tsananin kyau da ɗaukar hankali ne..
Zaune ta ke a cikin ajin sai dai zaman nata bai ɓoye yanayin halittarta ba…ta na da tsayi sannan ba ta da jiki amman ba za a kirata da ƴar siririya ba sakamokon yanayin
ƙirar da Allah ya yi mata…
Sannan kyakkyawa ce ajin farko,
Yauma kamar kullum tun shigowar ta ajin nasu lecturern ya fahimci hankali da tunanin ta ba sa ajin,
dan tun farko fara ɗecturen ya ga ta zabga Uban tagumi da Hannu ɗaya.
Yana shirin ɗauke Idanunsa daga kanta kawai ya ga hawaye sun fara zubowa daga cikin idanunta!
Wanda ya fahimci ita kanta ba ta san hawayen sun taho ba har sai da su ka samu nasarar sauƙa akan kumatunta tukunna ta ji ta fahimta, dan haka da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, kawai kuma sai ta fashe da kuka marar sauti.
Har aka yi lecture ɗim aka gama aka ɗauki attendance bama ta san an yi ba
Saboda yau ɗin zagewa ta yi sosai ta zubar da hawayen da suka tarar mata a ƙirji su ke bada gudunmmawa a ƙaruwar ƙuncin ta.
Ta kuwa dan ji sanyi ba kaɗan ba …..
‘’MANU!!
Za mu wuce‘’
Muryar budurwar da ta ke zaune a gefen ta ta katse mata hawaye da ajiyar zuciyar da take ta faman sauƙewa a jejjere.
Da sauri ta sa Hannu ta goge fuskarta, kafin ta ɗago.
Ko kallon su ba ta yi ba, kawai ta ɗan matsar da ƙafar ta gefe domin su samu damar wucewan…
Tana jin ɗayar ta ce
‘’Allah ya kyauta!!
Kowa dai yana da damuwar nan daurewa kawai akeyi.”
Bata da lokacin su, dan zuwa wannan lokacin abunda ya ke kanta ma ita kam ya ishe ta ya yi mata yawa ma, tunda gashi yau
har da kuka tuƙuru ta yi a aji, dan haka ko shirin biyesu ma ba ta yi ba, ta barsu su ka wuce. Kafin itama ta ɗan sunkuya ta ɗauki koɗaɗɗiyar Jakarta tukunna ta miƙe, ba ta yarda ta kalli kowa ba, kawai ta nufi ƙofa.
Ai kuwa kamar wata tv haka ragowar students ɗin suka bita da kallo, wasu ta basu tausayi wasu kuma ta basu mamaki!
Dan tashi ɗaya duk wanda ya kalli fuskarta to ya san kuka ne ta yi.
Gaba ɗaya duk sai ta ji ta muzanta ganin kalar yadda ake ta kallon ta..
Ta ji sauƙin raɗaɗin zuciyar ta tabbas
amman kuma duk sai ta ji takaicin kanta na kukan da ta zage ta rasga a aji, dan haka tana fita ta wuce
Ko ABBAKAR yau ba ta tsaya jira ba.
Tana fara tafiya ta jiyo shi ya biyo ta a baya yana kiran ta
“Manu ! Manu !! Manu!!!.”
Sai da ta ɗan gyara fuskarta wai ita ala dole kar shima ya gane kuka ne ta yi!
Tukunna ta ɗan tsaya ba tare da ta juya ba… a haka ya ƙaraso
ya sameta a wajen ya na
ɗan haki
wanda ya ke nuni da sai da ya haɗa da gudu tukunna iske ta, ya na hakin ya ce
‘’Hope dai ba ki yi attendance ba.
Kar Sir Najeeb ya ga sunanki biyu ya fito, ɗazu na ga kin
sunkuyar da kanki
s kuma na gefen ki da su ka gama basu tashe ki ba
shine na rubuta miki.”
Jinjina kanta ta yi kawai alamun ‘Eh’
Sannan ta sa Hannu ta ɗan goge fuskarta sam ta ƙi yarda ta kalleshi ita ala dole kar ya fahimci kuka ta yi.
A hankali ta ce ‘’na gode abbakar ‘’
Murmushi ya yi kafin ya ce
‘’oh com on Manu!
Na san fa kuka kika yi ’’
Girgiza kai ta yi, kafin ta ce
‘’Ban yi komai ba ‘’
Murmushi yayi mai ɗan haɗe da dariya kafin ya ce
‘’kalle ni ‘’
Bata ɗago ɗinba
dan haka ya zagayo ya tsaya a gaban ta sosai ya tsare ta da Idanu
ya na kallonta kawai kafin
a hankali ya samu Bakinshi ya sake furta kalmar
‘Kalle ni ‘
Yanzun ma ba ta ɗago ba, suna a haka wani ɗan ajin su ya zo ya cw
‘’Yauwa ku nake nema…
Sir Najeeb ya na kiran ku”
Har ya yi gaba sai kuma ya dawo ya ce
‘’ I mean, yana kiran ta dan ita yace in kira but na san tare za ku je
shiyasa na ce muku yana kiran ku ‘’
Ya fadi hakan yana dariya ƙasa-ƙasa sannan ya ɗaura da cewa
‘’Ku yi sauri yana ajin har yanzu’’
Kafin yace musu ‘’sai anjima‘’
Daga haka ya juya ya wuce..
Addua MANNUBIYA ta shiga yi….
Ta na roƙon Allah yasa ba wani abu serious bane ba, dan in dai ka ji kiran
sir Najeeb tou ba alkhairi bane ba…
Dan haka tashi ɗaya sai ta ɗan tsure!
Wanda hakan ya sanya har ba ta ma jin Abbakar wanda ya ke ta yi mata magana
har sai da ya sake cewa
‘’Manu.
Kar fa ya haushi ‘’
Tukunna suka jera su biyun suka nufi ajin da suka gama lectures ɗin a cikinsa yanzunnan…
Waya suka sameshi yana yi dan haka suka tsaya jira…
Ya fi minti huɗu kafin ya yi sallama da wanda ya ke wayar da shi tukunna ya miƙe ya fara harhaɗa takardun shi…
Yana haɗa takardun ba tare da ya kallesu ba ya cw
‘’Next time, idan kin san kuka da rashin maida hankali za ki yi mini a aji to kar ki sake shigowa‘’
Daga haka ya sa kai ya fice ,
ko haƙurin da suka fara bashi bai tsaya ya saurara ba….
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*03*
Ya na fita Abbakar ya fesar da iska kafin ya ce
‘’Allah ya taimake mu…mun ci sa’a.”
Dan tabbas shi kan shi ya ɗan tsorata kuma ya san ba ƙaramar sa’a su ka ci da sir najeeb ɗin ya bar Manubiya a iyaka warning
bai ce kar ta sake shigar masa aji ba.”
A hankali itama Manubiyan ta sauƙe numfashi, bata gama tunani ba ta ji ya ce
‘’Nima ina son ganinki. Bismillah, zauna.”
Ya faɗi hakan yana nuna mata wajen zama, sannan shima ya nemi seat ya zauna dan zuwa wannan lokacin babu kowa a ajin.
Shiruu ta yi kamar ba za ta zauna ɗin ba, sai kuma ta nema seat na kusa da ita row ɗin farko ta ja ta zauna tukunna ta ce
‘’Ina jinka.”