← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 84

Sashe 41

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘’You are suppose to be busy by this time(kamata ya yi a ce kana busy a dai dai wannan lokacin), ko ba da safe ka ce mata ta zo ba?’’
muryar Najeeb ta katse masa tunanin da yake yi.

‘’Yeah, gata nan ta zo amma basu shigo ba.
amm..Najeeb, wanann yaron da na gansu tare ranar a office d’inka waye ne shi d’in saboda yau ma gasu nan ta taho min da shi.’’

D’an guntun murmushi Najeeb ya yi yana mai jiyo kishi k’arara a muryar Yashjub d’in,kafin ya ce ’’inaga kamar d’an uwanta ne..
Maybe ko cousin dan surname d’in su ba d’aya bane, amma wani lokacin ma tare suke shigowa aji, so ina ga kamar a gida d’aya suke zaune.
are u jealous?’’
Najeeb ya k’arashe bayanin nasa da tambaya, yana mai dariya k’asa-k’asa.

Tsaki Yashjub d’in ya yi, dai dai nan Racheal ta d’an yi knocking tukunna ta yi sliding k’ofar ta shigo Manubiya na biye da ita a baya.

Sama-sama ya fara jin Najeeb
saboda lokaci d’aya jikinsa ya yi sanyi sannan yanayin bugun zuciyarsa ya k’aru.
A hankali ya cewa Najeeb “I’ll call you back’’
bai jira jin mai Najeeb d’in zai ce ba ya katse kiran, yana jin yadda yanayinsa ya sauya tashi d’aya.

Cikin nutsuwa Racheal ta ce ’’Sir she’s here(ga ta nan)”
A hankali ba tare da ya juyo ba ya ce ’’Thankyou,you can leave(za ki iya tafiya, na gode)”

Racheal d’in ce ta nunawa Manubiya inda zata zauna kafin ta juya ta fita bayan Manubiyan ta zauna da kyar, tunda suka shigo company d’in jikinta yayi sanyi..tunda ta hango shi a tsaye ya juya baya ta nemi kuzarinta ta rasa!!!
gashi yanzu kuma tunda ta shigo office d’in k’irjinta ya hanata sukuni…
Gashi ƙamshin turarensa wanda ya karad’e ilahirin office d’in ya yi mata kamar na mutumin da ta had’u da shi a office d’in Sir Najeeb,
dan tabbas hancinta ya shak’i ƙamshin sosai a wachchar ranar a lokacin da ya matso kusa da ita zai fita…
sannan babu abunda ya fi d’aga mata hankali irin muryar da ta ji a yanzu a lokacin da ya yi wa wadda ta rakota( Racheal) magana, kar dai fa ace wannan mutumin ne, dan in dai ba gizo muryarsa ta yi mata ba to kuwa tabbas wannan Mutumin shine wanda suka had’u da shi a office d’in Sir Najeeb kwanakin baya.

Da kyar Yashjub ya d’an nemo nutsuwa ya sakawa gangar jikinsa tukunna ya juyo, cikin takun shi na k’asaita ya nufo tebur d’in, ba tare da ya kalle ta ba.

Wani irin bugawa zuciyar Manubiya ta shiga yi
dan yana juyowa ta shaida shi
‘’amma Abbakar bai kyauta min ba’’
ta fad’i hakan a chan k’asan zuciyarta, kafin a hankali ta sunkuyar da kanta k’asa tana jin kamar ta tashi ta fita da mugun gudu.

Idanuwanta da zuciyarta sam
sun gagara daina zuzuta mata
tsananin kyawun da yayi ga wani haiba da kwarjinin da yayi mata wanda suka taimaka wajen sake hautsina mata lissafi…
A ranta ta shiga aiyyana cewa “ashe wanchan karon ban gansa sosai ba.’’
Tana wannan tunanin Yashjub ya nemi waje ya zauna a kujerar da take facing d’in ta, yana mai jin k’irjinsa yana bugawa, kafin a hankali ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zuba su a kanta…..
Wani irin sanyi ya ke ji yana ratsa shi tun daga saman kansa har izuwa kan babban d’an yatsan k’afarsa….a take wata nutsuwa da kasala suka sak’e rufar masa yana mai jin wani irin nishad’in da bai tab’a jin kwatankwacin irin shi ba.
Duk da yadda ta sunkuyar da kanta hakan bai hana shi k’arewa kyakkyawar fuskarta wadda ke zagaye a cikin hijabi kallo ba, a hankali a chan k’asan zuciyarsa ya ce
‘’Subahanallah, MashaaAllah,
Allahu akbar!..’’

Tun lokacin da ya zauna ya fara kallon ta ta diririce…
da kyar da mugun kyar ta samu ta iya d’ago fuskarta da niyyar gaida shi amma sai ta ga ya kafeta da kyawawan idanuwansa, cikin sauri ta kauda kanta gefe saboda girma da nauyin da ta ga kwayar idanun nasa sun yi mata…a hankali ta ce
‘’Good morning,Sir,’’
da kyar.

Lumshe idanunsa yayi ya bud’e yana kallon yadda take kallon gefe kad’an ita ala dole ba za ta had’a ido da shi ba bayan kwanakin baya da kyar ta iya zare idanunta a nashi..bai san lokacin da wani murmushi ya kufce masa ba
wanda har sai da ta d’an jiyo sautin kad’an, kafin cikin kamala da dad’in sauraro ta ji ya ce ’’’Morning, you called me day before yesterday(kin kira ni shekaran jiya)’’
ya fad’i hakan har zuwa wannan lokacin idanuwansa na a kanta yana yi mata wani irin kallo kamar wanda yake so ya k’irga duk wata b’ular gashin da ke a fuskarta ne. Shi kan sa yana so ya d’an d’auke idanun nasa daga kanta amma sam ya gagara, babu abun da ya fi d’aure masa kai kamar yadda tashi d’aya ya shiga nutsuwa walwala da farin ciki da annashuwar da bai tab’a shiga ba.

A hankali ya ji ta ce
“Sir Najeeb said you have a job for me, that’s why I called.(sir Najeeb ne ya ce kana da aikin da za ka bani, shiyasa na kira).”
Ta k’arashe maganar a hankali
kamar tana jin tsoro.

Shiruu ya yi, yana kallon ta kafin chan yace’’Yeah,i do,can i see your credentials.(eh, ina da aikin da zan baki, zan iya ganin takardunki?.)”

A hankali ta lumshe idanuwanta dan sai a wannan lokacin ne ta tuna bata d’auko na secondary school ba wanda ya ke shi a chan sama yake a cikin akwati, dama tana ta zuci zucin za ta d’auko ta had’a da ragowar sai dai kuma har ta fito Allah bai bata iko ba, haka nan ta mik’a masa na primary da diplomar ta tukunna ta ce masa’’ ta manta na secondary school d’in’’
dan haka ya ce ‘’ba damuwa, next zuwan da za ta yi, ta zo da shi’’.

Ya d’an jima yana nazari kafin
ya fara yi mata bayanin aikin
nata yadda zata fahimta…….
‘’Akwai estate a Kano, Lagos da Abuja.
Bana so idan abu ya b’aci a dinga kira na direct almost everyday (kusan kullum) sannan secretary d’ina is very busy (aiyyuka sun yi
mata yawa) itama, dan haka zan tura musu number d’inki ta yadda duk wani complain idan za su yi kawai za su gaya miki ki tara ki ajjiye, sai ki dinga reporting to me ranar Friday, duk Friday…
Kinga yau Monday to in four days time(to nan da kwanaki huɗu) za ki zo nan kenan,
Amman idan akwai abu urgent(abunda ya ke buƙatar a duba cikin gaggawa), za ki iya kirana ko kuma ki gaya min ta online, ba sai kin jira friday ba…
k’arshen wata zan dinga baki 30k.
Mun fahimci juna?’’.

A hankali ta jinjina kai kafin ta ce ‘’Yes,Sir
Thankyou so much.’’

Jinjina kai kawai yayi yana mai sauk’e wata b’oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya mik’a mata wata takarda mai d’auke da wajen saka;
Full name
Address
Personal sickness
Email
Phone number,da sauran su……
ya ce’’ki yi filling wannan.(ki cike wannan).”

Cikin nutsuwa ta zaro biro a jakarta, ta hau cikewa…
wajen phone number ne ta bari blank dan bata san ya za ta yi ba, da farko ta yi tunanin ta saka number Siyama tunda ita bata da waya sai kuma taga ai aiki ne bai kamata ta d’aura mata komai a wayarta ta takura mata ba sannan anytime za ‘a iya kiran ta kar aji wata ta d’auka ya zamana kamar bata d’auki aikin ma da mahimman ci ba, shiyasa ta ga gara a yi
k’ok’ari a san yadda za ayi inshaaAllah ko mai torchlight ce su nemo sai ta taho da number tare da certificate d’in nata, dan haka ta bar wajen blank
ta cike ragowar.
tana gamawa ta mik’a masa, tana addu’ar Allah ya sa daga wannan ya sallame ta.

D’auka ya yi, ya kalla yaga ta bar wajen phone number blank
dan haka ya ce ta k’arba ta k’arasa cikewa.
Sai da ta d’an yi shiruu tukunna tace masa ‘’a yanzun ba ta da waya,amma inshaaAllah zata taho da phone number d’in a next zuwanta tare da secondary school certificate d’in nata.’’

Shiruu yayi kawai ya zuba mata ido yana mamakin ‘ta ya kamar ta ace bata da waya’
Wanda hakan ya sanya Manubiya ta ji kamar ta kurma ihu!..dan
gaba d’aya ya d’aure ta da idanuwansa, ta koina jin kwayar idanunsa take yi suna yi mata yawo a jiki.

Ya jima yana k’are mata kallo kafin ya d’an sunkuya ya janyo d’aya a cikin drawer da ke jikin tebur d’in ya zaro wata farar leda, jiya ya sayi A1 d’in zai bawa mai wankin su da ya ce masa wayarsa ta fad’a a ruwa…
A hankali ya mik’a mata ya ce ‘’ga shi,idan kin yi charji sai ki turomin messge da number ki meanwhile zan basu email d’in ki idan number ya zama ready sai ki turomin in tura musu ta yadda za ki fara aikin asap.’’
ya fad’i hakan yana mai mik’a mata wayar.

sai da ya sake cewa ‘’ki karb’a mana,consider it as an allowance’’
tukunna a hankali kamar mara lakka a jiki ta sa hannu ta karb’a ta ce ’’Nagode,sosai,’’

dan dama har ga Allah bata san ta ina zata fara neman waya ba su da suke fama da abinci.

Ganin ya yi shiruu ya koma ya jingina kawai yana k’are mata kallo ne ya sa ahankali ta sake cewa’’na gode’’
daga nan ta yi masa sallama ta mik’e ta nufi k’ofa tana adduar Allah ya sa kar ya sake tsayar da ita, a haka har ta fice daga office d’in.
..
Tana fita ya lumshe kyawawan idanuwansa, ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake kai a zaune,
a hankali a fili ya ce
‘’It’s official,I’m in love
(Ta tabbata son Yarinyar nan na ke yi.)”
Chapter 41 · 0% Book details