← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 84

Sashe 28

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman shi Yasir har yanzu shiru Allah kad’ai ya san inda ya je ya zauna.
Dan haka ta yanke shawarar tunkarar Daddy da maganar yau duk da bata san ya za su kaya ba amma ta saka a ranta zata yi koma menene muddin za a nemo mata Yasir d’inta.

Dama yau ɗin ita ce da girki dan haka ana gama dinner bayan an d’an tab’a hira kowa ya watse itama ta je ta d’an kimtsa ta nufi chan sama hawa na biyu inda side d’in shi yake.

A parlournsa ta same shi yana waya dan haka ta koma gefe ta samu guri ta zauna.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*17*

Ya fi 1 hour yana wayar kafin finally ya katse kiran ya ci gaba da danna computer dake a gaban sa.

Ta ji zafin yadda ya yi mata, dama a wuya take dashi yau ko kunya babu haka ya dinga zolayar Ummi ɗazu a wajen dinner a gaban kowa ita kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba.

Da kyar ta samu ta danne abunda takeji yana taso mata, ahankali ta ce’’barka da dare,Daddy’’.

Ba tare da ya kalle ta ba
Ya ce ‘’za ki iya tafiya, na gode.’’
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya tartare kayayyakinsa waenda ke zube a gabansa kan centre table ɗin, daga nan ya nufi hanyar d’akinsa.

Da sauri itama ta mik’e ta ce ’’a kan Yasir na zo mu yi magana’’.

Kamar ba zai kula ta ba sai kuma ya ce ’’what about him?( me ya faru akanshi?).
Ba tare da ya kalle ta ba.

Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce
‘’Ba ka lura baya gidan nan ba?
Ya fi 4 weeks fa ba ya nan’’.

Sun fi 2 minutes a tsaye dan sam Daddy bai so ya kula ta. Ya so ya danne fushin sa ya manna mata kawai ya yi wucewar sa amma sai hakan ya gagara..
A hankali ya juyo ya ajjiye computersa da wayoyin
a kan kujerar dake kusa da shi
sannan ya taka ya k’arasa inda take ya ce
‘’Khadijah, kar ki yarda ki kai ni bango a cikin gidan nan, ba ki san ya nake ji ba idan na kalli fuskarki, ina zaune da ke ne kawai saboda Ƴaƴan da ke a tsakaninmu da kuma alk’awarin da na yiwa su Abba kafin su rasu sannan na dawo gidan nan ne domin na lura in dai na zauna a daban daban ni da Ƴaƴana tou tabbas za ki iya raba ni da su.

Banason yawan magana ta da ke! saboda na lura baƙin ciki, da tashin hankalina kike son gani, a ko da yaushe kin fi so ki ganni cikin tashin hankali….
Dan haka na zab’a yin nesa da ke!.

Ina samu lumana da kwanciyar hankali daga wajen Saddik’a, abun da kika gagara ki bani.’’

Bakin Mommy har rawa ya ke yi, ganin tana shirin fara magana ya sanya yayi saurin d’aga mata Hannu alamun ‘wait(jira)’
ya ce
‘’Ba na buk’atar komai daga gareki, kin yi kuma kin ce me isarki…..
Kin san bani da lafiya amma a wannan shekarun ki ka zab’i ki tuna mini da case d’in ‘Khadijah’.
Ban san mai zan ce miki ba.
Amma kamar yadda na yi miki sutura na bar ki a cikin Ƴaƴanki sannan bayan na zab’i raba gida da ke na hak’ura na dawo na ci gaba da zama da ke a k’ark’ashin inuwa d’aya tou nima inaso ki yi mini alfarma d’aya tak,ina so ‘ki fita a harka ta’!!!!
Iyaka wannan kawai nake da buk’ata daga gare ki.

Case d’in Yasir na ce a gaya miki ki yi solving tun kafin mu zo ni da Saddiƙa, yanzu kuma da ya ƙi dawowa wannan ma matsalarki ce, ke kika san yadda za ki yi ki je ki nemo sa, amma Yasir ba jariri bane ba da zaki fake da case d’in sa ki k’ulla wata alak’a a tsakanin mu,
duk inda ya je idan ya gaji zai dawo in bai gaji ba kuma
Ubangiji ya sada fuskokinmu
A aljannah….

abu na k’arshe da zan ce da ke shine ki tabbata wannan ita ce maganata mai tsayi ta k’arshe da ke, in ba haka ba wallahi zan baki mamaki.’’

Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Mommy, a hankali yana shirin wucewa ta ce
‘‘Ubangiji ma muna yi masa laifi mu rok’i gafara kuma ya yafe mana, na ce ka yi hak’uri Daddy!
Ka bani last chance!
I love u, kar ka yi mini haka…..’’
Cikin fushi ya ce
‘’Ba kya so na ba kya k’aunata sam, shiyasa kike turturing d’ina(azabtar da ni). ko kin san cewa akan maganar da kika yi mini kad’an ya rage in mik’a kaina ga hukuma?kuma na san kin san menene hukunci na ko?’’

Cikin zubar hawaye Mommy ta ce
‘’Ka yi hak’uri mu bar wannan maganar ta wuce…..’’

‘’Get out!’’
Daddy ya fad’a cikin katse ta.

Za ta yi magana ya sake cewa
‘’ki fita ,na ce.’’
Da d’an k’arfi.

A hankali ta sa Hannu ta share hawayenta ta toshe Bakinta saboda kar sautin kuka ya sake fitowa, sai da ya ɗan lafa tukunna cikin tsananin mutuwar jiki ta ce’’ka yi hak’uri’’
daga nan ta juya ta fita tana mai sake toshe Bakinta.

Ya dad’e a wajen kafiin da k’yar ya samu ya juya ya wuce d’akinsa.
….
A d’akinta ta tarar da Kausar da Yasira…
Ta so ta b’oye musu damuwar ta amma suna had’a idanu da su sai ta karaya bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.
Sai da suka yi da gaske tukunna suka samu suka rarrashe ta, ta yi shiru, Yasira ta d’au waya ta kira Baaba Larai, tana zuwa suka shiga tattaunawa.
Ba su suka bar d’akin nata ba sai wajajen k’arfe d’ayan dare bayan sun saka Kausar ta yi musu alk’awarin kiran Yasir washegari,
Idan Allah ya kaimu…..
…
Washegari da sassafe
Kausar ta tashi ta shirya cikin wata dress mai kyau wadda bata k’arasa rufe mata k’afafunta ba.
Jan jambaki da kwalliya ta rambad’a sosai wanda hakan ya sake fito da ainihin kalar farar fatarta…
Hula kawai ta saka a kanta daga nan ta kama hanya ta fice ta nufi side d’in su Yashjub tana adduar Allah yasa bai fita ba, dan dukda yau ba aiki ta ji Yasira tana cewa sunada important meeting.

A parlourn ta same shi shirye tsaf cikin suite ga briefcase d’insa a gefe yana zaune yana sipping tea.

A hankali ta saki wani lallausan murmushi kafin ta k’arasa ciki, cikin takun ta mai tsananin d’aukar hankali.
sai da ta je kusa da shi tukunna ta ce
‘’Salam alaika’’.

Tun lokacin da ta turo k’ofar ta shigo ya lura da ita dan haka ya sake tamke fuska tamau kamar bai tab’a murmushi ba.

A hankali ta nema waje ta zauna a gefen sa, sannan ta ce
‘’Ya Yash, Ina kwana’’.

Ci gaba kawai yayi da sipping tea d’in sa yana kallon tv still bai ce mata uffan ba.

Badaban Kausar A ce a fagen tsaurin ido ba to da
a yadda ya tamke fuska kaɗai ya Isa yasanya ta tsorata, ta fita.

Duk da tana d’an fargaba haka ta daure a karo na uku ta ce ’’Ya Yash’’.

Lumshe kyawawan idanuwansa yayi a hankali ya juyo gare ta sannan ya bud’e yana mai kallon ta ido cikin ido
tukunna ya ce
‘’Duk abun da kike buk’ata ki turomin Yadira anjima, tashi ki fita.’’
Ganin yadda ta kafe sa da idanuwa ne ya sanya kawai ya mik’e ya d’au briefcase d’insa ba tare da ya sake bi takanta ba ya nufi hanyar fita.

Da sauri ta sha gabansa cikin d’an gudu ta ce
‘’Ya Yash Mommy ce fa ta aiko ni wajen ka’’
Ta fad’i haka tana k’ok’arin matsawa jikinsa sosai sannan ta saka Hannu zata kamo briefcase ɗinsa.

Duk kalar tsaurin idonta sai da ta ji tsoron kalar kallon da yayi mata dan haka ta d’an ja baya kad’an ta sunkuyar da kanta k’asa.

Da kyar Yashjub ya samu ya d’an rarrashi kansa, kawai ya wuce ba tare da ya yi mata komai ba ya fice ya barta anan wajen
amma da farko yadda zuciya ta taso masa so yayi ya d’an wanke ta da mari watakila zata dawo saiti!!!

Idan akwai abunda ya fi tsana a rayuwar sa bayan cin amana to shine Mace marar kamun kai!
tabbas Kausar y’ar uwarsa ce
amman kwata-kwata jininsa bai d’auke ta ba tun filazal, gashi yanzun kuma rashin kamun kanta ya sanya ta kuma fita a kansa ko ganin Yarinyar baya son yi,wallahi.

Da wannan tunanin ya k’arasa motarsa ya shiga ya zauna ya
lumshe idanuwansa….
A take idanunta waenda izuwa yanzu abun ya zame masa jiki suka hau yi masa gizo.
A ransa ya ce
‘’Ga inda ake Mace nan, gaisuwar ta ma tsada ne da ita, sannan ta yi laifi amman tsabar sanin darajar Kai
bata yi gigitar da d’ayan Namijin ya yi yana bada hak’uri ba….
Ana ganinta kuma za a fahimci yadda itama take a ruɗe amma ta dake sam bata yarda ta zubar da class d’inta ba….”
A hankali wani lallausan murmushi ya sub’uce masa
A fili ya ce
‘’Sai shegen kukan shagwab’a kamar wata y’ar baby’’…

Yana nan zaune yanata tunani
kira ya shigo wayarsa…
Ba k’aramin fad’uwa gabansa yayi ba a lokacin da ya d’auko wayar zai amsa idanuwansa suka sauk’a akan time,
‘Wato zaman sa anan har ya yi 30 minutes kenan??’
ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya samu mai basa amsa ba.
Ganin kiran yana shirin tsinkewa ne yasa yayi sauri ya d’auka ya kara a kunnensa ahankali ya ce
‘’Daddy Ina kwana,sorry wani abu ya ɗan tsaida ni,gani nan zuwa’’ .
Yana gama fad’in haka ya kashe wayar ya kunna motar ya bata wuta ya wuce….
Chapter 28 · 0% Book details