Sashe 33
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko bayan fitar Baba sai da Ya
Musbah ya kuma yi wa Inna bud’ad’d’an bayani akan illolin da shi yake hangowa game da aikin Manu da kuma yadda ya kamata ace shi ne ya ke d’awainiya da family d’in ba wai ita Mace ba.
Amman yana gamawa da ya sake ce mata
‘’Kin yarda Manubiya ta je ta yi aikin da aka nemeta ta yi?’’
Sai ya ga ta lumshe masa idanuwanta ta bud’e.
Cikin rashin jin dad’i ya kalli Manu, shima ya ce
‘’Ki kira sa, duk yadda kukayi kya gaya min gobe, sai da safen ku.’’
Ya fad’i haka yana mai mik’ewa ya fita.
Haka kurum kuma itama Manu d’in sai ta ji duk bata son kira, sai da Jidda da Muhsin waenda suke ta murna da zumud’i suka tisa ta a gaba tukunna ta fita ta je ta aro wayar Siyama ta dawo d’akin.
…
Gani suka yi kawai Manubiyan tana ta kallon wayar da katin tana juyawa dan haka Jidda ta sa Hannu ta karb’i wayar da katin ta kwafe nambobin farko a cikin jerin nambobin waya guda ukun da ta gani ata chan k’asan katin,ta dannna call ta saka a speaker..
Yadda wayar take ringing tana d’uu-d’uu haka zuciyar Manubiya take bugawa kamar zata faso k’irjinta ta fito.
Jin har ta tsinke ba a d’aga ba
ya sanya ta sauk’e wani bahagon numfashi, dan haka kurum ta ji tana fargabar jin muryar wanda zai amsa kiran.
A hankali ta lumshe kyawawan idanuwanta tana mayar da numfashi a hankal a hankali…
Tana shirin bud’e idanunta ta yi magana ta ji Jidda ta sake danna kiran a karo na biyu
ta shiga ringing..
Da sauri ta bud’e idanuwanta ta wafce wayar ta ce
‘’Ke ya isa haka, ba ki ga dare ya yi ba, Mutum Babba da matarsa kin dame sa da kira haka ki bari gobe ma sake gwadaw……’’
ta fad’i haka tana duban wayar dan ta ga ko ta kashe ne saboda ta ji ta daina ringin d’in…
Tsit!haka muryarta ta katse sakamokon ganin timer da ta yi tana tafiya akan fuskar wayar alamun wanda aka kira ya riga da ya d’auka.
Ganin yadda Manubiyn ta yi tsit ta zubawa fuskar wayar ido ne
ya sanya Jidda da Muhsin su ka lek’a fuskar wayar suma,
cikin zumud’i k’asa-k’asa Muhsin ya ce
‘’Adda Manubiya an d’auka fa, ki yi magana mana.’’…..
A hankali Yashjub ya lumshe idanuwansa ya rintse pillow d’in da ya d’aura akan k’irjinsa yana mai sake tabbatarwa da kanshi
Tabbas ita d’in ce…….
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*21*
Earlier..
Zuwan Abokin Daddy, senator Bashir biyu wajen Yahanasu, yau zai yi na uku.
Suna waya sosai da Yahansun sannan suna chatting, ta fahimci yana k’aunarta sosai dan yana nuna mata kuma yana yawan gaya mata.
Itama kuwa ta kamu ba kad’an ba dan hatta Daddy da Mommy da su Yashjub duk sun fahimci hakan dan har walwala yanzu suka ga tana yi shiyasa
Daddy Mommy da Yash suka duk’ufa da addu’ar ‘Allah ubangiji ya tabbatar da auren ta, yasa kar a samu matsala a wannan karon’.
Yau tun safe take shirye-shirye, k’arfe biyu tana yi ta shiga kitchen ta fara girke-girke
dan ya ce mata yau yana son cin girkin matarsa, saboda already a jiya suka tsayar ita da shi a kan
Next week zai turo a saka rana kamar wata uku haka a yi aure,
so yau suka tsayar za su sanar da Daddy.
Tana cikin aikin Munira ta shigo, tana son Yahanasu dan haka ta dage akan sai ta taya ta. Duk y’an gidan they are nice to her(ba sa yi mata rashin kirki) duk da basa zama su yi hira especially da Ya’isha wadda take ganin itace sa’ar ta amma kuma babu kyara ba kallon banza tsakanin su iya gaisuwa ne da murmushi daganan kowa ta shige d’akinta, duk ranar da bata da makaranta ta kan je d’akin su Yasmeen domin su yi hira amma tana zuwa daga gaisuwa suke shareta ko kuma su fara waya tunda ta ga haka itama sai ta ke zama kawai a d’akinta wani lokacin kuma ta tafi wajen Mamanta ko Yahanasu su yi hira.
Ba laifi suna shiri da Baaba Larai itama da kuma Mommy ma, ba wai za’a zauna a yi hira ayi wasa da dariya ba amman dai ana gaisawa cikin mutunta juna da kulawa.
Mutum d’aya ce ta fahimci ta tsane ta a gidan ‘Kausar’ sai ko ‘Yashjub’ wanda shima in ta gaida shi da kyar yake amsawa ciki-ciki!
Kausar d’in kuwa ko ta gaishe ta bata amsawa, bata san mai ta yi mata ba
amman tabbas ta fahimci ta tsane ta gashi kuma ta lura kamar kaff gidan su Yasira da su Mommy sun fi son ta da k’aunarta.
…
Ba yadda Yahanasu bata yi da Munira ba amma ta dage akan sai ta tayata, a cewar ta dama zaman shiru ya isheta kuma ta riga ta gama exams(finals d’in ta)tun last week so bata da abun yi…
4 tana yi ta je ta yi Sallah ta dawo daga nan itama Yahanasu ta tafi domin ta yi Sallah sannan ta shirya bayan ta cewa Munirat d’in idan yayi kafin ta dawo ta juye a cooler dan already komai ya kusan kammaluwa.
Sai da Munira ta had’a komai tukunna ta saka masu aikin suka tayata ta kai parlourn bak’i!
Ta kunna burner ta saka turare ta gyaggyara komai sannan ta wuce d’akin Yahanasu.
A gaban madubi ta sameta
sanye cikin wata Turkish gown mai tsananin kyau da tsada,
kwalli kawai ta sanya wa idanuwanta sai powder da lipgloss amma ta yi tsananin kyau!! asalin kyawun siririya kuma kyakkyawar fuskarta ya fito sosai.
Murmushi Munira ta yi kafin tace
‘’Adda Yaha, yau in senator ya ganki sai ya hantsila’’
ta fad’i hakan ta na mai k’arasawa cikin d’akin.
Dariya duk sukayi kafin
Yahanasu tana dariya ta ce ‘’Ba ki da dama wallahi’’.
Suna tsaye Munira tana taya ta rolling wayar Yahanasu ta fara k’ara.
Tun kafin ta d’auki wayar dama ta fahimci shine dan ringing tone d’in da ta saka masa daban ne.
Tana d’auka kuwa ya ce mata “ya k’araso, yana ma parlourn bak’i, Kausar ta shigo da shi.”
Da sauri suka kammala,
Yahanasu ta nufi parlourn bak’i,
Munira kuma ta yi sama dan itama zafi take ji tana buk’atar ta d’an watsa ruwa..
Ya yaba kwalliyarta da girkin kuwa, sosai haka ya yi ta zuba santi.
Sai da ya kammala tukunna ya zaro kud’i ya bata ya ce ga tukuicin girkin ta sannan ya sake zaro wani ya ce
wannan kuma na masu aikin da suka d’an taya ta da y’an yanke-yanke ne .
Tashi d’aya ta ce masa “Masu aiki wanke-wanke kawai suka yi, girkin kuma tare suka yi da sister d’inta Munira y’ar amaryar Daddy.’’
Ya san lokacin da Daddy ya k’ara aure amman basu tab’a had’uwa da Amaryar ba, balle y’arta sannan haka kurum tun da ta ce Munirat yanayinsa sai ya chanja.
Haka de suka d’an tab’a hira,
Sai da ta zo fita domin ta je ta kira masa Daddy dan yana so su yi maganar akan zai turo
tukunna ya ce “ta turo mishi Munirat d’in, ya bata tukuicin ta sannan su gaisa’’
Da ‘’to’’ ta amsa tukunna ta sa kai ta fice.
Har Yahanasu ta k’arasa d’akin Munira d’in tana d’an jin ba dad’i musamman da ta tarar da Munirat d’in ta yi wanka ta shirya…
fuskarta babu kwalliya amma yarintarta da kyawunta sun fito matuk’a, dan haka atake sai ta ji d’an guntun kishi yana taso mata, amma kawai sai ta saka kyakkyawan zato a kyakkyawar zuciyarta ta tura masa Munirat d’in ita kuma ta wuce wajen Daddy domin ta sanar masa da sak’on Senator Bashir d’in.
Tana fita itama Munira ta d’auki hijabinta ta zura ta nufi k’asa d’akin bak’in, ba dan ranta yana so ba.
A hankali ta k’arasa bakin glass door d’in ta yi knocking tukunna ta shiga kanta a k’asa da sallama
‘’Ashe rai kanga rai’’
Muryarsa ta daki dodon kunnuwanta.
Da sauri ta d’ago, ai kuwa suna yin ido biyu ta juya da sauri zata fita.
Amman sai aka yi rashin sa’a ya riga ta zagayawa ya tare hanyar, dama tun da ya ga ta shigo ya mik’e daga wajen zaman shi ya Isa kusa da ita.
Da sauri ya ce
‘’Haba Munira, after long time no see (bayan lokaci mai tsayi ba a haɗu ba) shine kuma za ki yi min haka kamar kin ga wani Aljani?
Kin sa yadda na dinga neman ki kuwa?‘’
Already Munira har ta fara kuka, dan haka ta d’ago a gigice ta ce ’’Dan girman Allah ka rufa mun asiri, mamana zata iya ganin ka, a gidan nan take aure mijinta kuma shine Mahaifin Adda Yahanasu wadda za ka aure’’
Cikin katseta ya ce ‘’Munirat ai yanzu maganar aure kuma ta tashi tsakanina da Yahanasu sai dai a yi maganar auren mu ni da ke,dan ni ke zan aura yanzu kam.’’
‘’Cin fuskar da zaka yi min kenan ??’’ su ka ji muryar Daddy a kansu.
Wani irin kuka Munirat ta fashe da shi, daman abunda take jin tsoro kenan..
Yahanasu ta riga Daddy k’arasawa bakin parlourn, yadda ya ga tana hawaye
ya san ba k’aramin abu ta ji ba tunda gashi shima iyakar maganganun senator na karshe ya ji amma gaba d’aya hankalinsa har ya tashi.
Idonshi a kan senator ya k’arasa cikin parlourn,
ba tare da ya kalli Munirat ba
cikin fushi ya ce ‘’bamu guri’’
Da sauri ta juya ta fita har da tuntub’e.
A bakin k’ofar suka yi karo da Yahansu tana hawaye, tana ganin ta ta juya da sauri ta nufi main parlour yayinda Munirat d’in ta bi ta da gudu, sai da suka kusa shiga parlourn tukunna ta samu nasarar cafko Hannun Yahanasun tana kuka ta shiga bata hak’uri sannan ta shiga ƙoƙarin fahimtar da ita ‘wallahi bata da niyyar cin amanarta, kuma ko Maza sun k’are bata ga dalilin da zai sanya ta saurari senator Bashir ba ma ballantana a zo ga batun aure’’