← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 84

Sashe 84

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri Yashjub ya ce ‘’Na gode sosai Daddy, zan turo maka adress d’in yanzu inshaaAllah’’
daga haka ya mik’e da sauri yace’’sai da safe’’ tukunna ya fice
tun kafin Daddy ya sa shi ya nutse cikin k’asa a take a wajen dan ya lura sarai yau Daddy tsokana yakeji
shikuwa ba zai iya ba.
Hakanan ya wuce zuciyarsa cike taff da farin cikin da bai tab’a tsintar kanshi a cikin kwatan kwacin sa ba….

Bayan fitar Yashjub,
A hankali
Daddy ya lumshe idanuwanshi…
Tabbas ya yi matuƙar farin ciki da Yashjub ya samu wadda yakeso, kuma gashi da izinin Allah zai aureta.
Yana tuna lokacin da ya auri Mommy……shiyasa a ko da yaushe yake addu’ar Allah kar ya sa d’aya a cikin ya’yan shi ya ɗanɗana kwatankwacin wannan feeling ɗin (yanayin), dan shi kad’ai ya san mai ya ji, shi kad’ai ya san zafin aurar wanda ba ka so!.

Har i yau kuma yana tuna lokacin da ya auri amaryarsa Khadijah…farin cikin da ya rayu a ciki shi yake yi wa gaba d’aya ya’yansa kwad’ayin
su samu, shiyasa ya dad’e da yi musu alk’awarin ko waye sukeso
A ko wanne irin yanayi
InshaaAllah zai shige musu gaba ba zai yi k’asa a guiwa ba wajen ganin sun mallaki juna!!!
Wannan dalilin ne yasa bai takurawa kowa a cikinsu akan yayi aure ba, saboda yana so su nutsu
kowa ya nemi wanda yake k’auna cikin nutsuwa…
Yahanasu itama gani yayi kamar tana cutuwa ne shiyasa yake saka baki a cikin lamuranta ba dan haka ba to da ba zai tab’a cewa komai ba,
dan bashida wani burin da ya wuce yaga gaba d’aya y’ay’ansa sun samu asalin ƙauna da sahihin farin ciki na gaskiya
kamar yadda shima ya samu
A
lokacin da Khadijansa take da rai!!
A hankali wasu zafafan hawaye suka shiga bin k’uncinsa…
wannan wanne irin feeling (yanayi) ne?
Ya tsaneta!
Sannan kuma har yanzu yana mahaukacin sonta da k’aunarta
Kuma
Ji ya ke kamar ya kashe kansa saboda abunda ya yi mata…
Wanda Zuwa wannan lokacin ya gama yanke shawarar
Idan Allah ya ba shi ikon ganin auren hatta Yadira, ya kuma tabbatar da Ƴaƴansa duk sun girma sun kama ƙasa za su iya kulawa da kansu
to inshaaAllah zai mik’a kanshi ga hukuma!!
Ba zai iya ci gaba da jure wannan radaɗin ba ,shi kad’ai ya san me yake fuskanta me ya ke ji a cikin zuciya da ranshi!
Babu wanda ya lura ba kuma wanda ya sani amman a ko wacce rana ta duniyar nan yana fuskantar azaba mai tsanani ne.
……..
Tun ranar da Yassir ya je d’akin Kausar ya tarar da ita suna magana da Yassira…..tun daga wannan ranar bai sake saka ta a Idanunsa ba dan wasan y’ar b’uya ta hau yi da shi gadan-gadan.
Sai yau ne tukunna ta daure da kyar ta ce ‘bari dai ta lek’a sa’.

Sai chan dare wajajen sha biyu, tukunna ta samu ta lek’a d’akin nasa, ita ala dole za ta yi mai basaja gudun kar ya fahimci komai…

Ba yabo ba fallasa ya karb’eta, dan haka ta samu kwarin guiwar zama a kusa da shi suka gaisa tukunna ta ce “kwana biyu ka ji ni shiru, sorry mun d’an sake samun matsala ne ni da Daddy shiyasa ka ga Ina kuka ranar da ka zo, to kuma tun daga ranar bani da lafiya sai yau ne na d’an ji dama-dama,’’
Ta fad’i hakan tana mamakin yadda tun ranar da ya zo ta rufe k’ofa bai nemeta ba, sannan bai sake lek’a d’akin ta ba, ko a waya bai ce mata hi ba, yau kwanaki hud’u kenan.

Murmushi kawai ya yi mata ya ce ‘kar ta damu ba komai’
daganan ya d’an ja ta da hira…
faram-faram dai haka ya yi mata kamar ba komai.

Abu d’aya ne ya bata mamaki ta inda ‘ta nuna za ta kwana a d’akin nasa’ amman sai ya ce mata ‘’its fine(ba komai), ta tashi ta tafi kawai, ita da bata da lafiya ma’’

Itanma daman hakan take so,
dan haka ta yi masa sallama
daganan ta fice, tanata mamakin sa.

Sai kamar bayan mintuna goma da fitar tata tukunna ya d’auki wayarsa ya shiga ya kira wata number, tana fara ringin ya mik’e ya fice ya tsaya a balcony d’insa wanda yake opposite inda ake parking motocin gidan….
Har ga Allah bai shirya yin haka tun yanzu ba!
Ya so ace ya bashi wahala ya kassara shi tukunna sai yayi shawara abunda zai yi
masa a gaba
amma Kausar ta janyo komai,
ya lura barin shi a doran k’asa yana numfashi had’ari ne a garesa ta ko wanne fanni!!..dan haka dole a yi gama kawai.
Dakyar yana jin yanda tunanin ya sake tunzura zuciyarsa ta fara tafarfasa ya ce ’’ba kowa
ta nan, cameras d’in ma na tsaida su
Ka yi sauri kafin su yi zagaye.’’

Yana nan tsaye a wajen a yadda ya ke d’aya
daga cikin masu yi wa gidan hidima wanda suka gama wayar dashi kenan
Ya lallab’o ya je shi jikin motar da Yashjub yake fita aiki da ita kullum ya kunce tayoyi biyu ba duka ba…ya kunce su ta yadda ba za ayi tafiyar mintuna biyu da motar ba tayar gaba da ta baya waenda ya kunce d’in za su fita .

Sai da Yassir ya ga Mutumin ya kammala komai ya koma inda ya fito tukunna
shima ya koma d’akinshi ya rufe k’ofar balcony d’in, yana jin wani nauyi yana sauk’a daga kan k’irjinsa.
Addu’arsa d’aya ‘Allah yasa kar Yashjub ya bashi mamaki gobe ta hanyar chanza motar hawa’
Yayinda a d’ayan b’angaren zuciyarsa yake mamakin Kausar da kuma tunani da lissafin abunda zai yi mata idan zarginsa a kanta ya tabbata, hatta Yassira itama sai ta karb’i rabon ta wallahi,
dan ya lura tabbas itama ta san wani abun daman tun ba yau ba!
Za su san sun yi wasa da hankalin shi kuwa.
…….
A gidan dai ranar Yashjub ne kawai yayi baccin kirki..
Mommy da Baba Larai, za a iya cewa sun fi kowa tashin hankali!Saboda zuwa wannan lokacin su kansu sun san da tahowar auren gadan gadan!
Gashi sun nemi ko wacce kalar mafita sun rasa…dan aiki akeyi tuk’ura amma kamar ma rura wutar abun ake yi wanda hakan ne ya sake hautsina su saboda ba su tab’a zaton abun zai gagare su har haka ba.

Yahanasu kuwa tana chan shoppping online, dan Yashjub ya sanar mata yadda suka yi da Daddy shiyasa ta fara dudduba kayayyaki tun ayau saboda ta ga babu lokaci.

Daddy kuma takaicin abunda Ummi take yi masa ne ya hanasa bacci.

Kausar da Yassira ma kowacce a rikice.

Ummi takaici da tsanar Daddy ne ya hanata bacci.

Munirat kuma d’abiun Yassir ne suka taru suka d’aure mata Kai!
Shiyasa ta b’ata lokaci tana
Shawara akan ‘ta ci gaba da kula shi ko ta rabu da shi kawai’
ita dama bata da wani abokin shawara dan bata iya hulɗar ƙawance ba
ƴar uwarta kuma da Ummi duk
fushi sukeyi da ita har yau, sun k’i su sake mata bayaga hakan ma ko da ace sun sake mata d’in ita kanta ta san
bata isa ta tunkare su da maganar soyayyar ta da Yassir ba wanda ta san hakan ne ummulaba’isin fushin na su da ita.

Yasmeen da Ya’isha suma duk hankalin su a tashe yake,,ga kuma k’unci da tashin hankalin da suka gani tartare a fuskar Mommy da kuma abunda Yashjub da Yahanasu sukayi duk sai hakan ya taru ya b’ata musu rai, shiyasa suma suka gagara runtsawa.

Yassir kuwa abubuwa biyu ne suka had’ar masa
Na farko yanaso ya kawar da Yashjub
saboda komai ya dawo Hannunshi kuma ya na so ya yi hakan da wuri ko dan ya samu ya gano gabas d’in Kausar

Amma fa duk da taurin Zuciya irin tashi tun d’azu yake fargaba…ba wai fargabar kashe d’an uwanshi da ya shirya yi ba,
Yana fargaba ne akan kar zarginsa akan Kausar ya tabbata dan idan ya tabbata ɗin to
bai san me zai ji ba!
bai kuma san mai zai zama ba muddin ya tabbatar da cewa ‘Kausar tana son wanin shi,
wanin ma yayan shi,
sannan har su Yassira sun sani amman suke yi masa rufa-rufa
suka munafurcesa’
tabbas ya san in zarginsa ya tabbata hakan ne to
ya zama ba shi da kowa a tare da shi kenan
dan haka kansa kawai zai ke dubawa ko Yassira da yake ji da ita a matsayinta na tagwayensa ba zai sake bi takanta ba tunda suma basu damu da damuwar sa ba.!

Waennan tunane-tunanen
da kuma zullumin son ganin gobe ne suka hana shi bacci.

Sai da aka fara kiraye-kirayen assalatu tukunna da taimakon shed’an ya samu wani bacci mai d’an karen dad’i ya kwashesa……..
Chapter 84 · 0% Book details