Sashe 26
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nan ya tarar da Ya Musbah shi da Jidda suna ta lallab’a Inna wadda take ta faman hawaye.
Dan Baban yana fita sukayi la’akari da ita ashe ta farka tun tuni basu sani ba, saida Baba ya fara umartar Ya Musbah akan
ya je gida ya duba Baraka da mai sunan shi yaga komai kalau tunda tun safe yake asibiti kuma da suka dawo bai je ya lek’a gidan nasa ba.
Ba dan yaso ba ya tafi,
tukunna shi da Jidda suka ci gaba da lallab’a Inna………
Sai da su Manubiya suka kusa awa biyu tukunna suka dawo daga gidan Ammi duk su biyun jikinsu a sanyaye. Jidda kawai suka samu a d’akin ita da Inna wadda suka lallab’a dakyar daga nan ta sha maganinta bacci ya d’auke ta,Jiddan ce ta ce musu ’’Baba ya fita yanzu bai dad’e ba’’.
A hankali Muhsin ya ce’’Bara in je wajen shi, na san yana masallaci’’ daga haka ya fice ya bar musu d’akin.
Yanayin yadda Jiddan ta ganta ne ya sanya itama cikin mutuwar jiki tace ‘’lafiya dai ko? na gan ki wani iri’’.
A hankali Manubiya ta ce
“Wai har mun fara yau fa,
shiyasa ma kika ga mun dad’e.
Aikin ba sauk’i gaskiya kuma a haka kinga yanzu dare ne so na san na safe zai fi wahala…
wanke-wanke da shara mukayi yau, tace kuma gobe har da girki.
Muhsin kuma da muka je da niyyar ya dinga tayani
ta ce shi zai dinga sharar wannan makeken tsakar gidan mai uban girma, albashin mu dubu goma goma, a wata dubu ashirin mu biyu.
In Allah yasa su Baba sun samu kud’i masu nauyi watak’ila wata d’aya ko biyu kawai za mu yi muna aikin, na bata har wayar da ya baki ma’’.
Manubiya ta k’arashe maganar tana mai cire hijabin jikinta.
Ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin tace
‘’Adda Manu ko ni in karb’a ke ki huta ki yi karatun ki cikin kwanciyar hankali’’.
A hankali Manubiya ta koma kusa da ita ta zauna kafin ta ce
‘’Jiddah,a yadda matarnan take jin zafin ki idan kikaje mata gidan da sunan aikatau tsaf za ta iya cutar da ke, kuma bayaga haka ma bai kamata ke d’in ki je ba so ki bari karki damu ni da Muhsin d’in za mu yi, za mu iya’’.
Cikin zubar hawaye Jidda ta ce
‘’Adda Manu,ta yaya za ayi ni na yi laifi amma ace kune zaku biya price d’in
A Ina aka tab’a yin haka?’’.
Cikin d’an jan kumatunta Manubiya tace ‘’A gidan Baba, gidan da y’an uwa suke matukar k’aunar junan su, gidan da kai yake a had’e! Har ta kai
Idan abu ya shafi d’aya tou ya shafi dukkan mu, gidan da mu ke so mu nunawa Jiddan mu tana da gata’’.
This time around fashewa da kuka Jidda tayi ta fada jikinta ta rungumeta a hankali ta ce
‘’Nikam kar ku yi ku barshi zan yi in kuka yi bazan tab’a yafewa kaina ba..
Kullum zan dinga gani kamar na shiga hakkin kune’’
A hankali Manubiya ta ce
‘Jidda ki kwantar da hankalinki, bau komai kinji ko?
Kuma inaso ki saka a ranki muddin za ki ci gaba da kula Al’ameen tou abunda zai faru damu kenan.
dan Allah Jidda
For the last time ki fita harkar Al’ameen har abada’’.
Ahankali Jiddan ta cika ta ta d’ago tana kallon ta kafin ta ce
‘’na riga na gama yi wa kaina wannan alk’awarin!
InshaaAllah babu ni ba Yw Al’ameen, kawai dai dan Allah kar ku bari a aura min Ya Yusuf,
Wallahi bana son shi’’.
Cike da bata assurance had’e da kwarin guiwa Manubiya ta ce
“Su su uncle d’in wacce rawa suka taka tun daga haihuwarki har kawo yanzu da kike tunanin zamu bar su su yi miki auren dole?
ki kwantar da hankalinki kin ji ko!
InshaaAllah Yusuf sai dai ya ganki ya bari.’’
Ahankali Jidda ta sake hugging d’in Manubiya tanajin wani kwanciyar hankali a cikin ranta, harga Allah bata son Ya Yusuf!
bata san ya za ta yi ba
Idan k’addarar Ubangiji ta sanya ya zamto mijin ta ba, da sauri a ranta tace ‘’ya Allah kar ka sa in auri ya Yusuf,alfarmar annabi s.a.w’’.
Shiruu ta yi tana tunani
kafin ta d’ago ta gyara zamanta tukunna ta ce
‘’duk naga kin yi kalar gajiya
kin gaji sosai ko? bari in je in d’eba miki ruwan wanka, in d’aura
na fanfon ya d’auke’’.
Murmushin yak’e Manubiya ta yi kafin ta ce
‘’Mun riga mun tara ni da Muhsin kafin mu shigo,sai da ma muka d’aura a kitchen tukunna muka shigo nan, na san zuwa yanzu dai bai yi ba’’…
…Tun ranar da ta gan shi notunan kanta suka kwance, sanin da ta yi cewa sam shi d’in ba sa’an ta bane ba ta ko Ina, hakan ya sanya ta yi wa kanta fad’a! sannan ta dage da addu’a da sallar dare da nafilfili….
Ta samu sauk’i kuwa!
sai dai kuma bata san k’addarar da ta kai ta gidan Ammi ba yau ɗin gidan da tun da take a rayuwarta bata tab’a shiga ba!
Shin wacce irin kama ce tsakanin Matar da ta tarar tana yi wa Ammi kitso da wannan bawan Allahn da ta gani a office d’in Sir Najeeb sati biyu baya da suka wuce?…
Tunda ta ga Matar kuma tashi d’aya sai tunanin Mutumin ya dawo mata sabo fil.
“Innalillahi wainna ilaihirrajiun!!
Ya Allah kar ka d’aura mini abun da zai zama ajalina, ya Hayyu ya Qayyom kar ka ɗaura mini abunda ba zan iya ba’’.
Ta fad’a a chan k’asan ranta…..
Anya kuwa zata iya ci gaba da aikin gidan Ammi tana karo da wannan Fuskar kullum,dan ta lura matar kamar a gidan take saboda
inda ace zuwa ta yi tou da da ta gama yi wa Ammin kitso da zata tafi amma sai ta ga ta kama wani aikin kuma na daban, babban tashin hankalita shine
kar ta je shima Mutumin a gidan ya ke!!!
Dan tabbas maybe in dai ba tsananin kamanni ba to matar nan yayar sa ce. Ta san cewa Ammi d’a d’aya gare su ‘Al’ameen’ to kenan wannan mutumin y’an uwansu ne? da shi da yayar tasa a gidan suke kenan?
Inaa ba zata iya ba, saboda
gani d’aya ta yi masa lissafinta ya kwance shin ina kuma ga idan ta ci gaba da ganin shi kulliyaumin?……
‘’Adda Manu, ya kawo ruwan fa’’
Jidda wadda take ta faman yi mata magana bata kula ta ba tun dazu, ta fad’i hakan da d’an k’arfi.
A d’an firgice Manubiya ta yi firgigit ta d’ago tana kallon ta kafin ta samu da kyar ta had’iye wani abu wanda ya tokare mata mak’oshi tukunna a hankali tace’’Ok‘’.
kafin ta kalli Muhsin wanda ya dawo daga mik’a ruwan band’akin ta ce
‘’Na gode auta,bari in yi in rage maka’’.
Tana gama fad’in haka ta mik’e
ta d’auki abubuwan da zata buk’ata ta fad’a band’akin. …
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*16*
Tana fitowa daga wanka,
aka aiko kiran su daga wajen Kaka Mallan.
Muhsin kawai suka bari a wajen Inna su duka suka d’unguma.
Uncle,Ya Yusuf,Baba Habu Anty Umma sai Kaka Mallan suka tarar.
Ko gaisawa Uncle bai bari an yi ba dan yana lura babu Ya Musbah ya d’au waya ya hau kiransa yana mitar ‘ya an ce za’ayi meeting, amma an bar shi ya tafi,bai zo ba’.
Sai da aka jira ya zo ya fara bud’e taron da addu’a tukunna Uncle ya bari ma aka gaggaisa.
Ba tare da b’ata lokaci ba
Kaka Mallan wanda ya amsa gaisuwar su Baba da kyar ya kalli Baba ya ce
‘’Musa’’!
Sai da Baba ya lumshe Idanunsa ya bud’e tukunna ya ce ’’Na’am,Kaka.’’
Sai ya d’an nisa tukunna ya ce
‘’Dazu d’an uwanka ya zo ya same ni akan batun Matar senator da y’ar wajen ka, an yi part 2 kenan?’’
Shiruu Baba ya yo kafin chan ya ce
‘’InshaaAllah hakan ba zata sake faruwa ba, na tsawatar mata’’.
Cikin d’an daka tsawa Kaka Mallan ɗin ya ce
‘’Kai dallachan gafara, ka tsawatar kuma na yaushe, kwanakin baya ba an tsawatar matan ba amman ka ga alamun ta yi amfani da tsawatarwar?.
kuma tsabar cin fuska da rashin sanin ya kamata
MUSA, Yusuf fa da Mahaifinsa suna cikin gidan nan amman kuka barta take kula wani ‘Al’ameen’.
Dama na fahimce ka tun ba yau ba,komai naka daban yake…..
Duk wata hanyar da zaka bi ka salwantar da had’in kan zuri’ar nan tou ka sani, kai kenan ace komai naka a botsare? kuma duk in ka je ka dawo baka ganin dai-dai sam amma taurin kai ya ƙi bari ka saduda?
Ka duba kaga yadda ka kafe akan kasuwanci kana ganin babu riba amma dukda haka sai da ka d’aura Musbahu akan kasuwancin shima, kana gani y’an uwanka suna karatu amma kai ka nacewa abu d’aya gashi yanzu a ta dalilin botsarancin ka kai da iyalin naka gaba d’aya kun zama abun tausayi.”
Da sauri Manubiya ta mik’e ta juya za ta fita.
Cikin karsashi Kaka Mallan ya ce’’Wallahi zan ci ubanki, ni zaki mik’e ki fitarwa ina tsaka da magana, saboda na fad’i gaskiya?dawo ki zauna tun kafin in saka Yusuf ya ladaftarmin da ke’’.
Ko gezau Manubiya bata yi ba,
bata fitan ba kuma bata koma ta zauna d’in ba, har sai da Ya Musbah ya daka mata tsawa ya ce ’’Wai ba da ke ake magana ba?’’Tukunna ta koma ta zauna tana ji kamar ta fashe tsabar takaici.