← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 84

Sashe 17

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kawai ya yi kafin ya ce
‘’Jidda I love you.
Na san Ammina
tana son duk abun da nake so,
wanchan karon ma mishkila aka samu kuma bana nan amma yanzu komai ya daidaita.
Ki kwantar da hankalinki dan Allah,
ta ce ma zata zo har nan ta duba Inna,
sannan ta ce in cewa su Baba su yi hak’uri komai ya wuce.
Kuma ko yau kafin in fito ma sai da muka yi magana da ita akan
‘Ina dawowa daga tafiyar nan da zan yi im sha Allah za a fara maganar auren mu kuma ta amince d’ari-bisa-d’ari, ta ce ba za ma a d’auki lokaci mai tsayi ba, Abba kam dama shi ba shi da problem da auren tun farko.
So please had’in kanki kawai nake nema a yanzu.
Na san kwanakin baya dole kun ji babu dad’i kuma kun ji haushi amma pls darling ki yi hak’uri ki yafewa Al’ameen d’inki ki yafewa Ammi itama kin ji…”.
Ya ƙarashe maganar kamar zai fashe mata da kuka.

Shiruuu Jidda ta yi ta fad’a duniyar tunani…
Ita kanta ta san k’arya takeyi idan ta ce bata son Ya Al’ameen wanda tun tana ss1 su ke soyayyar su a b’oye a layin, saboda a lokacin ta san Baba ba zai tab’a barinta kula samari ba.
Haka Al’ameen ɗin ya yi hak’uri yayi ta jiran ta har ta kammala tukunna ya baiyyanawa Baba da Ya Musbah manufar sa…
Sun kuwa yi farin ciki ba wai dan saboda tsananin arziƙin Mahaifin shi ba wanda kaff Unguwar ba za’a nuna wanda ya kamo k’afarsa a kud’i ba!
Sai dan hankali da sanin ya kamatan Al’ameen d’in.

Duk arzik’in Mahaifinsa shima bai nuna k’in amincewa ko kyama ba, farin ciki ma ya yi da ɗansa ya samu wadda ya ke tsananin so har haka…
Amminsa ce a lokacin ta kafa ta tsare ta zuba musu tujara sosai
Sannan ta ce
‘sam bata yarda d’anta ya auri y’ar talakan miskini ba’.

To yanzu kam in dai Ammin tasa ta amince kamar yadda ya fad’a
shikenan ai bata da wani issue sam,
Ammi kamar uwa take a wajen ta kamar yadda Al’ameen ya nemi ta yafe mata tsaf zata yafe mata dukkannin abunda ta yi mata ita da ahalinta wannan ba matsala bace ba..

‘’Jidderty’’
Ta ji ya kira sunan ta.

A hankali ta ɗan kalle sa sai kuma ta sunkuyar da kanta.

Zai yi magana kenan Manubiya ta turo k’ofa ta shigo…
Suna had’a Ido da ita ya fara murmushi kafin ya ya ce
‘’Yayata wadda bata k’aunar gani na’’.

Cikin tarar numfashinsa ta ce
‘’Ka fad’a da k’arfi ka buga a jaridar da zata fita gobe, dan maganarka hakan take’’’

Da sauri Jidda ta ce
‘’Adda ‘’

Wani kallo Manubiya ta yi mata dan haka ta ja Bakinta ta yi tsit! Sannan ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba.

Kusa da Inna kawai ta k’arasa ta nemi waje ta zauna ta had’e rai, taso ta wanke Al’ameen
amma sai takaicinsa da na jidda suka hanata iya cewa komai.

Sun fi mintuna talatin a haka
kafin daga baya Al’ameen ɗin ya mik’e ya ce
‘’ni zan wuce’’

‘’Mun gode’’ kawai Jidda ta xe
Manubiya kuma ta mike ta ce
‘’Mu je, ina son ganin ka’’

Ko da suka fita nicely
Manubiya ta rok’e sa akan ya daina bibiyar su…

Amman sai ya tabbatar mata da cewa
‘’Ai Ammi ta sauk’o, ta ce a basu ma hak’uri kuma zata zo da kanta ta duba Inna’’

Ita dai Manubiya still cewa tayi
‘’Ya d’an jira sannan ya daina yawan zuwan
har sai an tabbatar da amincewar Ammin,
domin su a yanzu rikici da tashin hankali is the last thing da za su yi involving kansu a ciki ‘’

Ba dan ya so ba sai dan yadda Manubiyan ta dage,
haka nan ya ce mata’’ tou ‘’
kawai ya wuce.

Ko da ta koma ciki ma
sai da ta zubawa Jidda serious warning
kuma ta ga jiddan ta yarda tukunna ta kyale ta.
Tana kokwanton maganar Al’ameen
‘Wai Ammi ta yarda ya auri Jidda ‘

*Bayan Sati Biyu*
Successfully aka yi aikin Inna,
Manubiya da Jidda ne suke yi mata wanka da komai dan har yanzu b’arin Jikinta sam baya aiki, ko magana ba iyawa take yi ba.

Sun so su koma ward amma sai aka ce musu ai Al’ameen kud’in wata d’aya ya bayar so koda ace ba a kai one month d’inba
ya ce su za a bawa chanjin.

Tunda Jidda take a rayuwar ta bata tab’a b’oyewa Manubiya wani abu ba sai wannan karon..
Dan a washegarin ranar da Manubiyan ta ce kar ta sake kula Al’ameen sannan shima kar ya sake zuwa ma sai da ya dawo kuma ya sake cin sa’ar samun Jiddah ita kad’ai
lokacin Manubiya ta tafi allura.

Ganin tsoro k’arara a Idanun Jiddahn ne ya sanya ya ce mata “gobe zai dawo Karfe 4 na yamma”yayi mata kwatancen in da za su had’u.

Haka nan su ka dinga yi
Idan lokacin zuwan sa ya yi sai ta kwashi wanke-wanke ko ta karb’a sak’o
In ta je bata dawowa
sai sun sake had’a Appointment na inda za su had’u washegari.

Shi Al’ameen baya son causing mata problem da su Manubiya
kuma Ammin nasa bata samu daman zuwa ba ta tafi ummara
Shi kuma yana ganin tunda har mahaifiyarsa da mahaifinsa sun amince a gaskiya ba zai iya yin nesa da Jiddah ba,
dan yana mutuwar k’aunar ta.

Ita ma jiddan tana son abunta
Kuma saura masa sati uku a lokacin yanzu kuma saura sati d’aya ya tafi wani course da zai yi na 4weeks
Shiyasa kawai ta amince
kuma ta b’oyewa Manubiya dan kar ta hanata….
A cikin sati biyun nan kuwa
soyayya da shaƙuwa ta sake ƙulluwa tsakanin su bata wasa ba.
•••••
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*09*

*2 weeks ago*
*(sati biyu baya)*

Kamar yadda Mommy ta yi tsammani…
Washegari da safe ba zancen auren Yassir da Kausar!
Sannan babu Daddy babu alamun sa.
Ita a tunanin ta fushi yayi ya zauna a ɗaki, sai da dare yayi
ta je domin ta kai masa dinner tukunna
ta fahimci ashe bama ya gidan gaba d’aya!
Dan a nan inda ta ajjiye masa breakfast da lunch a kan dining table ɗin parlourn nasa
anan ta dawo ta same su yadda ta ajjiye babu ko alamar an tab’a ma.

Tabbas ta d’an firgita musamman ma da ta shiga d’akinsa ta tarar ya kwashe kusan kaff kayansa,tun anan ta sha jinin jikinta sannan ta fara da na sanin ambato masa ‘Khadijah’ da ta yi a jiyan bayan k’wak’kwaran warning ɗin da ya zabga mata ita da su Yahanasu akan kar wanda
ya kuskura ya yi zancen ko ya ambato ko da sunan Khadijahn ne a cikin gidan..

Tana tsaye tana tunanin ta hanyar da zata bi ta shawo kan Daddy domin ta san ba k’aramin yaji yayi mata ba,
Yassir ya shigo.

A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya domin tun safe yake tambayar ta ‘ina Daddy’
ita kuma ta zabga masa k’aryar ‘Daddyn ya ce sai gobe za a d’aura musu auren sannan ya tafi shirye shiryen gidan da za su zauna ne, shiyasa bai gansa ba.’

A b’angaren Yasir kuwa
dama tun d’azu da safen da ta fad’a masa maganar bai wani gasgatata ba shiyasa gaba d’aya tun safe hankalinsa a tashe yake!
Kausar itama ta k’i ta bari ya ganta, ta kashe wayoyinta!
Daddy baya amsa calls d’insa,
Mommy kuma ya lura kamar avoiding d’insa ma takeyi(wasar ƴan ɓuya take yi da shi).

Jiya bai yi barci ba sai da ya had’a Dinner ta gani ta fad’a wadda za a gudanar a yau da daddare bayan an kai masa Kausar gidansa,kusan kaff Abokanayen su babu wanda bai fad’ama yau auren shi da Kausar ba, a dai dai wannan lokacin side d’in su shi da Yashjub a cike yake taff da abokanayen su waenda suke gari maza,matan kuma ya kaisu side d’in Yasira dan kausar ta yi wuyar gani.

Abhankali ya taka ya isa gaban Mommy ya tsaya, farar Fuskarsa har ta yi jajawur dan tashi d’aya ya hango rashin gaskiya a tare da Mommyn…
Manyan Idanuwansa da suka yi jazir ya zuba mata kafin ya ce
‘’Mommy stop toying with me(Mommy ki daina yi
mini wasa da hankali)
na rok’e ki da girman Allah ki fad’a mini me ke faruwa’’

Sam, Mommy bata yi tsammanin wannan ɓacin ran daga Yasir lokaci d’aya ba! Dan
hatta jijiyoyiin kansa sun fito sun yi rud’u-rud’u, kan dogon hancinsa ma yayi jaa sosai.

A hankali cikin in ina ta ce
‘’Son,mun d’an samu matsala ne da Daddyn naku jiya,so ya yi fushi ya tafi.’’

Ba tare da ya daina kallon ta ba
Cikin tarar numfashinta ya ce
‘’Ina yaje???’’

A d’an rikice ta ce
‘’In da ace na sani da zan fad’a maka,’’

Da d’an k’arfi ya ce
‘’Dole kin sani, ai na san da gangan kika janyo fad’an saboda ba kya son auren ba kya son farin cikina, dan haka dole ki sani kuma dole ki nemo sa,haba Mommy how could u????
kin fi son farin cikin Kausar akan nawa ne???
kamar ba ni ne d’anki ba.’’

Da sauri ta matso ta kamo Hannusa kafin ta ce
‘’Ba haka bane ba Yassir, wallahi duk abun da ka ga nayi
Gaba nake hango maka, farin cikinka da dauwwamar cikar burin ka shi nake tayaka nema…
Kai farin cikin yanzu kake so ka samu
Ni kuma hangen nesa nakeyi maka. Yassir ka fahimce ni ka yarda dani duk abun da na yi wallahi
nayi ne saboda kai kad’ai,
Trust me.’’
Chapter 17 · 0% Book details