← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 84

Sashe 63

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take a alokaci d’aya fuskar black snake ta chanza daga jin batun dpo, cikin fushi ya d’ago yana kallon kowa….sai kuma yayi lissafin ai mutanen nan basu da ƙarfi da hanyar da za su kira someone influential (babban mutum) haka.
Wataƙilan dai wani Abokin hamaiyyarshi ne ya ji labarin zuwan sa shine akayi masa chune!.
Bayaga hakan ma ai tun d’azu yana tare dasu Manubiyan kuma babu wanda ya ga yayi waya a cikin su.

Yana wannan tunanin ya ji dpo yace
‘’Sir,wannan ba lokacin tunani baneba,u need to leave, now!(ya kamata ka tafi, yanzu yanzu).
ka san su kamar aljanu, yanzun nan za ka ga sun k’araso.’’

Cikin fushi black snake d’in ya juya buguzun-buguzun
Ya je shi ya damk’i hannun Manu ya fara janta sannan ya cewa yaran nasa su kamo
Jidda
duk wanda kuma yayi yunk’urin hanasu to su kaishi lahira.

Ya Nafi’u ne ya danne zuciyarsa da kyar ya iya rik’e Ya Musbah dan ya san muddin suka shiga to kashe su mutanen nan za su yi kuma in sun mutu ba za su samu su kwato su Jiddan daga hannunsu ba.

Da kyar Baba ya iya had’a gaba d’aya k’arfinsa da ragowar kuzarin da ya rage masa ya samu ya mik’e tsaye,jikinsa
yana karkarwa ya tsaya a inda black snake yake k’ok’arin bi ya wuce,yace’’ka kashe ni kawai!
A kan dai in bari ka tafi da y’ay’ana har biyu a gaban idona, gara kawai ka kashe ni!’’.

Wani wurgi black snake ya yi dashi wanda ya sanya shi ya tafi ya je ya daki gini….
Cikin fushi black snake ya cd
‘’Ban tab’a had’uwa da tsoho mai audacity (tsaurin ido) irin ka ba!
kar ka damu ba zan kashe ka ba amma tunda na lura kamar ka fi son wanchan Yaron naka mai kama da kai a cikin y’ayan naka maza to shi zan kashe’’.
Ya yi maganar yana nufin
Ya Musbah.

…Now(yanzu)…

‘’Ba za ka kashe kowa ba black snake’’
Muryar jami’in dss d’in da suka shigo taree shi da Yash ta
katsesu, sannan ta maida hankalin kowa gare su.

A take Yashjub ya ji ransa yayi wani irin b’aci na ban mamaki, zuciyarsa ta cunkushe tana tafarfasa sakamokon yadda ya ga black snake ya k’ank’ame Hannun Manu,
gashi sai k’ok’arin kwacewa takeyi tana wani irin kuka, kuma ko damuwa ma bai yi ba.
Sannan daga ita sai doguwar riga da hula, wuyanta duk a waje!.
Bai san lokacin da ya k’arasa ya fincike hannunta daga cikin na black snake d’in ba sannan ya hankad’asa gefe.

Wani irin murmushin takaici black snake yayi kafin ya ce
‘’Yashjub!the hero..we meet again!
(Jarumi Yashjub, mun ƙara haɗuwa kenan…)”

Banza Yashjub ya yi dashi, kawai ya juya inda ya hango hijabin da ya gani a yashe wanda yake da tabbacin na Manu ne, ya k’arasa ya je ya d’auko ya mik’a mata yana mai k’ok’arin danne fushin sa.

Dai dai nan jami’in dss tare da dandazon y’an sandan da suka biyo bayan su da shi da Yashjub suka yi kan black snake

Ba tare da tantama ba
Black snake ya harbi ss d’in a ciki
wanda hakan ya sanya gaba d’aya y’an sandan suka rufar masa, dama rabi a cikinsu duk bakinsu d’aya da dpo ba wai son kama black snake d’in sukeyi da gasken gaske ba.

Ai kuwa hakan ya bashi dama da shi da tawagar sa suka fice da gudu
Bayan ya kalli Baba ya ce masa “zan dawo d’aukar matata, nan ba da jimawa ba’’

Da sauri Yashjub yayi kan jami’in da aka harba, ganin
yana motsi yasa yace gara a yi sauri danne gurin su kai sa mota a wuce dashi asibiti.
Shi kuma ya bi bayan su black snake da gudu
amman ya na zuwa
sai k’urar motocin su kawai ya tarar.
‘’Damn it!!’’
Ya furta da k’arfi, yana jin
takaici kamar ya kurma uban ihu.
Dai-dai nan motar Najeeb ta k’araso cikin harabar gurin tare da dandazon motocin jami’an dss.

Najeeb yana k’arasowa yace
‘’Kar ka damu,rabin motocin sun bi su,za’a kama shi in sha Allah,bai dai tab’a kowa ba ko?’’

Cikin b’acin rai Yashjub ya ce
‘’Ya harbi mutane uku’’

A rikice Najeeb yace’’subahanaallah,da wa da wa?? ina Manubiyan take?’’

‘’Tana ciki!’’
kawai Yash ya iya cewa,
daga haka ya juya ya nufi ciki
bayan ya kira ambulance,
dan wani irin takaici yake ji,ya riga ya san dole ba za a iya kama black snake ba.

Suna shiga polisawan da wasu a cikin ss d’in suna fitowa d’auke da jami’in da aka harba.
Statement ya tarar ragowar ss d’in suna karb’a a wajen ya Musbah da ya Nafi’u yayin da Jidda da Manubiya suke kuka suna dudduba Baba.

Dukda abunda black snake ya aikata sai da Yashjub ya karb’i acc number d’insa a wajen dpo ya tura masa 1 million d’insa da yake bin Baba, bayan ya ji bayanin komai da ga Bakin dpo.

Zuwa wannan lokacin gaba d’aya ran Yashjub ya kammala b’aci daga jin bayanin, tabbas in da ace zai ga black snake yanzu to kuwa in bai kashe sa ba sai ya sumar da shi, musamman ma da ya ji cikakken labarin maganar auren da ya so a d’aura masa shi da Manubiya!…
‘wato da niyyar auren Manubiya ma yake yi!’
Idan ya yi tunani akan
‘Black snake d’in fa yayi tunanin auren Manubiya, kenan
ta kwanta masa shima son ta
yake yi’,
sai ya ji kamar ya bazama ya nemo shi ya chaka masa wuk’a.
Dan mai yasa zai yi wannan tunanin a kanta!.

how dare he!.
*MANNUBIYA*
*38*

Shiyasa har aka gama case ɗin….aka gama karb’ar statements d’in su,
suka nufi asibiti sam fuskarsa babu walwala!
Ya had’e girar sama da ta k’asa, ko magana ma ya daina yi.

Private hospital aka nufa da Baba da Abbakar, suna zuwa aka karb’esu emergency.
……
Wayar da Yashjub ya yi aka tabbatar masa da ‘black snake ya gudu, ba a samu damar kamasa ba’
ne ya sake harzuk’a shi.

Dukda halin da take a ciki sai da ta lura da shi dama tun ɗazu..
yanzun kuma ta tabbatar wayar da aka yi masa ce ta sake b’ata masa rai…
So take yi atleast (ko ma ƙa-ƙa dai)
ta je ta ce musu sun gode, dukda ta ga su Ya Musbah sun yi musu godiya sosai har karɓar nambobin juna ma taga sun yiyyi, amma dai dukda haka ya kamata su je su yi musu godiya suma ita da Jidda, sai dai kuma tana shakkar kar ta je ya maketa!
Dan in ba lokacin da su ke exchanging numbers shi da su Ya Musbah ba to bataga ya saki fuska dede da na second d’aya ba!…Sannan kuma
tana jin kunyar sa dan in ta tuna abunda ta yi masa jiya da safe gaba d’aya sai ta ji wani iri babu dad’i! duba da yadda yanzu yake tsaye tsayin daka akan al’amarin da ya kusan tarwatsa rayuwarta da ahalinta.

Gashi yanzun kwata-kwata bata hango walwala a tare da shi ba,
masifa ya ke yi wa kowa hatta sir Najeeb yanayin yadda ta ga yana masa magana kamar zai rufe sa da duka take gani….
waennan dalilan ya sanya ta d’an dakata tana mai tunanin ta yadda za ta yi masa godiyar.

Sallar la’asar aka kira, dan haka gaba d’aya Mazan suka fita masallaci, su kuma suka nufi band’akin da suka tambaya aka nuna musu…
Sallah kuma suka nemi waje inda babu mutane sosai, suka gabatar da ita cikin nutsuwa.
Bayan sun idar sukayi addu’oin samun lafiya wa Baba da Abbakar, har ma da Inna.

Basu dad’e da dawowa wajen ba su Yashjub ma suka shigo, shi da
sir Najeeb su Ya musbah a bayansu.

Ba k’aramin dad’i Manubiya ta ji ba, dan bata yi tunanin za su dawo su jira har sai an gama treatment d’in su Baban ba,
hakan ya sanya har bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba, tana murmushin tana kallon Yash d’in….
dai-dai shi kuma ya d’ago kansa shima da niyyar ya d’an saci kallon ta ai kuwa karaff suka had’a ido da ita tana kallon sa tana murmushi.

Da mugun sauri ta sunkuyar da kanta k’asa, ta fara wasa da y’an yatsun hannun ta…
murmushi sosai ne ya kufcewa Yash wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili!
Dasauri sir Najeeb ya d’ago yana kallon sa…
ganin inda yake kalla yana murmushin ne yasanya Najeeb d’in yin wata y’ar guntuwar dariya kafin ya ce ’’Romeo, a asibitin ma ba za’a d’aga k’afa ba?’’

‘’Hmm’’
Kawai Yashjub ya iya ce wa Najeeb, dan gaba d’aya Manubiya ta sanya shi a wani yanayi, shiyasa ko iya juyawa ya kalli Najeeb d’in ma bai yi ba, saboda gaba d’aya idanuwansa da hankalinsa kacokam suna akan ta ne!
So yake ta sake d’agowa ya kalleta amman sam tak’i, ta ma yi k’asa da kanta sosai.

Ganin ta ƙi d’agowa shi kuma zullumi yana shirin susuta shi ne ya sanya kawai ya nufi inda take.
Dama kuma yanata so ya d’an yi mata maganar ‘ko akwai wani abun bayan wanda dpo ya gaya mishi’ amma ya lura tanata kuka, shiyasa ya d’aga mata k’afa saboda jin kukan nata yake yi har cikin ransa a lokacin da take yi….dan har ga Allah ya san in ya je kusa da ita tana wannan kukan to tsaf za’a iya samun matsala, kukanta yana cikin abubuwa mafi munin da baya buk’atar gani a duniyar nan…….

A take Manubiya ta fahimci inda take yake nufowa, dan haka tashi d’aya fargabarta ta k’aru, dama ga fargabar jikinsu Baba dan ma an tabbatar musu da jikin na Baba
Ba wani abu me muni bane
Abbakar kuma yanada rai.

Tana wannan tunanin ta ji shi a tsaye a kanta, ji ta yi kamar ta mik’e tsaye ta ruga a guje.
Ba ta ida jan numfashin da ya mak’ale take kokawar janyoshi da kyar ba ta ji yace’’in zauna??’’

Dakyar da mugun kyar dan sai da ya sake maimaitawa tukunna ya ga tad’an matsa kusa da Jidda sosai sannan ta ce masa’’eh’’ a hankali.

Murmushi yayi kafin a hankali ya nemi gefenta da d’an tazara kad’an ya zauna cikin nutsuwar sa bayan yayi bismillah.
Chapter 63 · 0% Book details