← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 84

Sashe 12

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Kausar ta matso kusa da ita, daf! Sannan ta ce
‘’Ko kuma dai kin janyo mini ba, dan inda ace ba ki zo kina hargagi da shouting(ihu) ba ai da bai ji ba, na san dama ai abun da kike so kenan…so kike yi ya ji ɗin kuma gashi ya jiii!!!
Sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, tunda burin ki ya cika!!!’’.
Tana gama faɗin haka ta wuce sama da gudu tana kuka….
Ko akwatinta bata jira ɗauka ba.

Mommy ta daɗe tsaye a wajen kafin da kyar ta jaa k’afafuwanta, ta wuce…
Hawayen Kausar suna ɗaya daga cikin abubuwan da bata ƙaunar gani a duniyar nan…
•••••••
Tunda garin Allah ya waye su Manubiya su ke zuba idon ganin su Baba, amma shiru. Ganin har k’arfe 10 ta yi, ga jikin Manubiya itama sai ƙara tsanani yakeyi, hakan ya sanya suka yanke shawarar Jidda ta je ta dubo su Baba tun da sun san asibitin da aka kai Innar.

Da kyar suka haɗa naira hamsin kuɗin mota, ta bata tace ta hau bus, idan ba ta gaban asibitin murtalan za su bi ba sai su ajjiye ta a hanya ta ƙarasa.

A hankali ba don tana so ba ta miƙe ta shiga toilet ta yi brush ta wanke fuskarta, ta ɗan kimtsa tukunna ta fito ta yi musu sallama ta fita.

Unguwar shiru ba kowa, ƴan kasuwa sun tafi harkokin gaban su masu zuwa aiki sun wuce haka ma ƴan makaranta…
A takaice dai kowa ya tafi neman abunda zai fishshe sa.

…..Tun lokacin da ta fito shi ya hango ta, amma yadda ta taho ya sanya ya fahimci ita bata lura da shi ba.
Ƙare mata kallo kawai yake yi yana maimaitawa, yana mai sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya…
Shi fa tunda yake bai taɓa ganin farar mace tass!!! Kuma farin mai asalin kyau kamar na Jidda ba!
Dan duk wanda ya ganta ba zai taɓa tunanin Mahaifinta talaka ne ba.
Fatarta har wani shek’i take yi!
Ga idanuwa dara-dara manya sosai, oval shape, tubarkallah.
hancinta pointed nose ne, ba dogo chan bane kalar wanda za a ce masa ‘har baka’, pointed ne mai asalin kyau da ɗaukar hankali.
Bakinta shima mai kyau, laɓɓan masu ɗan cika! ba chan ba, sannan na ƙasan tsakiyar sa a ɗan rabe kamar an tsaga.
Sai dimples ɗinta a wajen hab’arta (k’asan lips d’inta gefe guda).

Ga shape da Allah ya yi mata, dan Jidda asalin figure 8 ce.

Yadda Jidda take, haka sak Manubiya take. Suna tsananin kama da juna,
Sai dai Jidda ta fi Manubiya hasken fata Manubiya kuma ta ɗan fi Jidda tsayi da jiki, kuma Idanuwan ta basu kai na Jidda girma ba, amman sun fi na Jidda kyau da kyalli da d’aukar hankali. Sannan ta fi Jidda tsayin gashi, dan nata har gadon baya yake , sab’anin na Jidda wanda bai ida kaiwa har gadon bayanta ba.
Yanayin dimples ɗinsu shima ya banbanta jidda guda ɗaya ne a k’asan hab’arta na Manubiya kuma a kumatunta suke (both side) Masu kyau da ɗaukar hankali.
A halayya ma sun bambanta dan
Manubiya tanada ɗan faɗa, Jidda kuwa in za’a saka mata hannu a baki, ba lalle ta ciza ba ……
..
Jikinta ne ya bata kamar ana kallon ta, dan haka ta ɗan ɗago da kanta, ai kuwa da shi ta fara tozali.
Suna haɗa idanu ta yi saurin mayar da kanta k’asa, ta k’ara sauri domin ta samu ta wuce sa…
amma sai ya yi saurin ƙarasawa inda take yana wani kalar murmushin da yake sanyawa take k’ara tsanar sa.
…
‘’Ina wuni’’
tace da shi. Daga nan ta fara ƙoƙarin zagaye shi zata wuce.

Hannu kawai ta ga ya saka zai kamo ta,
dan haka ta yi saurin kaucewa.
Da kyar ya iya ruƙo bakin hijabinta fuskarsa har zuwa wannan lokacin d’auke da murmushi…

Sai da ya dawo da ita gabansa ta hanyar janyo ta tukunna yace
‘’Matas, wai har yanzu ba za ki sakawa zuciyarki da rayuwarki salama ba ko?
Kin fa riga kin san ni ne mijinki har gaban abada!
To kuma mai ya sa ba za ki tursasawa zuciyarki ƙauna ta ba?’’
Yayi mata tambayar yana mai matsowa kusa da ita.

Da sauri ta ja baya,
Idanuwanta har sun kawo ruwa.
Muryarta na rawa tace
“Ya Yusuf ka sakar mini hijabina,
Ina sauri ne’’.

Kwaikwayar ƴar siririyar muryar tata mai cike da rauni yayi ta hanyar cewa
‘’A’a, ni ba zan saki hijabin matata ba’’.

Duk yadda ta so hana kanta kuka kasawa ta yi, dan haka kawai ta saki kukan da take ta k’ok’arin riƙewa….
da sauri ya cika mata hijabin
kafin ya ce
‘’to to sorry!!!…
Wasa fa nake yi miki, mai ya faru har haka?
Are u okay?’’.”

bata san lokacin da tq ce
‘’Inna ce fa bata da lafiya,
tun jiya su Baba suka tafi kaita asibiti har yanzu basu dawo ba.
Shine zan je wajensu, kai kuma ka tare mini hanya.’’

Cikin rashin jin daɗi ya ce
‘’yi hak’uri ai ban sani ba ne shiyasa.
Jira ni anan, bara in je in d’auko mashin ɗina sai mu je, ko?’’.

Kafin ma ta basa amsa har ya wuce da ɗan sauri, da alama yanayi nata da maganar rashin lafiyar Innar ya kid’ima sa.

Kamar wata Yarinya! Tana ganin shigewarsa gida ta ɗiba a guje, ta shige wani lunga ta ɓuya!.
Ta san babu kyau ka ce ka tsani Mutum amma wallahi ta tsani Ya Yusuf!!.

Tabbas! dama sai da ya shiga cikin gida tukunna yayi wannan tunanin,
aikuwa ilai sai gashi ya fita da gudu. Sai dai kuma gudun nashi bai amfaneshi da komsi ba dan babu
inda bai duba ba amma ya rasata…..
Saboda da Jiddan taga ya fara neman ta, sai ta yi wuff ta shige
gidan da yake a cikin lungun!
Allah yaso sun tab’a yin Islamiyya ɗayq da ƴar gidan dan haka ta gaida Maman Yarinyar (Matargidan) tace “dan Allah za ta yi fitsari”
matar ta ce mata “tou”
daga nan ta afka toilet.
Ta jima tukunna ta fito tayiwa matar sallama da godiya,
dan ita kaɗai ce a gidan
Yaran duk sun tafi makaranta.

Tana fitowa ta ɗan tsaya opposite gidan jikin katangar wani dank’areran gida wanda katangar ta shanye gaba ɗaya lungun, ta ɓangaren dama…
A tsorace shiga kalle-kalle kamar marar gaskiya, sai da ta tabbatar bata ga Ya Yusuf ba tukunna ta fara shirin nufar titi….

Ko taku biyu bata yi ba suka yi ido biyu da Ya Musbah.
Dan haka bata samu ta je asibitin ba sakamokom ce mata da ya yi “ ta taho su koma gida a je a yi wa Innar girki.
an kwantar da ita, wai aiki za ayi mata, kuma daga yau ba za su sake bari ta ci komai ba har sai bayan an yi aikin da kwana uku.”
…
Sai da suka shiga gidan tukunna Ya Musbah ya san ashe Manubiya itama bata da lafiya dan Jidda bata samu damar gaya masa ba, tunda ta ji wai ‘aiki za’a yi wa Innar’ gaba d’aya sai ta d’imauce ta rikice.
Ba ƙaramin tashi hankalin Ya musbah ya kuma yi ba,
sai da ya ga Manubiyan ta tashi ta zauna tanata maimaita masa cewa
‘jikin nata fa da sauki‘
tukunna ya ɗan ji relief(sauƙi).
Daganan ya shiga sanar musu
“Kidney ɗin Innar guda ɗaya ya samu matsala!
sannan ciwon zuciyarta shima ya motsa! Ga hawan jini!.
Kuma basu san garin yaya ba
amma jiya cikin dare ta samu stroke!
Maybe ko mak’udan kud’ad’en da ta ji Likita ya lisaafo ne suka d’aga mata hankali,
Allah kad’ai ya sani.
But yanzu dai an ce ana buƙatar a cire kidney ɗin da ya samu matsalar da wuri gudun kar mai kyaun itama ta kamu.”

Kuka suka saka gaba ɗaya su ukun, tun kafin ma ya dasa aya, ya so ya daure ya rarrashe su amma sai ya gagara!
shima kawai ya b’ige da hawaye.

Da kyar Manubiya ta tsaida kukan nata ita ta shiga rarrashinsu,
tukunna sukayi shiru.
Sun ɗan jima a ɗakin shiruuu kafin Manubiya ta ce
‘’Ya Musbah, yanzu ya za’ayi mu haɗa kan uban kuɗaɗen nan na aikin, da na gado da na magani?
Sannan
za su kai kimanin naira nawa??”

A hankali ya ce
‘’Baba ya saida filinsa dama tun a jiya, da namu. Sannan Al’ameen ya cika mana wasu kud’ad’en,’’.

Shiru ya yi kamar mai tunani
kafin ya kalli Muhsin ya ce
‘’Zo, mu je mu siyo abun kari mu yo cefane’’.

Suna fita
Manubiya ta juya ta zubawa Jidda kyawawan idanuwanta
ba tare da ta ce ko ta yi niyyar cewa komai ba.

Sarai Jidda ta gane tuhumar ta Manubiyan take yi
Don haka ta ce
‘’Ban san maganar ba,
bama mu had’u da shi ba, rabo na da shi tun wanchan satin.’’

Ajiyar zuciya kawai Manubiya ta sauƙe
kafin ta ce
‘’Jidda kina fita ɗazu ba ki daɗe ba
na tsinci naira hamsin a cikin littafina na makaranta dan haka na aika Muhsin na ce yayi gudu ya je titi ya ƙara miki kud’in mota tunda na san ba lalle kin kai ga zuwa titin ba ma.
Amma sai ya dawo ya ce mini bai ganki ba!.
Kuma Ya Musbah yanzu cewa ya yi a jikin gidan su ya ganki, wanda shi kan sa na san kawai maganar ce baya so shiyasa yayi miki shiru.’’

A hankali Jidda ta ce
‘’Wallahi rabo na da Ya Al’ameen tun wanchan satin, ki yarda dani,
dan Allah.’’
Ta ƙarashe maganar kamar zata fashe da kuka.

A take kuma sai tsananin tausayin ta ya rufe Manubiya, ko babu komai
ta san ba ƙaramin Namijin ƙoƙari Jidda take yi wajen ganin ta rabu da Al’ameen ɗin ba. …….
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*07*

Sai bayan sallar isha
tukunna, Mommy ta tattara gaba d’aya ragowar kwarin guiwarta, ta nufi side ɗin Kausar.

A parlournta ta same ta, kwance cikin luntsumemiyar resting chair ɗin dake yashe a balcony na parlourn wanda glass ne kawai ya raba balcony ɗin da parlourn.

A hankali Mommy ta ƙarasa kusa da ita, ta zauna a dai-dai wajen k’afafunta, tana tunanin ta ina zata fara rarrashin nata.
Chapter 12 · 0% Book details