← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 84

Sashe 77

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanayin yadda ta yi ‘k’asa da kai ta yi shiru’ ne ya sanya yayi tunanin ‘maybe ranta ya d’an
b’aci’ne, ga kuma yadda ya tamke fuska ko maraba bai yi mata ba wanda shi kanshi sai yanzun ya lura da hakan, shiyasa tashi d’aya shima duk sai ya ji ba dad’i dan haka ya sauk’e wata y’ar siririyar ajiyar zuciya kafin ahankali ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna yace’’Sorry!(yi haƙuri)”
kawai.

Duk shiruu sukayi kafin ya sake cewa
‘’Ya jikin Baba??’’

Ba tare da ta d’ago fuskarta ba sannan a hankali ta ce “Alhamdulillah’’

Murmushi ya yi kafin ya ce
‘’Fushi kikayi?’’

Girgiza kai ta yi da farko sai kuma bata san ya akayi ba amman kawai sai ta tsinci kanta da ce masa
‘’’(yi haƙuri)!’’
itama.

Murmushi mai sauti ya yi kafin yad’an had’e rai tukunna ya ce
‘’Kar ki damu next time idan kika sake saka wannan abun, ni kad’ai na san me zan yi miki’’
Ya k’arashe maganar yana dariya ahankali ahankali.

Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba itama kafin a hankali ta fara magana
“Sofia ta zo, tun a yau kawai har ta k’ara mana haske akan yadda za mu dinga yi wa Inna, na ji tace kullum itama za ta dinga zuwa ko?’’

‘’Um’’
kawai yace
Idanunsa akanta.

A hankali ta ci gaba da cewa “ban samu na yi maka godiya yadda ya kamata ba,
da tare za mu taho da su Ya Musbah tou kuma dole sai da shi tukunna za’a kai Inna asibiti, shiyasa ya ce in baka hak’uri in ce suma suna nan zuwa kuma mun gode sosai
Baba!Jidda!da Muhsin suma duk sun ce ayi maka godiya…
Allah ya saka maka da alkhairi’’.

Murmushi ya yi kafin ya ce ’’Allah ya k’arawa su Inna lafiya, bana buk’atar godiya daga gareki ko Ahalinki..
Dan Allah ki cewa su Musbah suma ba sai sun zo ba…’’

A hankali ta ce ’’a ganina ya zama dole mu yi maka godiya’’

Jin ya yi shiru yanata kallonta ne kawai ya sanya ta ce ’’once again mun gode, Allah ya biyaka.”

Kamar wadda ba zata yi magana ba sai kuma ta ce ’’zan tafi’’
ta fad’i hakan tana mai sunkuyar da kanta k’asa sosai.
So takeyi kawai ta tafi tunda ta gama abunda ya kawota, maganar aikin da ya ce akwai yau dama ta san kawai jan magana ne.

A hankali ya sauk’e nannauyar ajiyar zuciya sai kuma ya sunkuyar da kanshi yana murmushi
kafin ya d’ago ya ce ’’nima, a ganina ya zame min dole in bawa abunda nake tsananin k’auna kariya.’’

‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Haka Manubiya wadda ta runtse idanuwanta tashi d’aya ta shiga nanatawa a cikin zuciyarta, tana mai jin wani kalar fad’uwar gaban da bata tab’a ji ba tunda take a rayuwarta.
A take gaba d’aya ilahirin Jikinta yayi wani irin sanyi, kamar babu jini ko
rai a k’afafuwanta haka ta ji..
dan tabbas inda ace za a tsikara mata allura a wajen tou da ba lalle ta ji ba!…
A haƙiƙanin gaskiya ba ma ta jin dukkannin ilahirin Jikinta saboda tsabar yadda ta ɗauke lokaci guda koina ya yi mata sanyi.
Dakyar ta samu ta fara dawowa dai-dai ta d’an fara jin jinin jikinta yana kai mata a jikin nata, sai kuma ta d’an fara kyarma
ahankali ahankali.

Ganin yadda ta runtse idanunta ta k’ame a waje d’aya ne
ya sanya Yashjub ya furzar da wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya tashi ya koma inda take ya zauna a kujerar da ke a gefenta.
Kamar jiya yau ma yadda ya ga ta zabura sai da ta kusan bashi dariya…Kamar zata fashe da kuka haka ta juyo ba tare da ta yarda sun had’a ido ba ta ce ’’Dan Allah ka daina, banaso.’’

‘’Bakya so in ce miki Ina sonki?
K’arya kike so in yi miki?
Ko so kikeyi in ci gaba da azabtar da zuciyata ta hanyar hanata muradin ta??’’
Ya ce da ita yana kallonta.

Mik’ewa Manubiya ta yi da wani kalar sauri, ta juya za ta fita amma kafin ma ta yi taku d’aya kawai sai ta ji ya damk’o Hannunta!.

Da sauri ta juyo sai dai kafin ma ta ce wani abun tuni ta ji hawaye sun b’alle mata.

A hankali Yashjub ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna a hankali ya mik’e tsayen shima still yana rik’e da Hannun nata wanda
ya ke jinsa kamar kar ya cika kamar ya rik’e har abada kar ya barta ta je ko ina, ga wani musulmin taushi da d’umi da Hannun nata ya ke ƙunshe da! Wanda atake suka taru suka d’imauta sa.

Da kyar ya iya cewa “ki yi
hak’uri Mannubiya in abunda na gaya miki ya b’ata miki rai ne ki yi hak’uri,
Dan Allah.
Ba na son ganin hawayenki, ba ki san yadda nake ji a cikin raina ba, pls ki daina kukan nan….burina in sanya ki farin ciki in kula dake a ko da yaushe,
ba zan so in zamto silar zubar hawayenki ba, kar ki sa in kasa yafewa kaina pls.
A ganina ba laifi bane idan na gaya miki sirrin zuciyata shiyasa tun jiya nace miki alfarma da kuma tukuici, saboda na san dama ba lalle kema kina jin abunda nake ji ba, amma in har kikayi min wannan alfarmar kika bani wannan damar kika amince da ni kika bani damar kasancewa tare da ke har abada
Mannubiya
kin gama min komai.
Tun ba yau ba a matse nake, inaso in faiyyace miki sirrin raina, inaso kuma in ji naki,
Inaso in ji abunda yake cikin zuciyarki kema gameda ni, amman tabbas a yanzu ina jin tsoro sani saboda hawayen nan naki da na gani ba alama ne mai kyau ba!..
Dan haka in har kin san amsar da za ki bani ‘No’ zata kasance, to na rok’e ki da girman Allah kar ma ki ce min komai, ki je ki sake tunani kawai
dan tabbas na san zan iya rasa raina idan kika ce mini
A’A …..’’.

Bata ce dashi komai ba, bata ma da niyyar cewa komai, kukanta kawai take yi tana d’an k’ok’arin kwace Hannunta daga cikin nasa.

A hankali ya lumshe idanunsa yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya bud’e ya d’an sunkuyar da kanshi k’asa..ba abunda ya tsana a ynzu irin kukan nan da takeyi, sam ko da wasa baya son ganin hawayenta…Shiyasa ya bud’e idanunsa ya d’an runtse hannunta da ke a cikin nashi sannan a hankali ya sake matsowa kusa da ita, ya d’aga d’ayan Hannunsa wanda ba ya riƙe da komai, ya kai dai-dai setin fuskarta.

Tabbas ta fahimci so yake ya goge mata hawaye, dan haka cikin kuka wanda yake d’auke da b’acin rai ta ce “iyakar Hannuna da ka rik’e bai ishe ka ba??’’

‘’Oh no
(Wayyo)”
Yashjub ya fad’i hakan a fili, dan shi wallahi sai yanzu ya fahimta ya kuma fara ganewa…
Shi fa Indai yana gabanta to mantawa yake yi da kowa da kuma komai.
Har ga Allah bai san lokacin da ya damk’i Hannun nata ba da farkon da kuma ya rik’e d’in sam sai ya gagara saki.

“Damn it!”
Ya fad’a a chan kasan ranshi yana jin takaicin kanshi,
dan tabbas ya san ya kwasa.

Da ikon Allah kuma gashi har zuwa wannan lokacin ya gagara sakar mata Hannun nata yana nan riƙe da shi gam.

Da k’arfi Yassira ta daki glass d’in k’ofar wanda hakan yake nuni da alamun knocking…

A tare gaba d’ayan su suka d’aga Kai suna kallon k’ofar shigowar.

Sun yi mamakin ganin Kausar da Yassira a tsaye a cikin office d’in, dan basu san lokacin da suka k’araso ba ballantana su san lokacin da har suka shigo.

Da sauri Manubiya ta juya, ta goge hawayenta, daganana bata sake yarda ta juyo ba.

Cika mata Hannu Yashjub ya yi, sannan ya janye d’ayan Hannunshi wanda ya d’aga da niyyar goge mata hawaye, tukunna ya d’an matsa kusa da su ya kalli Yassira, fuskarshi ba yabo ba fallasa
Yace
‘‘Lafiya dai ko?’’

Da kyar Yassira ta samu ta iya cewa ‘’eh!lafiya, mun zo wajenka ne, sai dai na ga kamar kana busy….”

‘’Eh kam, very busy”
Ya bata amsar kanshi tsaye, kafin ya ce
‘’Ki jira in mun had’u a gida sai mu yi’’
Ya k’arashe maganar tasa cikin takaici, dan sam bai so su ka ga Manubiya yanzu ba.
Daga haka ya fara k’ok’arin juyawa ya ji ta ce
‘’Akan Mommy ne fa. Ba zai yiu mu yi a cikin gidan ba dama shiyasa muka biyo ka nan’’

Wannan karon had’e fuska Yashjub yayi tamau kafin yace “Yassira, i’m busy, ki jrani ko ma menene, idan na dawo gida sai in ji ko?!.Thankyou’’

Shiruu Yasirar ta yi kafin
daga baya ta d’an k’ak’alo murmushi, a hankali ta ce
‘‘Okay Yash’’

Jinjina Kai yayi, still fuskarshi a had’e ya ce
‘’sai anjima’’
har ga Allah
Allah Allah kawai yakeyi su yi su fita, saboda gaba d’ayanta Kausar! Da ita da shigarta! Da kwalliyarta!
Duk juya mishi kai kawai takeyi.

Sai da Yassira ta sake kallon Manubiya wadda ta juya baya tun shigowarsu tukunna ta kamo Hannun Kausar wadda itama tunda suka shigo ta yi ido biyu da Manubiya ta sunkuyar da kanta k’asa ta k’i cewa komai.
Ahankali Yasira ta ce mata
‘’mu je!’’
Ganin da ta yi kamar ma Kausar d’in bata jin abunda take ce mata ne ya sanya kawai ta ja
Hannunta suka fice daga office d’in .

Suna fita Yash ya zagaya ya d’auki wayarshi ya turawa Yassira massage
…’idan kika sake zuwarmin da ita office ɗina,
I’m going to humiliate the two of you like hell….
(Sai na haɗa da ke da itan na yi muku wulaƙancin da ba za ku taɓa mantawa ba)…..’

*MANNUBIYA*
*46*

Yana gama turawa Yassira message ya ga
Manubiya ta sak’ala jakarta, tana shirin juyawa ta tafi.
Dan haka ya k’arasa da sauri ya tare gabanta.

Kasa magana ta yi shiyasa kawai sai ta kawar da kanta gefe.
Chapter 77 · 0% Book details