Sashe 45
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hanyar stairs ta tsaya ta goge hawayenta tukunna ta k’arasa sauk’a ta nufi kitchen.
A kitchen d’in ta tarar da Yasira Kausar Yasmeen da Ya’isha,
da alamun kowa fita zata yi kuma masu aikin ba su gama jerawa a kan dining d’in ba shine suka zo suke d’iba anan d’in…
a cikin su ba wanda ya ce mata ci kan ki haka ta wuce ta ajjiye kwanukan ta shiga wanke Hannunta…
Cikin rashin mutunci ta ji Ya’isha na cewa
‘’Dad’ina da talaka bai iya samun guri ba, a yi employing d’inka amma ka nemi zak’ewa, na rantse da Allah Asabe duk ranar da kuka sake yin letti ba ku jera mana abinci har kuka ja muka makara ba to
ko wacce shegiya sai ta koma inda ta fito, sai ku dinga yin abu kamar ku kuka haifi Mutum…..
Mtswwwww’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai jan wani uban tsaki,
daganan ta sa Kai ta fice.
Wata dariya Yasmeen ta yi,
Irin wadda ta yi wa Ummi jiya ciki-ciki.
Dariya sosai Kausar ita kuma ta yi kafin tace
‘’Kin ga Malama, ki saki Baki ki yi dariyarki dan babu uban wanda ya Isa ya hanaki.’’
Ahankali amma yadda ta tabbatar Ummin za ta ji Yasira ta ce
‘’Tana jin tsoron a shiga tsakanin ta da Daddy ne’’
Cikin dariya k’asa-k’asa ta rainin hankali
Kausar tace ‘’au,haka ne fa’’
Daganan duk suka d’auka abincin da suka zuzzuba suka fita suka nufi dining table banda Yasmeen wadda ta tsaya haɗa tea a cikin kitchen d’in.
Har Ummi ta fita sai kuma ta tuna akwai flask d’in da ferfesun ciki bai gama zubewa ba dan haka ta juya da niyyar komawa ta cewa gwaggwo su juye mai kyau ne…
a k’ofar kitchen d’in suka yi kiciɓus da Yasmeen wadda ta yi kamar irin ta tare k’ofar nan ne..ita ba ta matsawa Ummin ta wuce ba sannan ita bata fito ba..
da mamaki Ummi take kallon yarinyar tana so ta ga iya gudun ruwanta.
A hankali Yasmeen wadda ta hango Daddy yana sauk’owa daga bene tace “na ga kin shigo da kwanuka a hargitse
kuma idonki kamar kin yi kuka, gaya min gaskiya dukan ki Daddy ya yi?’’..
Dama tun ɗazu da kyar Ummi take danne kanta dan bata so ta kula Yaran amman duk maganganun da suka yi a kitchen d’in ta san da ita suke ga kuma takaici da tashin hankalin da Daddy ya tsoma ta a ciki tun jiya shiyasa duk yadda ta so hana kanta ta kasa dan haka ta d’aga Hannu ta zabgawa Yasmeen wani irin gigitaccen mari,
dai-dai nan kuma Daddy ya k’arasa saukk’owa cikin parlourn.
Wani irin kuka Yasmeen ta saka ta durk’ushe a wajen ta dafe kunnnenta tana ihun ‘’Wayyo Allah kunnena’’
Dai-dai nan Daddy ya k’araso wajen a gigice, da k’arfi ya ce
‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
sakamokon ganin jini yana zubowa ta kunnen Yasmeen.
Sai a lokacin Ummi ta ji ashe wai ‘Yasmeen tana da abu a cikin kunnenta wanda ya ke zuk’o mata magana sakamokon rashin aiki da kunnuwan nata basa yi sosai.’
kuma ba kunya ba tsoron Allah a take Kausar har da rantsuwa ta yi tsalle ta dire wai “ai sun gayawa Ummin jiya da ta yi yunƙurin marin Yasmeen d’in amma shine yau sai da ta mare ta, shikenan yanzu in ba da kyar ba ta danna mata abun chan ciki ta lalata mata kunne gaba d’aya.”
Cikin tsananin gigita Ummi ta ce
‘’Kausar ki ji tsoron Allah, yaushe….
Wata rikitacciyar tsawa da Daddy ya buga mata ce ta sanya ta kasa ci gaba da magana…cikin tsananin fushi ya ce ’’ki b’ace min a wajen nan tun kafin na illataki .’’
A hankali sannan k’afafuwanta suna wani irin karkarwa ta samu da kyar ta juya ta kama hanyar sama zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Yayinda su kuma suka d’unguma kai Yasmeen asibiti, gaba d’ayan su.
••••••
Sai yau Manubiya ta d’auki wayarta a jikin charji daga gidan Ammi,
dan sai da ta bar wayar ta yi awannin da aka rubuta ana buk’atar ta yi a jikin charjin. Layinta na jiya da suka yi wa register ta saka, bayan kamar 30 minutes ta d’auki wayar ta dudduba daganan ta d’auko katin Yashjub cikin nutsuwa ta juye numbersa tukunna ta tura masa sak’o kamar
haka
’’Good morning Sir(ina kwana sir), yau na kunna wayar tawa daga charji, my mail is empty as for today(yau, mail ɗin nawa ba komai a ciki)..idan sun turo I’ll report everything to you on Friday (zan haɗa in sanar maka komai ranar juma’a)..
InshaaAllah
Thankyou(na gode)...
Manubiya Musa..’’
Fitowar Yashjub daga wanka kenan dan lokacin 7 dai-dai,itama Ammi ce ta ce mata ta tabbata ta je da wuri fiye da yadda take zuwa kullum, wai tana da bak’in da za su zo daga Abuja so akwai aiki sosai..
Yana fitowa ya ga wayarsa ta yi k’ara dan haka ya k’arasa ya d’auka ya shiga duba message d’in, dama ya saka a ransa maybe ita d’in ce dan tun jiya yake ta jiran ya ga kira ko messge d’inta.
Murmushi kawai ya yi, ya sake karanta sak’on ya kuma maimaitawa ya sake maimaitawa kafin ya ajjiye wayar da kyar yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya…
yanzu mene ne abun yi, saboda duk taurin kansa da kauce-kaucen sa ya riga ya sak’k’o, ya fahimci yana mahaukacin son Manubiya..duk yadda ya yi ta denying yana kaucewa, a iya jiya kad’ai ya tabbatar k’aunarta yake yi, k’auna ba ta wasa ba, amma kuma ta ya zai fad’a mata abunda ko Najeeb yana tunanin anya zai iya fad’awa kuwa….
numfashi ya fesar ya nemi guri ya zauna a ransa yace ‘’Yashjub a yadda kake son Manubiya, b’oye b’oye ba naka bane ba,’’
domin
shi kansa ya san yana da buk’atar wani abun ya faru soon…a fahimci juna a yi aure tun kafin sonta ya zautar da shi sannan ga wannan cousin d’in nata da ya ga take-taken kamar shima sonta yake yi, kasancewar sa na gida ne ya sanya Yashjub yake ganin gara ya d’auke Manubiya tun wuri tun kafin iyayenta su yi abunda zai kai sa lahira ta hanyar aura mata Abbakar.
A part from all these (bayaga duk waennan abubuwan ma) a yanda yake jin Manubiya a zuciyarsa da ransa to tabbas
ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa daga nan zuwa watanni hud’u ko uku gaba ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba…..
Da wannan tunanin ya shirya ya fice office, ko Daddy bai tsaya jira ba dan yana buk’atar ya yi tunani sosai sannan ya san ta inda zai fara Kafin Daddyn ya zo su fara aiki,kuma yana da buk’atar lek’awa d’ayan company d’in nasa duk a yau.
……
Manubiya tana ajjiye wayar ta juya kenan su ka yi ido biyu da Maamaa,
da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace’’Maamaa Ina kwana.’’
sai kuma ta fara k’ok’arin fita daga kitchen d’in.
Murmushi Mama ta yi sannan ta ce’’ni kam Manubiya tsoro na kikeyi ne?
naga kwata kwata kin k’i ki yarda ki saki jiki da ni ga shi kuma k’addara ta had’a mu zama guri d’aya,ya kenan?’’
Ta k’arashe maganar tata da tambaya tana murmushi.
Murmushi Manubiya ta yi
kafin a ranta ta ce
‘’Tabbas k’addara ta had’a ni zama guri d’aya bama da ke kad’ai ba har da wanda nake
gudun ki domin shi.’’
A fili kuma sai tace
‘’Ba komai Maama ba gudun ki nake yi ba kawai dai abubuwan ne suka d’an yi min yawa,shiyasa.’’
Cikin rashin jin dad’i Maama tace’’Ayya!na ji Ammi tana cewa mamanki ma ba lafiya ko?’’
Ahankali Manubiya ta d’aga kanta alamun’’eh’’
Cikin tsananin jin tausayin ta
maama ta ce
‘’Allah ya bata lafiya Allah ya sauwwak’e, ku yi ta addu’a za ta warke inshaaAllah, kin ji ko?’’
Ahankali ta jinjina mata kai tukunna tace ‘’nagode Maama’’
ta fad’a hakan tana mai Jin tsananin k’aunar matar na shiga ranta.
Murmushi Mama ta yi, ta matso ta d’an shafa fuskar Manubiya
tukunna ta ce
‘’Allah ya yi miki albarka”
daga nan ta wuce ta fita daga kitchen d’in..
so gamon jini!!
ita dai haka kurum Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar,
tana jinta ne har cikin ranta…….
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*28*
Har wajajen 11 shiru babu Daddy ba Yasira a company.
Baƙin da suka yi
ma Yashjub ne ya yi handling d’insu shi kad’ai, gashi yana ta kiran number Daddy amma baya d’auka ita kuma Yasira nambobinta duk ba sa shiga.
Dan haka Baƙin suna tafiya
shima ya kamo hanyar gida.
Sai k’arfe 10 tukunna likitocin da su ka karb’i Yasmeen suka fito,
cikin son fahimtar dasu
Babban Likitan ya kalle su ya ce
“It’s nothing serious(ba wani babban abu bane ba), dan bai tab’a komai ba kawai dai d’an kurjewa ta yi shiyasa kuka ga jini.
abun nata dama ina so in bata sabo shine kawai muka tsaya aka d’an yi dressing wajen na bata sabo na bata drugs da 1 week off ta huta a gida,
Allah ya kare gaba.’’
Cikin samun relief dukkan su suka ce ‘’Ameen’’ sai a lokacin tukunna Yasira ta d’au waya ta kira Mommy take gaya mata komai.
Office Yasira ta wuce
Yusra da Ya’isha da Yadira kuma school, yayinda Daddy da Kausar suka kama hanya domin maida Yasmeen gida.
Suna shiga Daddy ya cewa Kausar ta kai Yasmeen d’akinta shi kuma ya nufi b’angaren Ummi…..
Bai same ta a d’akin nata ba ashe ya baro ta a k’asa a d’akin Yahanasu wadda zazzab’i ya rufe tun jiya da daddare ba wanda ya sani.
Munirat ya tarar tana share d’akin, cike da girmamawa ta durk’usa har k’asa ta gaida shi, ba yabo ba fallasa ya amsa
kafin ya ce mata “Ina saddik’a?’’
A hanakali tace masa
‘’Tana d’akin Adda Yahanasu wadda batada lafiya’’
A ranta tana mamakin Allah dai yasa lafiya dan bata tab’a ganin shi a dai dai wannan lokacin a gida ba,
kuma a side d’in Ummi.