Sashe 38
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D’an murmushi ta yi a hankali daganan ta ce
‘’Bye, sai mun had’u anjiman’’
Tana gama fad’in haka ta mik’e za ta fita, da sauri ya ce
‘’Yauwa’’
sai kuma ya mik’e ya k’arasa drawer da ya ajjiye wayoyi da atms d’in Kausar ya d’auko envelope d’in da ya saka komai nata a ciki ya kaiwa Mommyn ya ce ‘’ga shi”.
Dukda hakan bai ga chanji a mood d’in nata ba(yanayin nata ba), dan kawai karb’a ta yi ba tare da ta kalle sa ba ta juya ta fita.
Ya dad’e yana nazarin Mommy
daga k’arshe ya yanke wa mood d’in nata (yanayin nata) hukuncin ‘wataƙila ta d’an ji zafin yadda ya ƙi tsayawa ta yi masa massage saboda wata friend wadda ya sani jiya-jiya already ta riga da ta kwantar masa da hankali.’
Daga haka ya janyo wayarsa ya turawa Manubiya message
kafin ya danna kiran Najeeb…
Yana d’auka kuwa ya kwashe da dariya.
Shiruuuuu Yashjub ya yi yana sauraron shi sai da ya yi mai isar sa tukunna ya ce “ya aka yi ne?’’
ya yi masa tambayar still yana dariya k’asa-k’asa.
‘’Iyakar plan d’in naka da idear taka kenan? wanne aiki to zan bata?’’
Yashjub yayi masa tambayar kai a d’aure.
Cikin dariya Najeeb ya ce
‘’Iyaka taimakon da zan iya yi maka kenan wallahi, tunda kaga ka zo mini da sharud’a, my hands are tied ta ko ina (ka ɗaure ni ta koina) shiyasa na barka ka yi figuring out komai da kanka, cikin sauk’i.’’
Ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin ya ce
‘’To ai ni aikin da zan bayar a dinga zuwa duk sati sau d’aya ne ban san shi ba’’
Yadda Najeeb ya yi wa Abbakar tak’aitaccen bayani akan aikin haka ya yi wa Yashjub, daganan ya d’aura da cewa “chatting nake yi da k’anwarka ka kira ni, kar ka ja min in je garin gyara maka ni kuma madam ta yi fushi, sai anjima.”
Yashjub yana shirin yin magana ya ji Najeeb ya katse kiran…
shiruu ya yi yana tunani kafin kuma ya fara wani kalar murmushin da ya dad’e bai yi ba….
….
Su Manubiya har sun cire rai suna shirin maidawa Siyama wayarta kawai suka ji message ya shigo..
Da farko kamar ba za su duba ba dan basu sani ba ko na siyaman ne sai kuma suka ga kamar number da suka kira ce dan haka suka duba.
Suna bud’ewa suka ga an turo Time da Adress d’in inda zata same shi, jibi Monday da safe inshaaAllah…
A take suka turawa Ya Musbah message d’in ta wayar Siyaman, duk da sun san gobe za su had’u, amma duk cikin su Baba ne kawai mai waya dan haka gara su ajjiye message d’in a wayarsa, in ya so goben sai su shirya komai, jibi su tafi tun da ya ce 8 na safe za ta je.
Suna gama tura masa Jidda ta maidawa Siyama wayarta ta dawo ta zauna ita da Muhsin suka shiga surutu da murnar aikin da Manubiya ta samu,
tun Manubiyan bata kula su har ta d’an fara saka musu Baki a hirar tasu wadda duk suna yi ne a kan albashin Manubiyan: za su siya kayan abinci da na farko, idan an sake biyan ta kuma sai su siyawa inna da Baba kayan sakawa, sannan suka ce za su biyawa Muhsin ya yi jarabawa ya wuce ss1 ya ci gaba da karatunsa shima….
Kusan duk a lissafin nasu ba su sako kan su ba kawai komai su iyayen su sai Muhsin wanda yake ta murnar ya ji an ce zai ci gaba da karatu..
wannan dalilin ne ya sanya hawaye suka b’allewa inna wadda ta farka daga bacci ba da dad’ewa ba..
da kyar ta samu ta rarrashi kanta ta yi shiru.
A haka Baba ya shigo ya same su hannunsa rik’e da bak’ar leda.
sai da suka yi masa sannu da zuwa tukunna Manubiya ta mik’e ta d’auko faranti ta na zuwa ya mik’a mata ledar ta karb’a ta yi godiya tukunna ta bud’e….
Kunun tsamiya ne a ciki d’an sachet guda d’aya sai gurasa guda hud’u mai gishira an d’an yayyafa mata mai.
Jidda ce ta karb’a kunun tsamiyar ta je ta ta damo wa inna ta dawo Manubiya da Muhsin kuma suka d’auki
gurasar d’aya d’aya su ka ci bayan sun yi sun yi da Baba akan shima ya ci amma ya ƙi, ya ce musu “ya ci tasa a waje kafin ya shigo”
ba dan sun yarda ba sai dan basu son yin ja in ja da shi ne yasanya suka hak’ura suka d’auki tashi guda d’ayar suka sake raba ta gida uku suka barwa Jidda wadda take bawa inna kunu nata su kuma suka ci nasu suka sha ruwa, daganan Manubiya ta d’auki bargon Baba da Muhsin ta yi musu shimfid’a ta ajjiye musu abun rufuwa…
dai dai nan ita kuma Jidda ta gama bawa Inna kunu, dan haka ta zauna zaman cin tata gurasar Manubiya kuma ta je ta d’an d’umamo ruwa ta dawo ta kaiwa Baba rabi toilet rabin kuma ta zo ta shiga gogewa Inna jiki.
Cikin sanyin jiki Baba ya mik’e ya je ya gasa k’afar sa wadda ta addabe sa kwana biyun nan, daganan ya yi uzuri, brush da alwalla ya fito ya zo ya yi addua ya kwanta yana tunanin mai gobe kuma zata k’unsa….
babbar damuwar sa itace ‘abinci’ dan wannan ma a bashi aka basa da kyar, dan haka ya san ba lalle wanda ya
basa bashin ya kuma basa gobe ba…..
Yana jin su (Yaran) suka shiga one by one kowa ya yi brush ya yi alwallah ya fito daga nan Manubiya ta kunna musu mosquito coils Jidda ta yi musu shimfida suka nema waje suka kwanta..
Har bacci ya kwashe su gaba d’aya amma shi ya gagara kawai dai ya lumshe idanuwansa ne kamar mai bacci ….
•••••••
Ummi bata cewa Munirat komai ba har suka k’arasa d’akin Ummin.
Sai da suka shiga ta rufe k’ofar d’akin nata tukunna ta juyo Munirat tana shirin yin magana Ummin ta kwashe ta da wani kalar gigitaccen mari, cikin fushi ta ce ’’na baki minti biyar ki yi mini cikekken bayani. Munirat kina haukane?
Yahansu fa?
Ba wai ina zargin ki da yi mata snatching (kwace) ba amman kamar yadda Daddy ya fad’a da Mutumin ya fara yi miki zancen banza da sai ki yi fitar ki ki bar shi, a iya d’azun yana ganin ki kawai ya ce miki zai aureki ko kuwa ya abun ya ke?’’
Cikin kuka Munirat ta ce
‘’Ummi alhaji Bashir ne fa kuma tare mun hanya yayi, amma wallahi Ina ganin sa na so in juya amma sai ya tare min hanya…’’
Shiruuu
Ummin ta yi ta kasa cewa komai kafin chan ta cewa Munirat d’in ‘’je ki yi alwallah ki yi sallah ki kwanta,’’
Daga haka ta juya ta fice daga d’akin.
Ko da Ummin ta fita a parlournta ta zauna ta yi tagumi, ta jima sosai a haka kafin daga baya ta mik’e ta nufi side d’in Daddy..
A d’akin Munirat ta ci y’an biscuits da apple ɗin da ta tarar a fridge ta sha ruwa bayan ta yi sallah ta kwanta tun tana tsammanin ganin Ummi har bacci ya kwashe ta tana sheshek’a tana ajiyar zuciya.
…
Kamar yadda Yashjub ya fad’a,sai da ya huta ya tabbatar Daddy ma ya gama duk wasu aiyyuka da uzururrukan sa tukunna ya nufi cikin gidan, bai tarar da kowa ba dan gidan yayi shiruu, dare yayi kowa yana d’akin sa.
yana tafe ya turawa Mommy massage daganan ya nufi sama side d’in Daddy yana k’arasawa k’ofar parlourn ya d’an yi knocking tukunna ya shiga da sallama.
Yana shiga ya hango sa ya rafka tagumi ya zurfafa a tunani, sai da ya je kusa da shi sosai ya zauna a kan 1 seater d’in da take facing 3 seater da yake zaune akai ya ce
‘’Daddy’’
Tukunna ya yi firgigit ya d’ago yana kallon sa
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*24*
Numfashi Daddy ya fesar kafin ya gyara zama ya bawa Yashjub dukkannin attention d’insa tukunna ya ce’’kana da buk’atar wani abu ne?’’
Ganin Yashjub d’in ya yi shiru ya gagara cewa komai ne ya sanya Daddy d’in sake cewa’’ina jin ka, akwai matsala ne?’’
A hankali Yashjub ya sunkuyar da kanshi yana tunani, sai da Daddyn ya sake basa dukkannin hankalinsa ya ce’’Talk,mana.’’
tukunna Yash d’in ya sauk’e ajiyar zuciya cikin nutsuwa da sanin kan zance ya fara magana
‘’Daddy..
Allah ya huci zuciyarka akan abun da zan fad’a maka yanzu,
Idan ya yi maka zafi ka yafe min”
sai da ya d’an yi shiru tukunna ya ce
‘’Daddy abun da aka yi wa Ummi a gidan nan yau bai kamata ba, sannan su Yasira a gaban ka suka dinga yi mata rashin kunya amma aka kasa tsawatar musu, bayan ba ma laifin Yarinyar nata bane ba, tunda ba ita ta ce tana son Mutumin ba…
kar so da tausayin Yahanasu ya rufe mana ido mu d’auki alhakin Ummi da y’arta bayan kai ne ka yi alk’awarin za ka zame mata uba.
Sannan magana ta biyu su Ya’isha ya kamata a taka musu burki tun yanzu, kar su saka Yarinyar nan a gaba, and also tun daga kan Yasir har izuwa kan Yadira gaskiya Daddy ya kamata a yi wani abun saboda kwata-kwata basu san ya kamata ba, ko ni da na tashi a Uk ba zan yi abubuwan da suke yi ba, na san muna iyakar k’ok’arin mu wajen basu tarbiyya amma abun nasu kullum k’ara gaba yake yi!..
Kalli abun da suka yi wa Munirat da Ummi yau sannan
Yassir yau da na je gidan da ya ke abunda na gani ba zan ma iya sake maimaitawa ba saboda k’azantar ta yi yawa….
da shi da Abokansa guest house guda suka ware suke zaune da y’an Mata abun babu kyan gani, ya kamata a tsawatar musu tun wuri Daddy,
B4 it’s too late
(Kafin lokaci ya ƙure).”