← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 84

Sashe 22

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta katse ya sake kira nan ma ta kusan katsewa tukunna ya d’auka da sallama…
A hankali Yashjub ya amsa,
tun kafin ya yi k’orafi Najeeb ya ce
‘’Sorry, ina wanka ne, yanzun nan fitowa ta na ga wayar tana haske’’
Ya k’arashe maganar yana mai shirin ajjiye wayar dan ya san tunda Yashjub d’in ya ji haka zai ce ‘ok,
Idan ya shirya ya kira sa kawai.’
Har ya maida wayar kan side drawer sai kuma ya ga still ba’a kashe ba, shiruuu ya d’an yi kafin ya sunkuya ya d’auki wayar ya mayar ya kara a kunnensa, a ransa
yana tunanin ‘shin me yake damun Yashjub haka, ko dai family matter ne? tunda dama ya ga Daddy ya kira shi d’azun, kuma tunda ya fita ko sallama bai dawo yayi masa ba kiran sa kawai yayi ya ce masa ya wuce!.
It’s very unlike him….’.

Yana cikin wannan lissafin a hankali ya ji Yashjub d’in ya ce
‘’Am..Najeeb, Yaran d’azu ya sunansu?
I mean, ya sunanta?’’

Shiruuuu Najeeb d’in ya yi ya zaro wayar daga kunnensa ya kalli sunan da kyau ya tabbatar Yashjub d’in ne tukunna ya mayar ya d’an tab’e Baki ya d’aga gira yana murmushi kad’an -kad’an yana jinjina Kai alamun ‘yes’ tukunna ya ce
‘’Okay!!…’’
sai kuma ya kwashe da dariya.

Da sauri Yashjub wanda dama
tunda ya yi masa tambayar a take ya fara jin inama he can take it back(inama bai yi ba), ya ce
‘’ka ji matsalar ka, ko?
Ba abun da kake tunani bane ba tou, she just looks like someone (ta yi min kama da wata) shiyasa nake so in yi confirming (in tabbatar)
Ita d’in ce ko ba ita bace ba, that’s all.”

Cikin son k’ok’arin danne dariyar tasa dan ya lura mutumin nasa har ya dan k’ule, Sir Najeeb ɗin ya ce
‘’Maybe ita ce, a ina ka san wacchar d’in?’’

Cikin rashin gaskiya Yash ya ce ‘’A uk, neighbor d’in mu ce, amma gidan nasu gaba d’aya sun dawo Nigeria, har ita.
Last year’’

‘’Girlfriend??’’
Najeeb ya sake jeho masa tambayar yana mamakin yadda Yash d’in ya k’irk’iro k’arya haka tashi guda ya zabga masa.

Cikin d’an d’aga murya
Yashjub ya ce
“I said neighbor!!(maƙociya fa na ce maka)
Ko ife-ifen d’alibai ya kurmantar da kai ne ban sani ba?.
Maƙociya ce kawai.
ka fad’a min sunan ta kawai mu wuce gurin’’
Ya k’arashe maganar tasa a k’age, dan ji yake yi kamar ya shiga ta waya ya zak’ulo sunan nata daga cikin bakin Najeeb d’in.

A hankali Najeeb ya ce
‘’Gaskiya ba ita bace ba!..
Yarinyar da ka gani ɗazu I don’t think ta san ko hanyar airport ma.
ko last time da kyar ta yi registration fa, har aka fara exams tana cike crf, da farko ma k’in yi mata signing mukayi
sai da hod ya ce ‘mu yi mata tana da d’an issue’
tukunna’’

Zuwa wannan lokacin Yashjub ya fara ji kamar ya shiga ta waya ya shak’o Najeeb!
Dukda tashi d’aya ya ji damuwa daga jin labarin nata
amman kuma jan ran da Najeeb yake ta yi masa ya gama k’ular da shi dan haka ya kira sunansa da dakakkiyar murya, ya ce
‘’Najeeb!’’

‘’Na’am,Yash.’’
Najeeb d’in ya amsa

Ya sunan Yarinyar da na gani ɗazu a office d’inka?’’

Sarai dama Najeeb ya gano shi, ya fahimci inda ya nufa..
Kwana-kwanar da ya tsaya yi masa ce ta sanya shima ya so ya ja masa rai amma jin yanayisa ya sanya kawai ya hak’ura!
Ya san zai dawo gareshi, soon.
Dan haka kawai sai ya ce masa
‘’Manubiya Musa’’

Ajiyar zuciyar da Yash ya sauk’e saida Najeeb d’in ya ji,
dan haka kawai ya yi murmushi a ransa
Ya na adduar ‘Allah ya sa su daidaita’
dan ya san idan
Yashjub ya samu ya auri wadda yake so to zai fita daga wannan k’uncin da ya d’aurawa kansa k’arfi da yaji ta dalilin miskilanci…
Yo miskilanci mana, saboda in ba
hakan ba
Mutum successful kamar Yashjub ace wai ba shi da aiki sai yamutse fuska da fushi da rashin hira da dariya da walwala, kullum…………

Yashjub yana gama jin sunan Manubiya ya yi sallama da Najeeb. ko komawa bai yi ya kwanta ba
Ya hau instagram ya shiga searching ‘Manubiya Musa’
dan ya san idan ya samu ya ga pictures ɗinta complete maybe zai samu ya ɗ’an rage damuwa
ya samu ta daina yi masa yawo a ido da kunne….
Sai dai kuma sam bai samu ba!
Shine twitter!!
Shine Facebook!!!
Ko ina sai da ya duba amman sam bai samu ba
Dan ko da ace bai santa ba idanuwan waenda ya ke gani masu irin sunan ta sam ba irin nata bane ba…
Dan haka tashi d’aya yake fahimtar ba ita d’in bace ba.

Tunani yayi ‘ko dai ya sake kiran Najeeb ya tambaye sa ko tana da wani nick name’ sai kuma ya ga in ya yi hakan Najeeb ɗin zai ga zak’ewar sa,
kuma ya san yana tambayar sa ma shikenan
zai fara judging d’in sa, dan haka sai kawai ya hak’ura ya koma ya shiga searching ‘Manubiya eyes’
A tunaninsa maybe friends d’inta da hakan suke kiran ta!
Tunda shakka babu Idanuwanta are one in a million.
Ya jima yana Abu d’aya kafin chaaan kuma ya yi shiruuuuu!
Ya fara tunani da auna wawtar sa.

Shiruu yayi shi kaɗai!
Yana mamakin yadda ya haukace tashi d’aya, dan shakka babu wannan d’an k’aramin haukane yake yi…
A hankali ya ajjiye wayar ya dafe goshin sa, sai da ya d’an nutsu tukunna ya ja ya kwanta ya shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere.

Yana kwanciya tashi d’aya
tunaninta ya dawo masa…
Me yake damun ta?!
Me ya ke saka ta saurin kuka?!
Me yake saurin breaking d’inta!!!
Ya akayi bata samun kud’in registration da wuri??!….
Runtse idanunsa ya yi da k’arfi
cikin b’acin rai ya yi tsaki!!!
kafin a fili ya ce
‘’Yau ni kam na had’u da aljana’’.

‘’Wacece aljanar??’’
Muryar Mommy wadda ta shigo yanzu ta daki dodon kunnuwansa.

Sarai, ya ji ta.
Sai dai bai bud’e idanunsa ba ma
ballantana ta yi tunanin samun amsa daga gare shi.

Wani maɗaukakin tashin hankali ta danne da kyar, kafin ta k’araso ta tsaya a kansa tukunna ta sake cewa
‘‘Wacece aljanah??’’

Sai da ya d’an d’auki lokaci
tukunna ya bud’e Idanuwansa ya kalle ta sannan ya ce
‘’Daddy ya ce gobe zai zo, da daddare. Yana buk’atar ganin kowa.
Sannan kin gayawa Yasir da Bakinki yadda kukayi da shi?”.

Cikin inda inda ta ce
‘’Shi Daddyn me ya ce maka mun yi da shi??
Me yace maka na ce?’’.
Ta yi maganar ta na mai zama a Bakin gadon wajen ƙafafunsa.

Sai da ya d’an yi murmushi kafin ya ce
‘’Nothing.
Ya ce dai kawai ki san yadda za ki yi da Yasir kafin ya zo, dan idan ya zo a goben baya son jin wata magana game da komai kuma,
akwai important abun da zai kawo shi!
So kar a zo ku bashi kunya’’.
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce ‘’sai anjima’’
daga haka ya nufi k’ofa.

Da sauri ta mik’e ta ce
‘’Yash.
Wacece aljanah?’’

Juyowa kawai ya yi ya kalleta,
kamar zai ce wani abun!
Sai kuma kawai ya sauk’e wata nannuyar ajiyar Zuciya
daga nan ya sa Kai ya fice ya barta nan a tsaye……

Gaba d’aya Kan Mommy d’aurewa ya yi, ta rasa mafita game da lamarin Daddy da kuma Yashjub, da su da maganganun su duk sun taru
sun d’aure mata Kai kwarai.
…….
Kamar yanda Daddy ya fad’a, washegari da daddare
bayan sallar isha’a,ya zo.
Tare suka shigo da Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya had’u da su suna parking dan haka ya jira suka shigo tare.

Suma gama zama ya haura sama domin yana son magana da Mommy kafin ta sauk’o saboda kar ta ga bambarakwai.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*13*

Waya ya same ta tana yi, da alama da Uncle d’intane
(yayan Abban ta….)
Yanayin maganan nata ya sa ya yi tunanin maybe ko k’ara ta kai.

A hankali ya nemi guri ya zauna yana mai lumshe idanuwansa a ransa ya ce
‘’In ban da abun Mommy, ta bar Abb’oi ya huta mana, Mutum ko gani bayayi sosai shekaru sun ja amman tana d’aga masa hankali, tabbas shiyasa bata shiri da ya’yan da jikokinsa
dan sun lura kashe musu shi take k’ok’arin yi da tension d’in matsalolin ta……”

‘’Yash!’’
Muryarta ta katse masa tunani.
A hankali ya bud’e idanuwansa
kafin ya mik’e ya k’arasa bakin gadon ya zauna ya ruk’o Hannayenta.

Tunda ta ga yayi mata haka
ta fahimci abu mai matuk’ar mahimmanci zai fad’a mata,
dan haka ta tarkata ilahirin hankalinta zuwa gare sa,
kirjinta yana mai dukan uku-uku.

Gaba d’aya tashi d’aya sai tausayin ta ya lullub’e sa, dan haka ya sake runtse Hannuwanta a nasa tukunna ya fara magana
‘’Mommy dan Allah ki yi hak’uri,
duk abun da zan fad’a miki yanzu inaso ki danne Zuciyarki, ki yi
hak’uri, ki fahimce ni’’.

Zuwa wannan lokacin gaba ɗaya hankalin Mommy ya gama tashi, da kyar ta samu ta iya ce masa
‘’in shaa Allah, Yash’’.

A hankali ya ce ‘’Su Daddy sun zo, suna k’asa shi da bak’uwa,
mun samu k’arin member a family d’in nan, jiya…….
Inaso ki fahimci ba wai saboda kun samu matsala ne shiyasa ya yi miki kishiya ba, dama chan akwai plan d’in b’oyewa yayi.
Nima ban sani ba sai last week
But I think an d’an matso da d’aurin auren kusa saboda a yadda na sani kamata yayi ace yanzu saura two weeks.
Mommy dan Allah ki yi hak’uri
na san dole za ki ji babu dad’i, ni kaina ina jiye miki, kinga dai bani da ko budurwa
amman ko tunani na yi
‘For instance (misali)ace
Inada budurwa, ta je tana kula wani’ to bansan ya zanyi ba!!!
Ballantana kuma ku da ku ke ma’aurata.
Ki yi hak’uri, na san babu dad’i
amman a yadda Daddy yake a yanzu
Idan kika b’ata masa rai tabbas ban san kuma mai zai yi ba!.
Ki yi hak’uri Mommy na san kina hak’uri da Daddy amma dan Allah ki ƙara ki sake hak’uri!!!
For us ….’’
Chapter 22 · 0% Book details