Sashe 76
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiruu kawai Baba ya yi, yana wani lissafin na daban. Kafin ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, tukunna ya mik’e da kyar dan ciwo Ƙafar takeyi masa..inda aka ciccire masa faratun duk sun kumbura sun sake taso masa sannan sun assasa ciwon k’afar nasa wanda dama yake ta fama da shi, dauriya ce kawai yakeyi tun kwanakin baya amma yanzu abun yana cin ƙarfinsa dan azaba yake sha sosai!! Hatta faratun hannunsa waenda aka cire suma duk ciwo su ke yi masa.
Ahankali ya d’ingisa ya nufi toilet domin ya watsa ruwa, dan tun d’azu Manubiya ta kai masa ruwan wanka.
Yana shiga Jidda ta shigo musu da breakfast, dan haka suka zauna su uku suna ci har da mai sunan Baba wanda Ya Musbah yaketa tsokanar sa yana ce masa acici dan sai da suka ci wainar gero tukunna suka fito.
Inna ma tun ɗazu an bata nata abun karin, an shirya ta.
Ganin sun kusan kammalawa ne ya sanya Ya Musbah mik’ewa ya fita domin ya dubo ko Nafi’u ya zo, in kuma bai ƙaraso ba sai ya kira sa.
Sai da Muhsin ya mik’e ya fita tukunna Jidda ta kalli Manu ta ce “na d’auka Muhsin zai yi fushi ko kuka da aka ce an fasa kaishi makaranta, ashe ya girma yayi hankali yanzu’’
Murmushi Manu ta yi kafin ta ce
‘’Ya ban tausayi, Allah ubangiji ya bamu ikon sanya shi a makarantar’’
‘’Ameen’’ jidda ta ce, daganan ta zare hannunta a abincin ta d’an matsa kusa da Manubiya sosai sannan ta ce ’’yanzu ya za’ayi? Za ki siya masa ne a hanya tukunna ku wuce office d’in nasa?
Dan gaskiya bai kamata ku had’u ba tare da kin bashi ɗan gift ba’’
‘’Babu gift d’in da zan bashi’’
Manu ta fad’a hakan ba tare da ta kalleta ba.
Da sauri Jiddah ta d’an zabura sai kuma ta ce ’’amma wasa kikeyi ko?’’
Sai a sannan Manu ta d’ago kyawawan idanuwanta ta kalleta tukunna ta ce
‘’Da gaske nakeyi, ya riga ya fara rok’on tukuici da kanshi, kinga kuwa ai ya yi wa kansa’’
Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ‘’kamar yaya?’’
……yadda su ka yi da shi jiya akan batun tukuici Manu ta kwashe tsaf ta gayawa jidda…
Kafin ta d’aura da cewa ’’tun d’azu nake ta faman fargaba,
ban san me zai ce yana so ba, na riga na yarda da shi akan
ba zai cutar da ni ba,
amma dukda kawai ni I’m so nervous( ina cike da fargaba)”
Ta k’arashe maganar tata tana mai mayar da idanunta kan jellof d’in taliyar da ke a gaban su.
Shiruuu Jidda ta yi, ta zuba mata idanu, har sai da Manubiyan ta gaji dan kanta ta d’ago ta kalleta
Tukunna Jidda ta yi murmushi kanta tsaye
ta ce ’’kema kina son shi ko??’’
Wata mahaukaciyar zabura Manu ta yi a lokaci guda ta yi amfani da d’ayan Hannunta na hagu ta toshema Jidda Baki, ta fara rarraba ido a cikin d’akin.
Dai-dai nan Baba ya fito daga toilet d’in sanye da kayan da ya chanja a ciki wanda ya cire kuma riƙe a hannunshi tare da brush da vaseline d’in shi.
Kallonsu ya yi kafin ya ce ’’d’azu Kaka Mallan ya kira akan yana buk’atar ganin mu ni da su Uncle da gaggawa. idan Likitar ta zo
ku yi komai in kunga ban dawo ba sai ku wuce kawai ba sai kun jira ni ba’’
Daga haka ya ajjiye kayan wankin a wajen da suke tarawa ya ajjiye brush da Vaseline d’in suma a wajensu sannan ya wuce yana mai cewa “idan na dawo na ci nawa abincin’’..
Yana fita Jidda ta ce ’’Adda Manu yanzu y….’’
Cikin katseta Manubiya ta ce ’’Jidda dan Allah kar ki yi min haka, kar ki ƙarasa rikitani’’
Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ‘’ki tsaya tou mana ki ji abunda zan fad’a ma’’
Kamar Manubiya za ta fashe da kuka ta ce ’’Plss Jidda….’’
Daganan ta mik’e ta fad’a toilet ta wanke Hannu tare da kuskure Bakinta sannan ta d’auro alwallah ta fito.
Fitowarta ke da wuya, wayarta ta d’auki k’ara…
Tana dubawa ta ga Yash ne me kiran.
Batayi mamaki ba, dan itama tunanin sa take yi dan haka ta d’auka a hankali ta kara a kunnenta….
…bayan kashe mata jiki da doguwar gaisuwa, ya ce
mata ’’Dr Sofia fa tana waje, ta zo tun ɗazu’’
Da “to” ta amsa masa, tukunna suka yi sllama daga haka ta nufi k’ofa da niyyar fita ta je ta shigo da ita amman sai suka yi karo da ya Musbah da ya Nafi’u dan haka ta gaya musu ita kuma ta koma ciki.
Su ne suka je suka shigo da baturiyar likitar mai suna Sofia
matar mai kirki sosai da bagwariyar Hausar ta…
Sama da awa d’aya ta d’auka tana examining (gwadawa da bincika ) innar kafin ta ce ’’su wuce asibitin ta’’
A inda ta gaya musu asibitin nata yake ya baud’e sosai da office d’in Yashjub!
Gashi sun riga sun ce masa za su zo, kuma shi kansa Ya Nafi’u ya kamata ace yana wajen interview ɗinsa ma yanzu haka…shiyasa suka yanke akan
‘Ya Nafi’u ya tafi interview d’inshi,
Manubiya ta je ta yi wa Yashjub godiya a madadin dukkansu sannan ta gaya masa dalilin da ya sanya ba su zo su duka ba.
Ya Musbah shi kuma ya tafi asibiti tare da Inna.
*MANNUBIYA*
*45*

Babu kalar lallamin da Manubiya ba ta yi wa Jidda akan ‘ta zo su je tare’ ba, amma k’iri-k’iri Jidda ta ce mata ‘’A’a!, idan na bi ki wa zai kula da su mai sunan baba da Muhsin?’’
Da sauri Manubiya ta ce
‘’To duk ku zo mu tafi tare’’
Cikin tarar numfashinta Jidda ta ce ‘’kuma in Baba ya dawo sai ya ga ba kowa?’’
Haka suka yi ta fama, dan duk ta inda ta b’ullo sai Jidda ta toshe.
Ya Musbah ma bayan Jidda ya bi ya ce ’’ko baya ga hakama ta ya an cewa Yashjub d’in za su zo su uku yanzu kuma kawai yaga Yara.
Kawai ta je d’in in yaso ta ce masa inshaaAllah shima shi da Ya Nafi’u suna nan zuwa’’.
Hakanan Manubiya ta fita ko sallama bata yi wa Jidda ba,
Jiddan tanata tsokanarta
k’asa-k’asa
da
‘‘Oga wife’’
Ita dai Manubiya bata kulata ba, ta barta kawai akan sai ta dawo sai su yi ta.
Har ta Isa company d’in kuwa tana fargaba! bata san
tukuicin da zai ce yana so ba
sannan ga matsayar da Jidda ta riga ta gama cimmawa,
da kuma abunda ita kanta zuciyarta take raya mata
shiyasa gaba d’ayanta ta bi ta sake diriricewa.
Yau tana zuwa receptionist d’in ya ce mata ‘’an ce in ta zo kawai ta wuce office d’in ceo, ba sai an rakata ba’’
‘’Okay’’ kawai ta ce,
daga nan ta nufi office d’in nashi dake a chan sama kai tsaye.
A bakin glass door d’in
ta tsaya ta d’an yi knocking glass d’inc tukunna ta tura ta shiga da sallama.
A zaune ta sameshi ya k’urawa k’ofar ido…fuskarsa tamau kamar bai tab’a dariya ba, dan har sai da ya d’an bata tsoro amman kawai sai ta dake ta k’arasa ta nemi waje ta zauna, a hankali ta ce ’’ina kwana’’.
Tunda yake a rayuwar sa bai tab’a ganinta da mayafi ba sai yau, mayafin ma kuma mai shara shara….sanye take da doguwar riga d’inkin Ashape, atamfar army green da d’an kwalliyar milk da black, rigar bata wani kamata ba
amma yanayin jikinta da kuma mayafin da ta rufa (black clour)wanda bata saba sakawa ba ne
ya taimaka wajen fito da surar Jikin nata, mayafin nata babba ne sai dai ya d’an yi shara-shara.Ta yi normal d’aurin d’ankwalinta ta gaba ta baya kuma ta nannad’e sa akan ribbon d’inta wanda ta tufke uban tulin gashinta da shi, sannan ta d’aura mayafin nata akai.
Kwalli, powder sai man leb’e ne kawai a fuskarta
amman ba k’aramin kyau ta yi ba,
dan har wani fisfisga Yash ya ji numfashinsa yanayi….
‘‘Yanzu duk inda ta bi ta wuce tun daga gidansu har nan haka Maza suka ganta kuma suma haka suka dinga ji kenan?
bata tab’a saka mayafi ba sai yanzu da ya ke jin masifaffen kishin ta’’
Yashjub ya aiyyana hakan a cikin ransa.
A b’angaren Manubiya kuwa ita kanta tun d’azu a takure take dan ba wani sabawa ta yi da mayafin ba, ta yi kuskure ta bar hijabanta duk sun yi datti, kuma bata samu sun yi wanki da wuri wannan satin ita da Jidda ba, sannan ga abunda ya zo ya faru gaba d’aya ya d’auke musu hankali shiyasa basu nutsu ba ma ballantana ayi maganar yin wanki.
A hankali ta d’an kalleshi ta ga still ita yake kallo, dan haka ta sake yin k’asa da kanta ta ce ’’ina kwana’’
Kamar wani mai jin bacci haka ya lumshe lumsassun idanuwansa ya had’iye wani k’ululun abunda ya tokare masa mak’oshinsa yake shirin hanasa numfashi
tukunna ya ce
‘’Me ya faru da hijaban ki yau?’’
Yayi mata tambayar yana mai matsar da computer dake a gabanshi gefe wanda hakan
ya bashi damar sakata a gaba ya tsura mata ido sosai.
Gaba d’aya diriricewa Manubiya ta yi, sam ta kasa magana
dan haka kawai sai ta sake yin k’asa da kanta…
Zuwa yanzu ta fahimci wataƙila mayafin da ta rufo ne ya b’ata masa rai shiyasa duk sai ta ji ba dad’i, dan sam bataso ta zamto silar b’acin ransa ta ko wacce siga. Ga kuma tunanin ta na ‘maybe kishina yakeyi’
gaba d’aya sai ya sake kashe mata jiki.