← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 84

Sashe 10

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uncle, Baba Habu da Anty Umma Mahaifiyar su ɗaya
Yayinda shi kuma Baba ya kasance ɗan gidan Amarya.
Mahaifiyarsu Uncle ce ta fara rasuwa kafin tashi Mahaifiyar wadda ta rasu wajen haihuwarsa.
Tun suna Yara sun taso basu da wani haɗin kai.

Tun lokacin da Iyayen nasu Mata suka rasu Mahaifinsu bai ƙara aure ba shima har ya bar duniya.
Hakanan suka tashi a wannan gida wanda suka gada kowa yayi
aurenshi yake yin rayuwarshi daga shi sai iyalinsa.
Duk cikinsu shine (Baba) mai ɗan ƙaramin waje
sakamokon siyar musu nashi portion ɗin da ya dinga yi saboda ya samu ya sake jan wani jarin sannan kuma aci abinci a gidansa.
Ko da ya haifi Musbahu, Yaron ya kai minzalin hankali Baba
ya so ya ɗaura shi akan layin sana’a shima, har rantar kuɗi ya dunga yi yana bashi jari
amma shima sam sanar tashi bata yi Albarka ba!
Ganin sana’ar ba zata yiu ba ya sanya suka haƙura!.
Da ragowar ƴan kuɗaɗen Hannunsu waenda basu wani kai sun kawo ba Baba suka haɗa suka fara makanikanci dan a lokacin
shekarun Musbahu sun kai sha bakwai babu damar komawa makaranta.

A wannan lokacin ne kuma
Allah ya ɗaurawa Baba Musa tsananin son yaga Ƴaƴansa sun yi karatun…
Haka ya sanya ya tsaya tsayin daka akan karatun nasu, dan bai yi ƙasa a guiwa ba wajen sanya su a makaranta.
A lokacin Manubiya har dariya ake yi mata dan ta yi girma a ajin Yara! Saboda tare ya haɗa ya sanyasu su uku aji ɗaya
Manubiya Muhsin da Jidda
Duk a aji ɗaya.
Hatta jidda a lokacin ta yi girma a ajin, amma sam Yaran(su Manubiyan) basu wani damu ba
Saboda suma suna tsananin son karatun!
Sannan suna da tsananin ƙoƙari da naci akan karatun, hakan ya sanya cikin ikon Allah hazaƙar su ta sanya aka dinga yi musu double promotion wanda har ta kaisu ga taddo sa’o’insu.

Da farko private suka fara
amman yanayin rayuwa ya sanya dole Baba ya maida su ta gwamnati
wanda duk gidan su kaɗai ne
su ke yin karatu a makarantar gwamnati.

Jamb ne ya so bawa Manubiya matsala
amman waec ɗinta da neco har mamaki ya dunga bawa mutane
saboda yanda ta fito da flying colours. Rashin cin jamb ɗin da bata yi bane ya sanya ta shiga poly ta yi diploma tukunna ta wuce BUK da D E , yanzu haka tana level 3 suna karantar English ita da Abbakar wanda suke karatun tare da shi tun
a poly shine kaɗai Abokinta har gobe kuma shi ɗin ne,
bata da ƙawa mace….
Saboda yanayin rayuwarta da ta zauna ta duba sai ta ke ganin kamar ƙawance ba nata bane ba
kullum Kayanta a koɗe!
Gashi ko kuɗin handout wani lokacin sai dai ta ara ta yi karatun a iya makarantar
Sannan idan an zo tafiya cafeteria (wajen cin abinci) sai dai ta gudu
Dan indai an je sai dai a siya mata ba dai ita ta siya da kanta ba!
Shiyasa da ta fahimci rayuwa ba zata yiwu a haka ba sai ta shafawa kanta lafiya.
Abubakar ne kawai Abokinta,
anan unguwar tasu yake bayan layin su…
Mahaifiyarshi ƙawar Maman Baraka ce!
Tare suka buɗe gidan abincinsu
tun shekarun baya da daɗewa…

Jidda kuma wannan shekarar ta zana waec, ta ci itama kuma cikin Ikon Allah ita taci har jamb,
yanzu saura mata post utme.

Muhsin kuma yana js2 tun last year, yanayin rayuwa yasa ya kasa ci gaba da karatun.
>>>>
‘’Baba Ina wuni”
Muryar Abbakar ta katsewa Baba tunanin da yake yi.

A hankali sannan a ɗan ɓoye ya sake goge Idanuwansa
tukunna ya juya yana kallonsu shi da Muhsin.
Da kulawa ya amsa shi yana tambayar sa ya Mamansa shi kuma Abbakar ɗin yace masa ‘’tana lafiya’’
kafin cikin yin ƙasa da Kai ya ce ‘’Baba ɗazu a aji ana ta bayani amma sai na lura sam hankalin Manubiya baya a ajin….
daga baya ma sai na fahimci ashe kuka take yi.
Na so in taimake ta dan na san akan rashin lafiyar Inna ne amma sam sai ta ƙi yarda.
Dan Allah Baba ga kuɗi nan na bawa Muhsin a kai Innar asibiti dasu..
Kar kace a’a, nima kamar uwa Inna take a waje na”
Sai da ya ɗan yi shiru tukunna a hankali ya ɗaura da cewa
“Allah ya bata lafiya, ya kawo
mata sauƙi’’
Yana gama faɗin haka ya musu sallama ya juya ya wuce…

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*05*

Sai da Muhsin ya ɗan taɓa Baba tukunna ya yi fir-gi-git ya ce ‘’Na’am.’’
Sai kuma ya fara neman Abbakar ɗin amma sai yaga babu shi babu alamun sa…
A hankali ya cewa Muhsin ‘’ka je gidansu, ka ce masa na gode!
Sam banga wucewar sa ba.”

‘’To’’
Muhsin ya ce, kafin ya miƙa masa kuɗin ya na mai cewa ‘’gashi.’’

Sai da kwallah ta zubowa Baba kafin ya sanya Hannu ya karɓa tukunna ya miƙe ya wuce cikin gidan da sauri….

Muhsin kuma ya wuce gidan su Abbakar.

Kusan karo suka yi shi da Manubiya wadda ta fito da gudu!
Suna haɗa idanu da Baban nata sai ta fashe da kuka ta fara waiwaye, tana nuna masa ɗakin tana juyowa tana kuka wiwi, tama kasa yin magana.

Da sauri ya wuceta ta bisbi a baya, suka ɗunguma zuwa ɗakin.

Abunda yayi tunani ɗin ne kuwa!!
Dan haka ya durkusa ya fara ƙoƙarin kinkimar Inna wadda ta sanƙame Idanuwanta suka ƙaƙ-ƙafe…
dai-dai nan Ya Musbah ya shigo …..
..
Allah ya taimake su Nafi’u ya taho da Motarsa 206, dan haka aka saka Innar a ciki, suka wuce zuwa asibitin su huɗu: Baba, Ya musbah, Nafi’u wanda ke driving da Innar.

Rashin gurin zama da kuma jiran Muhsin ne ya sanya su Manubiya suka haƙura ba don sun so ba, amman har waje bakin ƙofa suka biyo su kowacce tana kuka, sai da suka ga wucewar su tukunna suka fara ƙoƙarin komawa ciki da kyar….

Ba su kai ga komawar ba..a nan bakin ƙofar gidan su Baba Habu shi da Uncle wanda dawowar sa kenan daga parking motarsa a gidan makwafcin su, inda yake ajjiyewa kullum, su ka iskesu.

Gaisuwarsu kawai Uncle ya iya amsawa daga nan ya shige ciki ya barsu tsaye su da
Baba Habu, wanda shima ɗin ya fara ƙoƙarin shigewa ciki kamar ba zai tambaye su ba, sai
kuma ya ce musu ‘’lafiya kuwa?’’
Jidda ce ta iya bashi amsa
dan ita Manubiya haushin sa take ji saboda son zuciyar da ya ɓullo da shi kwana biyun nan…ba sa shiga harkarsu
sannan ba sa taimaka musu
amman ya tashi ya tsaya yana ƙoƙarin ƙulla aure tsakanin Jidda da Ya Yusuf, bai damu da yadda Jiddan bata son Ya yusuf ɗin ba
kawai shi dai farin cikin ɗansa yake dubawa….

A tunanin Jidda zai bi bayan su Baba tunda ta lura tunda aka fara maganarta da Ya Yusuf ya na ɗan kula su
amma sai ta ji ya ce
‘’Allah ya bata lafiya’’
Daga haka shima ya ja ƙafafunsa ya shige ciki.

Yana wucewa dai-dai nan Muhsin yana ƙarasowa wajen
dan haka suka wuce ciki duk su ukun.

Sai chan dare tukunna Ya Nafi’u ya dawo, ya zo ya ce musu “su kwantar da hankalinsuc jikin Innar da dauƙi.”
Wanda a take yanayinsa ya sanya
tashi ɗaya suka fahimci ya faɗa musu hakan ne kawai dan su ɗan kwantar da hankalunsu.

Daman ba su yi girki ba!
Tashin hankali kuma ya sanya suka kasa ma jin yunwar.
jugum!! Haka suka kwana ita da Jidda sam basu runtsa ba!
Muhsin shima barcin ɗan kaɗan ya yi.
safiya tana yi zazzaɓi mai zafi ya rufe Manubiya dan har da yau ɗin kwanan ta na uku kenan batayi bacci ba ……
•••••••••
Tun lokacin da Yassir ya fita daga ɗakin da Ƙausar take ciki
bata sake ganin sa ba.

Hada-hadar komawa ma Abokinsa ya ɗaurama wa komai, shi kuma ya yi wucewar sa.

In banda addua babu abunda Ƙausar ta ke ta yi a ranta akan ‘Allah Ubangiji ya sa Yassir Zuciya yayi.
Sannan ya haƙura da ita kenan har abada’
Haka nan ta kwana tana wannan adduar tare da tunani barkatai a ranta!
washegari itama suka haɗa komai nasu itada ƙawayenta suka nufi airport……
…
Da safe around 8, flight ɗinsu ya yi landing a gida, Nigeria.
Suna fitowa suka tarar da
Sister ɗinta ’Yasira’ ta na jiransu ….
…
Sai da suka fara ajjiye ƙawayen nata waenda suka dawo tare tukunna suka ɗauki hanyar gidansu wanda ke a sultan road, Kano state.
shiruuuu! Haka motar ta ɗauka babu mai cewa komai kafin chan Yasira ta yi murmushi ta ce
‘’tun jiya da ya dawo
dama na fahimci faɗa kukayi,
yanzu kuma mood ɗinki kaɗai ya tabbbatar min da hakan.
Kin gaya masa ne?’’
Ta ƙarashe maganar tata da tambaya tana me ɗan waiwayawa ta kalle ta kafin ta maida hankalinta akan tuƙin da take yi.

Kamar Ƙausar ba zata amsa mata ta ba,
sai kuma ta ce
‘’kina nufin na sanar masa
‘bana son shi, yayan sa nake so???’.”

Wata ƴar siririyar dariya Yasirar ta yi, kafin ta ce
‘’Noo!
Ki dai san ta yadda za ku yi breaking up tun wuri kawai kuma cikin sauƙi, saboda in har kika bari kuka yi baram-baram da shi, to fa ki tabbata auren ki da Ya Yashjub ba mai yiuwa bane ba!.
So, find an easy way out (Ki nemo mafita mai ɓullewa, mafi sauƙi) soon.

Rikitacciyar zuciyarki data ɗauko mana aiki mai zafi, ta nemo mana mafita, a samu a rabu cikin sauki.’’

Wata nannauyar ajiyar zuciya Kausar ta sauƙe kafin ta ce
‘’Abun da nake ta so in yi kenan, amma
shi kuma Yasir nacin bala’i ne da shi, kamar maye haka yake, ya ƙi ya bani haɗin Kai, ban….’’
Ganin yadda Yasirar ta yi
shiruuu ta ɗan ɓata fuska ne
ya sanya Kausar ɗin yin shiru kafin ta ɗan yi gyaran murya, tukunna
a ankali tace
‘’Sorry.’’
Chapter 10 · 0% Book details