Sashe 14
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba Habun shima naira ɗari biyu ya basu ya ce “su siya mata lemon zak’ii su gaishe ta su ce yana mata ya jiki, Allah ya bata lafiya.”
Muhsin ne ya karba sukayi godiya shi da Jidda daganan suka fito suka kama hanyar asibitin….
A ward Ya Musbah ya san ya bar su
amma suna zuwa
Nurse ɗin ta ce masa ai an maida ita aminity 2.
Yana mamaki yana tunani haka nan ya wuce shi da su Manubiya suka nufi aminity inda aka nuna musu.
suna shiga suka tarar da Al’ameen a zaune, In banda ƙamshin Kaji da youghurt ba abunda ɗakin yake yi, hatta ruwan sha ya siyo wajen katan goma da lemuka suna kusan goman duk an jibge sai kace waenda za su buɗe shago ne.
Tunda suka fara shigowa ya kafesu da ido. kasancewar Jiddan ce a ƙarshe ya sanya bai ganta da wuri ba har sai da dukkan su suka ida shigowa tukunna….
A hankali ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya a ɓoye kafin ya sunkuyar da kansa k’asa ya lumshe idanunsa.
Itama Jiddan tunda ta shigo suka haɗa ido gaba daya duk sai ta diririce.
Cike da damuwa da rashin jin daɗi suka matsa kusa dasu Baba, da kulawa suka gaida Mahaifin nasu su duka huɗun,
tare da tambayar sa ya “jikin Inna”wadda suka tarar tana bacci.
A hankali shi da Al’ameen suka ce ‘’Alhamdulillah’’.
daga nan Al’ameen da Ya Musbah suka yi musabaha cikin mutanta juna da girmamawa, Muhsin kuma ya gaida shi, haka itama Jiddan ta shiga gaida shi dakyar ba tare da ta yarda ta kalle sa ba.
Sai da ya kalle ta ya ɗan yi murmushi tukunna ya amsa da kulawa.
Cikin rashin kuzari Ya Musbah wanda ya gama ƙarewa ɗakin kallo ya kalli Al’ameen ɗin yace
‘’Al’ameen, wannan duk aikin ka ne ko? wahalar bata yi yawa ba kuwa?’’
Sai da yayi murmushi tukunna ya miƙe tsaye ya ce
‘’ko d’aya Ya musbah, ka mai daina kiran hakan da wahala dan Allah, fatan mu Allah ya bawa Innarmu lafiya.
ni bari in wuce, zuwa anjima inshaaAllah zan dawo.”
Har Manubiya za ta yi magana
sai kuma suka haɗa ido da Baba wanda tun ɗazu ta ga ya kafeta da ido.
Cikin ɗan sigar zolaya Al’ameen ɗin ya k’arasa kusa da ita ya ce
‘’Adda Manubiya ina wuni’’
yana ɗan murmushi.
Ta so ta amsa sai dai kuma takaicin da ya taso mata ya turnuƙe ta lokaci guda ya sanya bata ma san lokacin da ta wuce shi ta isa kan kujerar da ya tashi akai ta zauna ba.
A hankali ya kalli Jidda wadda take kallon su tun ɗazu
Ya ce
‘’Sai anjima,Allah ya ƙara sauk’i’’.
Sai da ta sunkuyar da kanta ƙasa tukunna tace
‘’Ameen, mun gode’’.
Murmushi kawai ya yi, daganan yayi musu sai anjima, yasa kai ya fita.
Yana fita Manubiya ta ce
‘’Haba Baba, ya zaka yarda Al’ameen yayi mana wannan hidimar haka?! salon mahaifiyarsa ta zo ta d’agawa kowa hankali??’’
Da sauri ya ɗaga mata Hannu
Kafin ya xɓce
‘’Fad’a kike yi min?’’
Cikin yin ƙasa da kai ta ce
‘’ka yi hak’uri’’
A hankali.
Sai da ya duba Inna ya tabbatar da baccin nata yayi nisa tukunna ya kalli Ƴaƴan nashi gaba d’ayan su…
Kafin a hankali ya fara magana
‘’Ku yi hak’uri, na san na gaza muku a matsayi na na Mahaifinku.
A ko da yaushe ina jin takaicin halin da muka tsinci kanmu a cikin sa duk a ta dalilin taurin kaina, dan na san inda ace tun farko da sana’a ta ƙi karbata na haƙura na koma karatu da wuri to da yanzu ina da aiki na. Ina jin tausayin ku a ko da yaushe sai dai yanzu ban san da wanne ido zan iya ci gaba da kallon ku ba.
Tun wanchan watan da ya wuce Mutumin da ya ara mini kud’i lokacin da za a yi mini aikin ƙafa a yanke ya zo da takardar sammaci, bana so ya d’aga maganar kowa ya ji,
domin a lokacin ma Innar ku tana asibiti, shiyasa da ya buk’aci zai fanshi kud’in sa da garejina na yarda na amince akayi komai cikin lumana.’’
Sai da Baba ya runtse idanunsa ya bud’e su tukunna ya d’aura da cewa
‘’Jiya kuma na siyar da fili na wanda ake rini a ciki ake biyana duk shekara, da naku na ƙauye
sannan a halin da ake ciki yanzu, mai gareji ya ce yana buk’atar kangon zai fara gini a ciki wai
d’ansa zai yi aure.
Dama ba wani abun kirki ne a ciki ba
sai ƴan kayan gyaran mota da benchi.
Ba komai yasa nake fad’a muku a yanzu ba sai dan ku san a yanzu bani da komai!
Dama filayen nake shirin siyarwa in fanshi gareji na
na san koda rabin kud’in ne in na ba sa zai iya jira daga baya in cika ma sa ragowar, to kuma sai maganar aikin Innar kun da ya taso jiya gadan gadan ya sanya dole in siyar da filin a fara shirye-shirye tunda lafiya itace a kan gaba.
Ku yi hak’uri ku yafewa mahaifinku na gaza maku,
tun farko ban baku kyakkyawar rayuwa ba yanzu
kuma ban san wacce irin rayuwa za mu yi a gaba ba, babu fili babu gareji’’.
Ya ƙarashe maganar tashi yana me fashewa da kuka.
Da sauri
Ya musbah ya matsa kusa da shi ya durk’usa a gaban sa ya kamo Hannayensa, cikin karyewar zuciya ya fara magana
‘’Baba kar ka ce haka dan Allah, ai ba dole bane sai ka bamu rayuwar daula, abun da yake akan ka shine
ka bamu tarbiyya sannan ka yi iyakar k’ok’arin ka wajen tufatar da mu da kuma ciyar damu
sai kuma muhalli,
wanda baka tab’a gazawa ba.
Bamu da abun da za mu ce maka sai godiya, fatan alkhairi da kuma adduar Allah ya saka muku da gidan aljannah kai da Inna, Allah kuma yasa ku gama da duniya lafiya.
Baba kana cikin iyayen da ko wanne ɗa zai yi alfahari da.
kuma dama yanzu ai lokacin hutun ka ne,
nema yana a kaina yanzu!
Dan haka ka daina ɗaga hankalinka dan Allah’’
A hankali itama Manubiya ta matso ta ce
‘’Baba gaskiya Ya Musbah ya fad’a, na san bamu tashi a had’ad’d’en gida cikin daula ba
Amman Allah ya azurta mu da mahaifi mai tsananin son mu da k’aunar mu, dan Allah ka kwantar da hankalin ka,
dan ni kam ko da ace za a dawo da duniya farko a bani damar in zab’i Mahaifina wallahi Baba kai zan zab’a.’’
Cikin sharar kwallah Jidda tace
‘’Iyaka soyayyar ka da kulawar ka a garemu ta wadatar Baba.
InshaaAllahu za mu taimaki juna daga yanzu, kar ka damu da salwantar da garejinka ya yi
na san Ubangijin da ya halicce mu ba zai hanamu abin da za mu ci ba,
Kuma inshaaAllah ubangiji zai kawo mana mafita cikin sauƙi’’.
..
Garejin na sa ba wani kud’i yake kawo masa ba tunda babu ciniki sakamokon kayan aiki da suka yi musu k’aranci kuma babu kud’in saye,
sai filinshi wanda masu rini suke biyan sa dubu talatin duk shekara,
Da su ya dogara da su yake ciyar da iyalin nasa to gashi yanzu ya rasa su a lokaci guda!!!
Bai san ya zai yi ba bai san ya za su ci abinci ba amma kamar yadda yaran suka faɗa yanzu,
Allah zai san yadda zai yi da su….
Yarda da k’addara da kuma kalaman su masu dad’i da kwantar da hankali ne suka ɗan kwantarwa da mahaifin nasu hankali. …
…..
Jidda ce ta zuba masa abinci suka tilasta masa har sai da suka ga ya d’an ci da dama tukunna suka kyale shi.
…
Hamdala da tasbihi
Baba Musa ya ke ta jerowa a chan ƙasan zuciyarsa,
dan shi kam Ubangiji ya gama azurta shi da Ƴaƴan da ko wanne uba zai yi alfahari da,
hankali, nutsuwa da tsantsar sanin abun da ya dace
duk sun had’a.
Gashi dai ko yanzu k’iri-k’iri sun dage su na ta k’ok’arin ganin sun kwantar masa da hankali
sun kuma nuna masa ba komai
amma ƙarara yake iya
hango tsantsar tashin hankalin da suke ta ƙoƙarin ganin sun danne a idanun gaba d’ayan su, har Muhsin. ……………
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*08*
Kausar tana fitowa daga banɗakin, suka sauƙa k’asa tare, ita da Yasira.
A dining table suka hango gaba d’aya ahalin gidan a zaune.
Inda Daddy ya ke suka nufa domin su gaida shi sannan su yi masa sannu da zuwa. Suna isa suka durkusa cikin girmamawa suka gaida shi a tare, tare da yi masa sannu da zuwa.
Da kulawa ya kalli Yasira ya dafa kanta ya amsa kafin ya kalli Kausar kamar zai amsa sai kuma ya dauk’e kai ya dauk’i ruwa yana shirin sha ya ji ta sake cewa ‘’barka da dawowa Daddy’’
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce
‘’Yauwa’’ daga nan ya fara shan ruwan da ya kai Bakinsa.
Ba iya Kausar ɗin ba hatta Yasira da kyar ta iya mik’ewa daga wajen, suka wuce suka nema waje suma suka zauna.
Babban dining table ne sosai
mai ɗauke da kujeru wajen goma sha biyar!
Daddy ne zaune a
seat ɗin tsakiya ata farko wanda yake facing na ƙarshe inda Mommy ta ke zaune.
Yashjub da Yasir sun saka Daddy a tsakiya a ta gefe da gefen sa(kujerunsu suna kallon juna) a kusa da Mommy kuma
Yasmin da Ya’isha ne.
Yasmin ita ke bin Yasir da Yasira
Shekarunta 25 a duniya,likita ce. Sai Ya’isha mai shekaru 24 a duniya wadda ta fara masters kwanan nan a Dangote Business School.
A kusa da su kuma
Yusra da Yadira ne,
Yusra shekarunta ashirin a duniya ita take bin Ya’isha tana karatu a B u k tana level 3
Sai auta Yadira wadda take itama a buk level one shekarunta sha bakwai a duniya.
Cikin nutsuwa Daddy ya yi serving kan shi, daganan kowa ya shiga zuba abunda ransa yake so.