Sashe 65
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tarar numfashinsa Najeeb d’in ya ce ’’me ka manta? yace ka je right away fa(yanzu yanzunnan) tashi mu wuce, na ji b’acin rai sosai a muryarsa’’
Najeeb d’in ya fad’i hakan yana mai juyawa.
Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya kalli inda Manubiya ta bi ta shige…
wallahi ba daban Daddy ne ya kirasa ba to da bai ga dalilin da zai sanya ya fita a asibitin nan ba tare da sun yi sallama da Manu ba, bayaga hakan shi fa bai ma gaji da ganin ta ba.
A gaggauce suka tsaya suka biya duk wasu bills daga nan suka fice suka nufi motocin su Najeeb yanata sauri yana cewa ‘’ka yi sauri fa Yashjub,kar ka dad’e ransa ya sake b’aci..’’
*MANNUBIYA*
*39*
A zaune su Manu suka tarar da Baba, ana gwada masa sugar dan complete checkup Yash ya biya ya ce a yi musu.
suna had’a ido da shi gaba d’ayansu sai suka sake zama emotional(sai raunin zuciyoyinsu ya tsananta)
Tashi d’aya Jidda da manubiya suka fara hawaye, ya Musbah shima sai da ya yi da gaske tukunna ya iya hana kansa kuka…ji yake kamar ya d’aura hannu aka ya yi ta kurma uban ihu!…
Wai akan naira miliyan d’aya tak!kalli abunda aka yi wa mahaifinsa sannan aka yi shirin tafiya da k’annensa Mata har biyu amma babu abunda ya iya tab’ukawa.
Nurse d’in tana fita suka rufarwa Baba, har suna y’ar rige-rige wajen k’arasawa tare da tambayar sa “ya jikinsa?”
murmushi ya yi dan dukda hali na tashin hankalin da yake a ciki sai da ya ji wani sanyi da fariin ciki suna ratsashi na ganin yanda y’ay’an nasa suka
damu sannan su ke ta d’awainiya da shi, dan haka ya shiga kwantar musu da hankali kafin ya kalli ya Musbah ya ce ‘’Ina Yaran su ke?
Ai bai kamata ku barsu a waje ba ko?
ku je ku shigo da su da wuri, kar su tafi ban yi musu godiya ba.’’
Jinjina kai ya Nafi’u ya yi suka fita da shi da ya Musbah amma ko da suka fita basu tarar da kowa ba wnda hakan yake nuni da cewar su Yash d’in sun tafi kenan, dan haka suka koma ciki!
Suka sanarwa baba…sai da suka ce masa ai
suna da nambobin wayarsu, tukunna ya d’an ji sanyi, sannan ya ce ‘ko da sun Kira su a waya ya zama dole
su je har office d’insa ko gidansa ayi
masa godiya, dan duk Mutumin dayayi musu alkhairi irin wanda Yashjub yayi musu to tabbas ya chanchanci kulawa ta musamman daga garesu suma.
Ta wayar ya Nafi’u aka kira Yash ɗin wanda gaba d’aya kunya ta lullub’esa sannan duk sai ya ji wani iri na daga godiyar da baban yake ta yi masa…
Hakanan dai a kunyance suka yi wayar daganan Yash ya yi masa sallama tare da fatan ‘Allah ya basa lafiya, ya kuma kare gaba’.
Har Najeeb sai da Baba yasa aka kira masa shi shima yayi masa godiya tukunna hankalinsa ya kwanta…dukda kuwa Baba k’arfin hali ne kawai yake yi amman gaba d’aya abun wani iri yake jin sa ace wai
‘ka ci kud’i har za a tafi da y’ay’anka Mata, amma ka gagara tab’uka komai….’
A hankali ya lumshe idanunsa a ransa ya ce ‘’Innalillahi a inna ilaihirrajiun,’’
Daidai nan kiran wayar Aisha ya shigo wayar Manubiya, dan haka ta d’an fita waje domin ta amsa…bataso ta yi wayar a gaban Baba dan bata sani ba ko wani abun ne ya taso daga b’angaren Inna, dan ta san yana ji zai ce zai tafi gida, to kuma shima ga yanayin jikin nasa sai a hankali….
dan haka ta fita tana mai addu’ar Allah yasa lafiya….
Jidda ma tana ganin fitar Manubiyan itama ta mik’e ta mara mata baya.
Baba yana jin fitar su ya bud’e idanunsa ya zubawa inda su ka bi suka fita idanu yana jin tsananin tausayin su yana ratsashi dan tabbas shi kansa ya san ba za su ji dad’in hukuncin da ya gama yankewa a kansu ba.
Ya ji dad’in fitar da suka yi dan haka ya gyara zama ya kalli ya Nafi’u da ya Musbah ya ce’’ inshaaAllahu nan da sati biyu nake so in aurar da Jidda da Manubiya…’’
Kwarewar da Ya Musbah ya yi ya fari tari a wahale ne ya katse Baba…Da kyar!! Dan sai da ya sha ruwa sosai ya d’an zauna tukunna ya d’an ji dama-dama still yana tarin kad’an-kad’an…
Bai iya jira tarin ya tsaya gaba d’aya ba ya ce ‘’Baba aure a cikin sati biyu kuma sab….’’
Cikin tarar numfashinsa Baba ya ce ‘inshaaAllahu Rabbi…
Yanzu Manubiya nake so ku nemawa tsayayye wanda yake a shirye tsaf, nan da sati biyu sai a had’a a yi…
Jidda ita dama Yusuf a shirye ya ke, inshaaAllah Ina fita daga nan zan samu Baba Habu mu…’’
Duk yadda Ya Musbah ya so ya danne fushin sa kasawa ya yi,
Dan bai ma san lokacin da ya katse Baban ba.. cikin tarar numfashinsa a hassale ya ce ’’Baba amma dai ba Yusuf d’an gidan Baba Habu na gidanmu kake maganar za ka aurawa Jidda ba dai ko?!
Ba dai Yusuf d’an iska wanda ya jefa mu a cikin wannan bala’in za ka d’auki Jidda ka aurawa ba ko?!
Dan in dai shi kake nufi to a gaskiya Baba ba zan tab’a barin Jidda ta aure sa ba…’’
Cikin fushi da fad’a Baba ya ce ‘’a kul ɗin ka Musbahu!!!
Wannan iftila’in da ya fad’o min babu ruwan Yusuf a cikinsa! Dan haka kar ka d’aura masa laifin da ba nasa ba.
eh! Na san muna yawon samun sab’ani
da su amma na san ko
Hauka Yusuf ya ke yi ba zai tab’a yi mini abunda zai jefani cikin wannan halin ba,’’
Cikin fushi Ya Musbah ya ce ’’baba habu fa shi y…’’
Cikin tarar numfashinsa a hasale Baba ya ce “Musbahu bana son rashin kan gado fa?
So nawa nake ce maka ko da wasa kar ka yarda ka k’ullaci ƴan uwana da y’ay’ansu akan abubuwan da suke yi?
Idan ka k’ullace su kaima ai ka zama su kenan!!
Ka ga sai ka bada gudummawar tarwatsewar zumuncin namu cikin sauk’i.
In ba rashin kirki ba Musbahu har kai ne wai za ka kalleni kana cewa wani bazaka bari Jidda ta auri Yusuf ba Kaine ka haifa min ita???”
Sai yanzu Ya Nafi’u ya fesar da iska ya k’arasa gaban Baba ya zauna akan kujerar da ke a bakin gadon tukunna ya ce ’’Baba ka yi hak’uri, kar ka yi (wa furucin Musbahu fahimta ata bai bai) misunderstanding d’in sa,
maganar gaskiya Baba Yusuf bai cancanci a bashi Jidda ba duba da yadda….”
Cikin katseshi Baba ya ce ‘’Bari ka ji Nafi’u!
Dama na san za ku yi
Tunanin wai ko ata sanadiyyar Yusuf ne na fad’a wannan halin, wanda sam abun ba haka yake ba!
Yusuf taimakona ya yi amma sai abun (taimakon) ya zo da tangard’a!
Ya yi mini bayani kuma na fahimci komai dan haka bana son jin komai daga Bakin kowa illah ku ce mini ‘to’ kawai.
Yusuf zai auri
Jidda nan da sati biyu, Manubiya kuma ku nema mata Miji, wannan shine kawai abunda nake so ku fahimta sannan ku yi mini biyayya a kai.’’
Shiruu Ya Nafi’u ya yi kamar ba zai ce komai ba sai
kuma ya ce ‘’amma Baba auren gaggawa da….”
Cikin katse shi Baban ya ce
‘’Nafi’u baka ji abunda Mutumin chan black snake ya fad’i mun kafin ya tafi ba?
Idan ba ka ji ba bari in maimaita maka.
Ce min yayi ‘sai ya dawo d’aukar Matansa’!’’.
Shiruu Baba ya yi kafin zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin rik’ewa suka samu nasarar zubo masa, cike da rauni ya ce ‘’Nafi’u tunda na haifi Yaran nan ban jiyar da su dad’i, farin ciki da walwala ba!!
Allah ya rufa asiri amma idan aka ce yau ga black snake ya dawo kamar yadda ya fad’a ɗin ya d’auki Yaran nan ban san ta ya zan fuskanci ni karan kaina ba ballantan asu kansu yaran, Mahaifiyarsu, uwa uba ubangijina, Nafi’u ban san da wannne Bakin zan yi masa bayanin yadda na kula da amanar da ya bani ba’’
Baba ya k’arashe maganar tasa yana mai fashewa da wani irin kuka.
Jiki a sanyaya Ya Nafiu ya shiga ƙoƙarin ganin ya lallaɓa Baba dan a samu ya yi shiru…
shi kansa ya Musbah ya ji ba dad’in kukan da mahaifin nasa yake yi shiyasa gaba d’aya jikinsa yayi sanyi, yayinda zuciyarsa take wani irin tafarfasa!!!
tabbas Hausawa sun yi gaskiya da sukace’’munafuki in ya rigaka shiga d’akin uwarka, to ko ruwa baka isa ka sha ba.’’
Allah kad’ai ya san me da me Yusuf ya gayawa Baba shi kuma ya hau
kai d’aram ya zauna.
Gashi ya san halin Baba da wata iriyar rikitattiyar kafiya, dan haka ya riga ya san ko ta ya zai yi masa bayani ba zai tab’a yarda ba.
Gashi yanzu ya saka shi a gaba yana kuka, shiyasa tashi d’aya gaba d’aya jikin Ya Musbah ya yi sanyi, dan jin kukan Baba yake yi har cikin ransa, ji yake yi kamar ya je ya samu Yusuf ya d’aga shi sama kawai ya goce…
zai bar maganar yanzu, ya samu ya lallab’a Baba amma inshaaAllah ba zai taɓa bari Jidda ta auri Yusuf ba’’.
A hankali ya matsa ya shiga rarrashin sa shima yana mai bashi hak’urin abunda ya yi masa yanzun…