← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 84

Sashe 44

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

and one more thing(sannan abu ɗaya da nake so in sake jaddada miki)….
Idan kina son magana da Yasira ko Kausar to kin san hanyar inda d’akunan su yake, kar ki sake cewa za ki aikeni tunda ni ba y’ar aiken ki bace ba…”
Tana gama fad’in haka ta wuce ta bar wajen fuuu kamar za ta tashi sama….

Tana wucewa Yusra itama ta mik’e ta bi bayanta haka ma Yadira.

A hankali Yasmeen ta mik’e
ta ce ’’Mommy good night, muna da wani surgery d’in gobe da sassafe…

Baabaa Larai a yi min faten doya irin na jiya pls’’
Ta fad’a hakan tana langab’ar da Kai.

Murmushi Baaba Larai ta yi, daga nan ta ce ‘’inshaaAllah y’ar albarka, Allah ya taimaka.
sai da safe.’’

‘’Na gode Baaba Larai d’inmu’’
Yasmeen ta fad’i hakan da murmushi akan fuskarta kafin itama ta wuce abunta ba tare da ta kalli inda Ummi take nan a daskare ba.

A hankali Yahanasu ta lumshe idanuwanta a ranta ta ce’’inama Bashir bai shigo cikin rayuwarta ba,”
Tunda gashi dai yanzu ba auren ta zai yi ba amman kuma ya zamto silar da zai tarwatsa auren Daddy da Ummi wanda take addu’ar a samu ya d’auree har abada.

Da gudu Munirat ta mik’e ta bar wajen ta na hawaye….
wannan shine duka biyu!!! ga cin mutunci gashi kuma Ummi ta hanata yin magana.

A hankali Mommy tace ‘’Sai da safen ku’’
Daga nan ta mik’e ta bar wajen.

Ummi za ta bar wajen kenan
Yahanasu ta mik’e ta matso ta kamo Hannunta tace “Ummi dan Allah ki yi hak’uri, ko da ace kowa bai fahimce ki ba to ni na fahimce ki, tun a jiya Yash yayi min bayanin komai ta waya, nima kuma a jiyan duk na yi wa Yasira bayani kuma na ji suna maganar Yassira ta tura a group d’in su dan haka kinga sun san labarin kenan kawai dai gaskiyar ce ba sa so kuma suke k’ok’arin dannewa tunda dama abunda ya farun ba shine asalin dalilin su na kyarar ku ba.
kawai ki yi hak’uri Ummi, ki daina k’ok’arin had’a kansu da Munirat dan ba zai tab’a had’uwa ba…
ki zuba musu ido kawai.
ki kwantar da hankalinki Munirat is not alone (ba za ta ji kaɗaici) a cikin gidan nan ba, tunda ina nan, ba za ta yi zaman kad’aici ba, inshaaAllah…’’

Cikin takaici Ummi ta ce
‘’Na gode Yahanasu, amma ko ba komai ya zama dole in ji takaicin yadda Mommy ta ke yin burus akan lamarin nan…
ki duba ki ga yadda nake bata girmanta amma ita in Yaran nan za su wanka min mari ba za ta tab’a hanawa ba.’’
Cikin katseta Baaba Larai ta ce
‘’Ummi, sai dai fa ki yi hak’uri, duk cikin Yaran nan ki gaya min waye kika ga yana jin maganar Mommy a cikin su? Tun daga kan Yassira har izuwa kan Yadira
Yahanasu kada’i ke yi mata biyayya amman ragowar duk binsu kawai take yi.

Dalilin da kika ga yasanya bata saka muku Baki
Shine
Bata so ta shiga fad’an kuma su disgata a gaban ki, dan itama ba jin maganarta akeyi a cikin gidan nan ba!!
hatta shi kanshi Daddy d’in ba bi ta kanta yake yi ba kuma na san kin san me ke faruwa a tsakaninsu shi da ita tunda ta ce min rannan a gabanki ya koreta…….
Ba wai Ina gaya miki hakan dan ki raina ta ba, A’a ina gaya miki ne dan ki daina jin haushin ta, ki yi mata uzuri ki barta da abunda ya ke damunta….
Dan haka idan zan baki shawara ki d’auka to ki daina k’ok’arin tilastawa Yaran nan akan dole sai sun bi ki dan hakan da kike yi kamar kina sake rura wutar rikici a tsakaninki da su ne.
Sannan wani abunda na lura kamar baki sani ba
shine
ko dambatuwa kuka yi da ke da Yaran nan to fa idan ubansu ya zo bayansu zai bi, dan babu abunda ya tsana a duniyar nan kamar ka tab’a masa ƴaƴa…
Dan haka tunda har kika ga uwarsu ma ba ta tilasta musu to kema ki koma gefe ki zubawa kowa ido.’’
Tana gama fad’ar haka ta
wuce, ta nufi sama wajen Mommy..
..
A d’akinta ta sameta tanata faman safa da marwa…
tana ganin shigowarta ta yi maza ta k’arasa wajen ta, a d’an rikice ta ce “yauwa Larai, ke nake ta jira, ya ake ciki?

Ajiyar zuciya Baaba Larai ta sauk’e kafin ta ce
‘’Na barta a k’asa, ita da Yahanasu’’

Cikin katseta Mommy ta ce ‘’Ba maganarta nake yi miki ba, maganar Yashjub nake yi..na gaya miki tun jiya ai..maganar ki gaskiya ce, da Bakinsa ya tabbatar min amman har yanzu ban ji kin ce komai ba.’’
Murmushi Baaba Larai ta yi kafin ta nemi waje ta zauna sannan ta ce ‘’Tunda kika ji na yid shiru akwai dalili….
yanzu
Yahanasu ce naga Bakinta ya fara bud’uwa, kina ganin ba matsala kuwa?.
Na lura da ita, bata shakkar kowa kwana biyun nan, yanzu haka a gabana ta gama aibanta su Kausar sannan k’iri-k’iri Ina kallon idanunta tana kallon nawa amma ta bi bayan Ummi ta bata gaskiya…
shiyasa na ke ganin gara a yi wani abun tun kafin ta je ta b’allo ruwa.”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce
‘’Larai bar batun Yahanasu tukunna, Ina tunanin shurun nata da rashin fitar da take yi ne ya shafe ta har a ta b’angaren aure fa, ko ke ba ki yi wannan lissafin ba?
Ba ki fahimci komai ba?.
Saboda har ga Allah na fara jin tsoron zalintar Yahanasu da nake yi dayawa har haka saboda nawa gain d’in(ribar)’’

Shiruu Baaba Larai ta yi kafin ta ce ’’gaskiya ni kam ba zan bi ta taki ba Khadija, saboda idan Bakin Yahanasu ya bud’u ba ke kadaice a wahala ba, bari ki ji in gaya miki yau tun safe da ta bar gidan nan bata dawo ba sai magrib.’’

Cikin rashin jinn dad’i Mommy ta nemi guri ta zauna itama a kusa da ita kafin a hankali ta ce ‘’shikenan Larai, ki yi abunda kike ganin ya dace.’’

Murmushi Baaba Larai ta yi
kafin ta gyara zama ta ce
‘’Ita kuma Ummi………..’’

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*27*

Sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta fasa zuwa gidan yayarta…da fad’a da rarrashi duk ta haɗa tukunna ta samu ta d’an kwantar mata da hankali, dukda kuwa ita ma hankalin nata ba a kwance ya ke ba…
abun tausayi haka itama Munirat d’in ta shiga kwantarwa da mahaifiyar tata hankali.

sun jima suna magana kafin Ummi ta mik’e ta nufi wajen Daddy jiki ba kwari.

A bakin k’ofar shiga parlourn
suka had’u da Yasmin, tana shiga Yasmeen d’in kuma tana fitowa..ko kallon ta bata yi ba
Itama Ummin bata kulata ba.

Da sallama ta shiga, ba ta same shi a parlournsa ba sai a chan cikin d’akinsa a zaune a kan gado,
Ya yi shiruu alamun tunani yake yi.

A kusa da shi ta je ta nemi guri ta zauna kafin a hankali ta ce
‘’Barka da dawowa Daddy, ya
meeting d’in?’’.

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce
‘’Alhamdulillah’’
Daga nan ya mik’e ya fad’a toilet.

Har ya fito tana nan a zaune,
ta yi zurfi a tunani..

Sai da ya gama shirin bacci tukunna ta ce
‘’Bara in kawo maka abinci’’
Ta fad’i hakan tana shirin mik’ewa.

Cikin dakatar da ita yace ‘’don’t bother, a k’oshe na ke.’’

Cikin kwantar da murya tace
‘’Daddy, ka d’an ci ko kad’an ne m….’’

‘’Wai Saddik’a ni k’aramin Yaro ne?d’ura zaki yi min ko me?
Na ce miki a k’oshe nake amma kin bi kin ishe ni…
daga meeting na dawo Ina buk’atar hutu shin baki da fahimta ne????”

A hankali ta ce ‘’ka yi hak’uri,
Allah ya huci zuciyarka’’…

Har zai kwanta sai kuma ya ce
‘’Ki koma parlour ko kuma ki zab’i wani bedroom d’in ki kwana,
ban ce ki fita a side d’ina ba…kawai ki nemi wani bedroom d’in a parlourn..’’
Sai da ya sake cewa’’bakya ji na ne?’’
Tukunna da kyar Ummi ta ce ‘’to Daddy, sai da safe.’’

Washegari da sassafe ta tashi, tunda ta yi sallar asuba ba ta koma ba, dama tun a daren jiyan ta fitar da abincin da ya ce ba zai ci ba ta saka a fridge dan a lokacin hatta gwaggo ta riga ta tafi side d’insu na masu aiki.

Had’add’en breakfast mai rai da lafiya yau ma Ummi ta shiga had’awa Daddy…
tana cikin yi su gwaggo suka shigo dan haka ta shiga akayi har na gaba d’aya gidan tare da ita.

K’arfe bakwai da kwata suka kammala, dan haka ta d’auki na Daddy ta nufi sama da shi cike da sassarfa.

A bakin k’ofar d’akinshi ta same sa yana gyara zaman necktie d’insa, tun kafin ta gaida shi ya ce ’’koma da abincinki yanzu ma, na k’oshi’’

A hankali ta nufe sa da tray d’in a hannunta da niyyar idan ta je ta durk’usa ta bashi hak’uri, amma tana zuwa kusa da shi tun kafin ta durk’usa ya yi wani irin fatali da abincin wanda ta sanadiyyar hakan gaba d’aya parlourn, kayan jikinsa da kayan jikinta suka b’aci….

Cikin fushi ya juya ya koma d’aki ya bar ta nan a tsaye cikin tsananin tashin hankali da mamaki, bata san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka shiga tsilalo mata ba.

Da kyar ta samu ta goge wajen tana yi tana kuka haka nan ta je ta chanja kayan jikinta tukunna ta dawo ta tattare kwanukan ta nufi k’asa.
Chapter 44 · 0% Book details