← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 84

Sashe 81

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsabar takaici Manubiya bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, cikin kukan ta ce
‘’Baba yaudarar ka ma fa yayi!
cutar ka yayi! Takardun da ya baka ka saka Hannu ba abunda ya fad’a maka ne rubuce a jiki ba!.
Baka ga black snake ya zo ba?
Me ya had’o ka da shi tou tunda shi Yusuf d’in cewa ya yi banki ne’’

Rai a ɓace Baba ya ce
‘’Ko da ace ban yi karatu ba
na san abunda yake a rubuce a jikin takardar nan tunda na san kuma na yarda
Yusuf ba zai cutar da ni ya had’ani da wannan mugun Mutumin ba.
Shi kansa Yusuf d’in yanzu haka a cikin danger yake…..
Shi wannan black snake d’in shi ne ya had’a da ni da shi gaba d’ayanmu ya biyo mana ta k’ark’ashin k’asa’’

‘’To tayaya akayi shi Yusuf d’in ya san Mutum irin….’’.
Maficin da Baba ya jefa mata ne yasanya ta yin shiru….cikin fad’a sosai ya ce
‘’Ungo naki’’
ya fad’i hakan yana yi mata dak’uwa kafin ya d’aura da cewa “ina fad’a kina faɗa! Ce miki akayi ban san me nakeyi ba??’’

Ya Musbah ta kalla wanda ta ga yana yi mata alamun ta yi shiru kawai ta hanyar
d’aura yatsunsa a kan Bakinsa.

Kuka kawai ta sake fashewa da shi tsabar takaici da bak’in ciki, hakanan ta yi shiru Baba ya balbaleta ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kafin daga k’arshe ya tashi ya fita.
Bai ma san ta ina zai fara ba
gashi Uncle ya ce
‘’Idan ya k’i yarda ya siyar da d’akin nashi da filin cikin sauk’i to zai sako hukuma ya fad’i abunda y’ay’ansa sukayi’’.
Saboda Allah ta ya za su yi masa haka? taya za su tsame sa a cikin gidan! Bayaga haka ma ta Ina zai fara neman wani d’akin a wannan d’an kud’in da suka ambata za su siye d’akin.
Yana fita direct masallaci ya nufa ya ci sa’a kuwa babu kowa a ciki….tun tasowar su su Uncle ba su tab’a yi masa abunda ya ji zafinsa kamar na yau ba, wato sun nuna cewa su uwarsu d’aya kenan
shine bare a cikin su
abunda ba su tab’a yi ba kenan….
Fisabilillahi in ba haka suke son nunawa ba
ta ya za a yi case da Yusuf d’an gidan Baba Habu wanda yake kamar d’a a tsakanin su su duka ukun
abunda ya kamata ace su yi sulhu a tsakaninsu su gyara
amman ace wai Uncle ya shigarwa Baba Habu!
Wannan wanne irin nuna banbanci!wulak’anci! da cin fuska ne……!.
Duk yadda Baba ya so daurewa kasawa yayi
bai san lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba……

Baba yana fita su Ya Nafi’u suma suka mik’e suka fita aka bar Manubiya Inna Jidda da Muhsin…
Jidda gaba d’aya ta yi laushi dan gani take yi kamar komai duk laifinta ne shiyasa ta ma kasa rarrashin Manubiyan dan ita ba ma ta san me zata yi ba tsakanin kuka ko ihu!
Da kyar ta lallab’a ta iya mik’ewa ta je ta kwanta a gefen Inna ta yi shiruuu.

Sun jima a haka kafin Manu ta tashi ta fita dan azahar har ta yi.
A kithchen d’in ta zauna tunda ta fara girkin har ta gama sam ba ta damu da hayak’in ba
sai da ta gama tukunna ta juye a kula ta koma d’akin.

Hakanan gidan ya kasance jigum mai sunan baba ne kawai yaketa faman tsalle-tallen sa.

Ya Nafi’u da Ya Musbah kuwa ba su zauna ba har dare, duk
inda suka je ko dai a lissafo musu uban kuɗaɗe ace su nemi lawyer ko kuma tashi d’aya ana ganinsu ma
ace su yi haƙuri kawai dan ansan ba iyawa za su yi ba.

Manubiya ma sai dare tukunna ta d’auki wayarta, ba ta yi mamakin ganin misscalls kusan takwas duk na Yashjub ba dan tunda ta dawo bata bi ta kan wayar ba kuma tun jiya lokacin da ya ce zai kira ta after thirty minutes ta saka wayar a silent gudun kar ta tashi su Baba.

Bataso ta kira shi dan kunya takeji amman haka nan ta daure ta danna call tana sauk’e numfashi a hankali a hankali.
Har ta katse bai d’auka ba dama addua takeyi kar ya dauka d’in saboda na flashing ne kawai da ita ta san kuma yana d’auka mtn za su katse.

Tana tsinkewa kuwa a take ya biyo kiran.
Cikin nutsuwarta ta d’auka ta kara a kunnenta bakinta d’auke da sallama …….……..bayan kamar awa biyu Jidda ta fito ta zauna a gefenta ta na yi mata nuni da alamun lokaci.

Jinjina Kai Manu ta yi kafin ta zaro wayar
ta d’an kalli screen d’in, ba k’aramin mamaki ta yi ba kuwa da ta ga har sun wuce awa biyu suna wayar dan haka ta fara yi masa sallama….
Da kyar ya hak’ura ya kashe bayan ta ce masa bacci take ji sosai……

Murmushi Jidda ta yi bayan Manubiya ta kashe wayar cikin d’an sigar tsokana ta kalle ta ta ce ’’yau ansha till down.
Dama gani na yi tun d’azu Baba yana zaune kar ya fara tambayar ki shiyasa.
Dan naga kamar kun manta da kowa a duniyar sai faman I love u ilove you ake…’’

Toshe mata Baki Manubiya ta yi tana d’an hararar ta kafin ta ce “ba wani I love you kusan ma duk labarin ku ke da Muhsin nake ta bashi’’

A hankali Jidda ta ce ‘’amman dai zuwa yanzu ke kan ki na san kin yarda son ki yake yi ko?’’

A hankali Manubiya ta d’an gyara zama ta kalli Jiddan, tun d’azu basu samu hankalinsu ya dawo Jikinsu ba bare su zauna Shiyasa bata gaya mata komai ba, sai yanzu ne da ta d’an ga walwala a fuskar Jiddan yasanya itama ta samu kwarin guiwar zaiyyane mata yadda sukayi ita da Yashjub d’azu da safe…..tiryan tiryan haka ta bata labarin kafin ta d’aura da cewa “yanzu ma muna fara waya ya ce wai yanaso zai kira Ya Musbah a fara magana, ba yadda ban yi da shi ba amman ya dage wai gobe da safe inshaaAllah zai kira shi’’

Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ’’to da farko dai ‘Alhamdulillah’wallahi na ji dad’i sosai saboda kun dace, abu na biyu kuma shi wannan bawan Allah haka ake yi? Irin wannan zumud’i haka? Ke da baki riga kin ce masa ‘eh’ ba ma,
saurin me yake yi?’’

D’an turo Baki Manu ta yi kafin tace “Nima dai abunda na gani kenan’’

Dariya ce take ciyo Jidda ganin yadda Manubiyan take so ta yi mata basaja k’iri-k’iri
Dan haka ta ce ’’to kawai ki fito ki gaya masa gaskiya mana, ki ce masa kawai bakya son shi’’

Da sauri Manu ta d’ago ta kalle ta ganin yadda Jiddan take guntse Baki tana dariya k’asa-k’asa ne ya sanya ta fahimci jan magana Jiddan take yi dan haka ta kai mata dukan wasa ta ce ’’ja’ira’’

Ahankali Jiddan ta matso ta rungume Manubiya tukunna tace “Ba sai kin fad’a min ba Adda Manu kema na san kina son shi tun ba yau ba, Ina miki addu’ar Allah Ubangiji ya tabbatar da alkhairi sannan ya dauwwamar da farin ciki a rayuwar ku, ya tabbatar da aurenku ya sa kar a samu matsalar komai.’’

A hankali Manubiya itama ta sa hannu ta rungumo k’anwar tata tana mai jin tsananin tausayin ta yana ratsata…..ba dan Ammi ce mahaifiyar Al’ameen ba da ba abunda zai hanata tsayawa tsayin daka har sai ta ga Jidda ta auri Al’ameen, dan ta san yadda Jidda take son Al’ameen tun kafin ta yi wayo shiyasa take tsananin jin tausayin ta dan soyayyar da ta ke yi wa Yashjub ta sanyata ta sake fahimtar yadda Jidda ta ji a lokacin da aka rabata da Al’ameen, dan tabbas in da ace itace wani ya yi gigin rabata da Yashjub to da batasan ya zata yi ba, da wuya idan bata rasa ranta ba.

A hankali ta zaro Jidda daga jikinta cikin rarrashi da bada Baki ta shiga kwantar mata da hankali tare da yi mata addu’ar Allah ya bata wanda zata so sama da Al’ameen wanda zai so ta shima tsakani da Allah.
Sun jima Sosai a wajen suna kwantarwa da juna hankali tare da bada shawarwari kafin su mik’e suka shiga d’aki.

Sai da kowa yayi bacci tukunna Manubiya ta yi. Tunanin ta ya karkata ga Abbakar wanda tun ranar da suka bar asibiti ya daina d’aukar wayarta baya kiranta
gashi su Baba sun hanata zuwa ta dubosa, su ya Nafi’u dai sun koma duba shi dukda kuwa abunda mahaifiyarsa ta yi hakan bai hanasu zuwa ba
amma ita sun ce ba zata je ba.

Ta d’an ji haushin abunda yayi mata dan bata yi tunanin zai
d’auke mata wuta lokaci d’aya haka ba, duk da ta san dama dole mahaifiyarsa za ta kora masa warning a kanta amman bata yi zaton wannan d’aukewar d’iff d’in daga garesa ba amma kuma da ta tuna daraja irinta uwa sai ta goge duk wani takaicinshi a ranta.

Tabbas ta san za ta yi misssing Abbakar saboda shi ɗaya take da shi a matsayin Aboki, amman tunda haka shi da mahaifiyarshi suka tsara ba komai
za ta jure
Allah yasa hakan ne mafi alkhairi….
tana wannan tunanin itama ta ja abin rufa ta yi luff sai kuma ta fara tunanin Yash kafin ta
fara karatun Al’kurani ahankali ahankali a cikin ranta
daganan bacci yayi awon gaba da ita….

A b’angaren Abbakar kuwa
dama tun kafin ya farka mahaifiyarsa da maman Baraka suka gama had’a plan d’in su…….yana farkawa kuwa ko likita ba su kira ya duba shi ba suka shirga masa k’aryar “ai Manubiya ta yi aure Babanta ya aurar da ita a wani mutum yanzunnan aka gama d’aura auren a cikin asibitin.’’
Tashi d’aya Abbakar ya amince kuma tunanin sa ya bashi ai Yashjub aka aurawa Manubiya watak’il ya zo ya taimakesu Baba kuma ya ji dad’in taimakon da ya zo yayi musu shi ne ya ba sa Manubiya.
Chapter 81 · 0% Book details