Sashe 52
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
so tun kafin abun ya kai ga haka..maganin bari kar a soma.Ina yi masa addu’a kai ma ka taya ni..Allah ya shirya sa, bana so in sake jin wata maganar.’’
Da kyar bayan kamar mintuna biyu Yash ya samu ya iya cew Daddy “to “
dan sai da yayi da gaske tukunna ya iya danne fushin sa.
Daga nan ya yi masa sai da safe ya mik’e ya fice, ya bar sa yana tunanin Ummi,
Matar da da har farce take yanke masa! biyayya
kala-kala amman wai ita ce yanzu banda gaisuwa ba abunda yake shiga tsakanin su, yadda take yi wa kowa a gidan haka take yi masa shima babu wannan kulawar ta musamman da take bashi,
abincinsa d’azu da ta kai masa (breakfast)
kawai direwa ta yi ta juya
sannan ba ta je ta wanke masa toilet da gyaran d’aki ba kuma yau ta karb’i girki, yana da tabbacin ba lalle ma yau ta kwana
d’akinsa ba dan ko kallon sa bata yi..
Wallahi! ba dan shekaran jiya jiya ya gama yi wa Hajiya Mama alk’awarin zai zauna da Ummi ba da tuni ya
salleme ta….
He apologized(ya bada haƙuri), tunda har ya ce mata ta zauna a gidanshi ai kuwa kamar he apologized ɗinne (ya bada haƙurin ne) amma duk da haka kalli attitude d’in da take bashi….
Ya jima a wajen kafin da kyar ya samu ya mik’e ya nufi sama ranshi a mugun b’ace, kamar yadda ya yi zato kuwa har asubah ba Ummi babu alamarta, dan haka ya kuma kumbura ya nad’i takaicin ta shima ya ci alwashin zuba mata ido kuma wallahi mistake d’aya idan ta yi sai ya koya mata hankali a cikin gidan duk kuwa da shekarunta ai itama bata san darajar shekaru ba tunda gashi ta raina shi.
Takaici da mamakin Daddy ne suka hana Yash bacci,
babu yadda bai yi ba amma sam ya gagara yin bacci.
He really can’t believe(Ya kasa yarda da) wai Daddy ne ya ja masa layi a kan Yassir,
kenan dai yanzu abunda yake nufi
‘a zubawa Yassir
ido yayi duk abun da yaga dama…’
ta ya ma zai ce laifin Munirat ne bayan ranar
dakyar ya kwaceta daga Hannun Yassir d’in,
he hates to think about it amma maganar gaskiya Daddy is very selfish when it comes to his children
(Baya so ya dinga irin tunanin nan amma Daddy yanada son kai sosai a duk harkar da ta shafi ƴaƴansa).
Ganin takaici yana shirin saka shi d’an k’aramin hauka ne ya sanya kawai ya d’auki waya ya shiga kiran Manubiya lokacin 10 har da rabi.
Sai da wayar ta fara ringin tukunna ya fara tunanin anya kuwa ya dace ya kira ta kar ya je ko ta yi bacci, bayaga haka ma me zai ce mata idan ta d’auka.
Amma kuma he needs her (Amma kuma yanada buƙatarta), yanada bukatar ya ji ko da muryarta ne, ba shi da wani zaɓin….
Yana cikin wannan tunanin ya ji
sautin muryarta a hankali ta ce
‘’Assalama alaikom’’
A hankali ya lumshe idanuwansa yana sauraron ta tana ta
hello!hello!!’’
Sai da ta jera wajen hud’u
tukunna da kyar ya ce
‘’Ki zo da wuri gobe, sannan ki zo da SScertificate ɗin naki’’.
‘’Ok,inshaaAllah’’
Ta ce, daga nan ta yi shiru..
Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya samu ya iya kashe wayar dakyar yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa….
Washegari..
Ya Musbah ya so ya raka ta sai aka yi rashin sa’a me sunan Baba ba shi da lafiya, dan haka ya barta ta tafi ita kad’ai su kuma shi da Baraka da Muhsin suka tafi kai Yaron asibiti.
7:3O ta Isa bakin company d’in na shi, k’irjinta yana abunda ya saba a duk lokacin da ta san ta kusanto shi.
haka nan ta nufi gate d’in,
sauri take so ta yi ta gama dan tana da exams kuma bata samu ta lek’a gidan Ammi ba dan sai da suka ɗan yi meeting ita da Ya Musbah akan ‘ya karb’i kud’in da Baba ya bata ya biya kud’in hayan su sa ci gaba da aikin ba komai’
dama ta san ba zai yarda ba ai kuwa ilai yak’i amincewa,
, shiyasa bata samu ta je gidan ba saboda bata gama yanke shawara da farko ba da kuma ta gama yanke shawarar lokaci ya riga ya shige mata, dan haka in dai ta gama da nan da wuri tana so ta biya gidan Ammi su gama da ita tukunna ta wuce exams saboda kar matar ta ga ko dan ta bar aiki shine yau zata yi mata wulak’anci ta bar ta da aiki ya kai rana……
..
Tana zuwa bakin gate security ya gaisheta ya bud’e mata k’aramar k’ofa ta wuce ciki.
Yau ma Racheal ce ta yi mata rakiya har chan sama office d’in nasa amma yau ba ta shiga ba suna zuwa ta ce mata ta shiga ita kuma ta juya ta koma.
Tana hango shi fad’uwar da gaban ta yake yi ya tsananta…
yau black suite yake sanye da
amman ya cire babban suite d’in ya sak’ale ya bar k’aramar ta ciki armless (marar Hannu) da white long sleeve (farar riga ta ciki mai dogon Hannu) din da suka yi masa asalin kyau,
ba ta san ya aka yi ba kawai sai ta shagala da kallon sa tana mamakin tsananin kyawu da kwarjinin da Allah ya ba shi.
Tana tsayawa a wajen jikinsa ya ba shi da Mutum a gurin dan haka ya d’ago da niyyar tabbatarwa
yana d’agowa kuwa suka had’a ido da ita.
Da sauri ta sunkuyar da kanta dan tashi d’aya duk sai ta diririce…..kafin da kyar ta samu ta d’an d’aga hannunta ta yi knocking a hankali tukunna ta tura k’ofar ta shiga a hankali bakinta d’auke da sallama…….
*MANNUBIYA*
*31*
A hankali ya amsa..yau ma kamar ranar farko haka ya kafe ta da idanu tun lokacin da ta shigo har ta k’araso ta zo ta zauna a hankali ta ce
‘’Good morning Sir.
(Ina kwana, sir).”
A hankali ya samu ya ɗan motsa ɗan mitsitsin bakinsa ya ce
‘’Morning’’
ya fad’i hakan still idanunsa na a kanta….
yana son blue a rayuwar sa gashi yau Manubiya ta sako royal blue d’in hijab wanda colour d’in ya fito sosai, har da kwalli da man leb’e yau ta saka
wanda hakan ya sake rikita Yashjub dan lokaci d’aya ya ji komai ya tsaya masa chak!..tashi d’aya ta tafi da imanin sa.
Ganin da Manubiya ta yi Yashjub ba shi da niyyar daina kallon ta ne ya sanya ta d’auko wayarta ta shiga yi masa bayanin k’orafin da aka bata…
baiwar Allah har printing ta yi ta taho da shi dan ita har gobe ganin sauk’in aikin ta ke yi sosai!
duba da yadda za’a dinga biyan ta har 3Ok a wata…
sai da ta karanta masa ta d’ora da bayani tukunna ta hada da certificate d’in nata da takardar ta tura masa gaban shi.
Shi dai Yash ya ga ta ajjiye takardu kuma ya san tanata magana tun d’azu amma
wallahi shi bai fahimci komai ba..duk bayanin da ta yi sam bai fahimci ‘Alif’ daga ciki ba.
kallon ta kawai ya ke yi yana jin wani sanyi da nutsuwa sannan yana lissafin mallakar ta a matsayin Mata…....yana mai addu’ar Allah yasa idan an fara maganar auren su kar a d’auki lokaci mai tsayi...shi kad’ai ya san me yake ji game da baiwar Allah n nan,a hankali ya fesar da numfashi ya lumshe idanunsa…
lokacin da yake ganin Abokansa a makaranta suna hauka a kan y’an matan su haushi suke ba sa,yanzu kuwa ya daina ganin laifin su dan a halin da yake ciki baya jin akwai abunda ba zai iya aikatawa akan baiwar Allah n nan ba muddin bai sab’ama addinin musulunci ba, ko ihu ne idan Manubiya tace tana so ya yi ta kurmawa tou tabbas a shirye ya ke, zai kurma!!!!
Ashe haka so yake?….
Yahanasu ta yi gaskiya,dan yana bata labarin Manubiya ta ce masa
“in bai yi sauri ya gaya mata yana son ta ba to nan da y’an kwanaki kad’an sai ya ji kamar ya yi hauka.”
“Sir I’m done(sir, na kammala bayanin)”
Muryar Manubiya ta katsewa Yashjub tunani wadda ta fad’i hakan ba tare da ta kalle sa ba.
‘’You look cute today!
(Kin yi kyau yau!)’’
Muryar Yashjub ta dira a cikin dodon kunnuwan Manubiya.
Wani irin fad’uwa gabanta ya yi wanda har sai da ya sanya ta d’an sake sunkuyar da kanta k’asa.
Kamar ta fashe da kuka haka ta ji…
Tabbas Yashjub so yake ya karya juriyarta dan in aka ci gaba a haka ba zata iya ci gaba da tsayawa kai da fata a kan abunda ta yi wa kanta alƙawari dan ta ga alamar ya dage sai ya ga bayan d’an guntun kwarin guiwar tata, bai san a ta ya take iya yin aikin nan da shi ba! bai san me take ji ba! bai san yadda take kokawa da zuciyarta bane ba…..
Tana buk’atar aikin nan
saboda ta samu ta kula da ahalinta amma muddin zai dinga torturing d’inta(wahalar da ita) irin haka gaskiya ba zata iya jura ba gara ta nemi wani hanyar taimakawa ahalin nata, dan ba za ta yadda ya juyar mata da tunani ba.
Tana sane da shi akan kiran da ya yi mata jiya akan maganar certificate….bayan tuni a zuwanta na farko ya riga ya ce mata ta taho da certificate d’in nata
photocopy, amma shine ya kama ya wani kira ta jiya cikin dare.
Ba ta san takun da yake haɗawa akanta ba amma tabbas ba za ta ba shi k’ofa ba, tunda ta san ba auren ta zai yi ba dan wannan ba sa’an auren ta bane ba, dan ko da ace ya yi niyya ma ta san yana zuwa idan ya ga yanayin gidan su zai fasa, bayaga haka ma ta ma san yana da matar shi tuni dan wannan a shekarunsa ga kud’i ga kyau ya ci a ce yana da mata da Yaro ko Yara….