Sashe 7
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin rashin jin daɗi ya ce
‘’Manu, bana jin daɗin ɓoye-ɓoyen nan da kike yi mini kwana biyun nan, idan akwai wata matsalar da ban san da ita ba
Talk to me…ki gaya mini, mu
samu mu nemo mafita tare, ko kin daina trusting ɗina ne?”
ya ƙarashe tambayar tashi a hankali yana mai kallon ta.
Sai da ta sauƙe ajiyar zuciya tukunna ta ce
‘’Ba haka bane ba.’’
Cikin tarar numfashinta ya ce
‘’To yaya ne?’’
Girgiza kai kawai ta yi tana jin wani takaici ya na sake lulluɓeta, kafin ta ce
“Kaka Mallan ne, ya ke so ya ɓullo da wani sabon issue.”
A hankali ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya kafin ta ci gaba da cewa
‘’sai kuma Baraka itama…”
Sai kuma ta ɗan yi shiru,
chan kuma kawai sai ta ce
‘’Kaka Mallam ne ya ce wai in bar makarantar
in yi aure.”
Da sauri Abbakar ya ce
‘’what? Saboda me wai?”
A hankali ta ce
‘’Nima ban san dalilin sa ba,
kawai ya ga kwana biyu ciwon Inna ya motsa shine ya ke son sake ɗaga mata hankali ita da Baba…”
Saboda In ba hakan ba meye zai sa ya ɓullo da wani case ɗin? Ai ya san Baba ba ya so ace ba za mu yi karatu ba,kuma ya san baya son yawan yin jayayya da su.”
‘’Ya kamata a yi wani abun akan wannan tsohon fa‘’.
Abbakar ɗin ya ce cikin rashin jin daɗi. Sai kuma ya ɗaura da cewa
‘’me Baba ya ce?”
Cike da damuwa ta ce
‘’Shiru ya yi, kuma ni har ga Allah ina jin tsoron shirun nan da ya yi…
Ina Jin tsoro kar ya amince saboda ka san san shi baya son yin hayaniya da su.”
Da sauri Abbakar ya ce
‘’Ba na jin Baba zai yarda su hana ki karatu fa, No matter what‘’
Cikin gyara zaman sa da bata dukkannin attention ɗin sa
ya ce
‘’Ki nutsu ki daina ɗaga hankalinki dan Allah, ki kwantar da hankalinki kar ki damu inshaaAllah sai kin yi har PhD, kar ki taɓa bari tsohon nan ya hanaki walwala ya saka ki a damuwa, kalli yadda kike kuka a aji fa.”
Ya ƙarashe maganar cikin rashin jin daɗi.
Jin jina kai kawai ta yi, daga haka ta fara ƙoƙarin miƙewa.
A hankali ya na kallonta ya ce
‘’Ita kuma Barakan mai ta yi?”
Sai da ta ɗan kalle shi da kyawawan rinannun idanuwanta tukunna ta kauda kai gefe ta ce
‘’Ba komai ‘’
Daga haka ta miƙe tsaye.
Da sauri shima ya miƙe ya ƙarasa gareta sannan ya ce
‘’Ya jikin Inna? An haɗa kuɗin kai ta asibitin?’’
Da sauri ta ce
‘’An haɗa”
daga haka ta juya ta nufi ƙofar fita.
Tun ɗazu dama ya so ya gano a inda main problem ɗin da ya sanyata kukan ya ke!
Yanzu kuma yadda ta yi ya tabbatar masa da hakan….
Ya riga ya san ko me zai yi ba zata yarda ta karɓi sisi a wajen sa ba sannan
ya fahimci Baraka ta kuma yin abunda ta fi komai ƙwarewa akai wannan karon ma!
Inda ya ke da tabbacin ta ɓullo
da wani abun ne ta amshe gaba ɗaya kuɗaɗen Haannun Ya Musbah…
Ya rasa gane dalilin da ya sanya
Baraka ta ke wannan rashin imanin, bai san menene a kanta ba!
Bai kuma san dalilin da ya sanya Baba da Ya Musbah su ke biye mata suke ɗaga mata ƙafa ta ke tsula duk tsiyar da ta ga dama ba!
Ganin da Abbakar ya yi Mannubiya har ta fice hakan ya sanya shima ya bi bayan ta da ɗan saurinsa, a ranshi kuwa ya riga ya gama yanke shawarar abunda ya kamata ya yi wajen taimaka mata domin a samu a kai Innar Asibiti..
Matar satin ta kusan ɗaya ta na fama da ciwonta wanda ya motsa mata, tabbas ya kamata ace ta je ta ga Likita.
Yana fita ya hango ta
har ta ɗau hanyar da zai sada ta da gate…
Dan haka ya ƙarasa su ka nufi gate ɗin tare shi da ita.
Ba gida zai yi ba shiyasa basu tafi gidan tare ba, amman sai da ya sanya ta a adaidaita sahu ya biya kuɗin kamar kullum tukunna ya juya shima ya tari tashi adaidaita sahun ya shige ya yi gaba……
Anguwar su ɗaya da Abbakar shine best frnd ɗinta…tun daga sakandire Abotar tasu ta yi ƙarfi, amma tun su na Yara su ke shiri dama.
Abokanayen sa Maza har dariya su ke yi masa, dan
tun yana ɗan mitsitsi ya ke
wanke ƙafa ya tafi gidan su Manubiya wasa, tun Inna ta na hanawa har ta zo ta daina.
Har kawo yanzu kuwa shi kaɗai ne Abokin ta tun da ita ɗin
Ba kula ƴan unguwar su ta ke yi sosai ba saboda munafurce munafurcen su…..
a makarantar ma
ta ƙi yarda ta yi ƙawaye, dukda yadda ake son yin ƙawance da ita amma ita ta ƙi yarda, duba da yadda yaran su ke ƴan gayu
a ganin ta idan ta biye su za a iya zuwa gaɓar da za ta kasa godewa Ubangiji na na’imomin da ya yi mata.
gashi kullum idan aka je wajen cin abinci sai dai su yi ta biya mata
kuɗin
Ba wai suna complain bane kawai dai itace ba ta feeling comfortable (ta kasa sakewa da hakan) kuma ta san
yau da gobe sai Allah
shiyasa ta ke ta zizzillewa.
Tun suna yi mata naci tana zillewa har suka haƙura suka rabu da ita. Su suna ganin girman kai gare ta, yayinda Ita kuma a nata ganin bai kamata ta ɗaurawa kanta abunda ya fi ƙarfin ta ba,
Matsalar ta ma ita kam ta isheta.
Tana wannan tunanin mai Adaidaita sahun ya ƙaraso cikin layin nasu wanda ke a Anguwar ‘Gadon ƙaya’,.
Ita ta nuna masa ƙofar gidan ya yi parking daga haka ta fito ta nufi gidan bayan ta ce masa ta gode .
Tun a kallo ɗaya, in aka yi wa gidan ya ke faiyyace daɗewarsa a doron ƙasa, sannan bai ma san me ake nufi da renovation (sabunta gini) ba.
Katangar gidan both side sun tsatstsage, yayin da fentin ya goge gaba ɗayan shi!
Ba’a ganin komai sai jar ƙasar ginin gidan wanda ya baiyyana daga tsakiya zuwa ƙasa, ta saman katangar kuma ragowar farar ƙasar fentin da bata gama gogewa ba ce itama duk ta yi dishi-dishi, sai zanen Yara na shirme wanda akayi da baƙin gawayi, duk a jikin katangar.
Normal ƙaure ne a gidan sai dai shima ya ji jiki matuƙa……
Tana ƙarasawa jikin kyauren ta kama ta tura ƙofar ta kutsa kanta cikin gidan…
Dama tun daga waje yanayin gidan ya ke nuna Babban gida ne, saboda yanayin faɗin tsayin katangar…
Ta wani dogon soro ta bi
kafin ta ƙarasa ainihin cikin farfajiyar gidan!
A ta farko-farko gefen dama babban kitchen ɗin gidan ya ke wanda murhu da kurfeti suka cika shi taf ta inda hakan ya ke nuni da kowa girkin shi ya ke yi a daban.
Farfajiyar asalin cikin gidan kuwa ɗauke ta ke da fanni-fanni wajen guda takwas!
Wasu sabbi ƙal ginin zamani
wasu tsofaffi tukuf ginin ƙasa
Wasu manya ne domin tun daga kallo ɗaya in an musu an san za su ƙunshi wajen ɗakuna uku sannan a ciki har a samu parlour ma sai kuma masu ciki da parlour, yayinda wasu kuma ɗaki ɗaya ne kawai sai banɗaki…..
Ginin daya fi ko wanne tsufa kuma ɗaya daga cikin jerin ƙananun buildings ɗin Manubiya
ta nufa, tana zuwa dai-dai bakin ƙofar ɗakin ta sa Hannu ta ɗaga labulen ta shiga ciki da sallama.
Babban ɗaki ne sosai da manya manyan taga guda biyu suna kallon juna
sai ƙofar banɗakin da ta ke a chan kusurwar ɗakin.
Ƙatuwar katifa ce kawai a yashe a gefe cikin ɗakin.
Sai babban wardrobe na katako..
Laidar ɗakin bata wani yayyage ba ammanfa ta ji jiki dan ta yi laushi matuƙa…kallo ɗaya za a yi mata a fahimci takatsantsan da kula ne kawai su ka kawota war haka ba ta fatattake ba.
Wata farar budurwa, fara ƙal, ce, zaune a kan katifar ƙafafunta su na ƙasa. dududu budurwar ba za ta wuce shekaru sha bakwai a duniya ba, sai gefen ta kuma wata dattijuwar mata ce kwance a kan katifar, budurwar na yi mata fifita.
Tun a kallo ɗaya yanayin Matar ya ke nuni da abun tausayi dan sosai ta ke jin jiki, a zahirance da baɗini.
Saitin su kuma wani dattijon tsoho ne zaune da wani Yaro a gefen shi, Yaron ba zai wuce shekaru sha ɗaya a duniya ba, dattijon kuma ba wani mai shekaru bane a baɗini a zahirance ne kawai tsufanshi ya fito ya baiyyana muraran saboda yanayin rayuwa.
Fuskokin su gaba ɗayasu, babu walwala! Kowa ya yi jigum, ana ta tunani, Ba ma su san Manubiyan ta ɗaga labulen ba har sai da su ka ji sautin muryarta, sanda ta shigo da sallama.
Jidda, wadda ke zaune a kusa da Inna ce ta ɗago ta kalle ta a hankali ta ce
‘’har kin dawo?
Sannu da zuwa.’’
Jinjina kai kawai Manu ta iya yi kafin ta juya ta kalli Muhsin
wanda ya ke yi mata sannu da zuwa shima, ta yi masa wani guntun murmushi tukunna cikin nutsuwa ta ƙarasa ta durƙusa a gaban Baba ta ce
‘’Baba Ina wuni.’’
Kamar ba zai yi mata magana ba sai kuma ya ce
‘’Mai yasa baki ɗauki kuɗin motar da na ajjiye miki ba?
Bana ce miki munada kuɗin abun karyawa ba?.
Mai yasa kike da taurin kai ne?’’
ya jero mata tambayoyin a jere kafin ya ɗaura da cewa
‘’Ce miki akayi nan da b.u.k ɗin tafiyar wasa ce?”
Ya ƙarashe tambayar ta sa ta ƙarshe cike da rashin jin daɗi da takaici.
A hankali ta sunkuyar da kanta ƙasa tukunna
ta ce
‘’ka yi haƙuri Baba ba zan ƙara ba.’’
Sai da ya ɗan fesar da iska tukunna ya kauda kai gefe ya ci gaba da tunanin da ya ke yi kafin ta shigo.
Su Jidda ta juya ta kalla kafin ta ce
‘’Ya jikin nata?”
Da kyar dan sai da ta haɗiye wani abu wanda ya tokare mata maƙoshi tukunna Jidda ta ce
‘’Da sauƙi. Alhamdulillah .’’