← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 84

Sashe 51

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘’Tunanin me kike yi?’’
Muryar Manubiya wadda ta shigo yanzun ta katsewa Jidda tunani.

Da sauri ta d’an matse kwallar da ta tarar mata tana shirin zubowa sannan ta ce
‘’Ba komai, ya aikin?’’
Ajiyar zuciya Manubiya ta sauk’e kafin ta ce
‘’Huh!Alhamdulillah…
Ammi fa ta tafi next level, dan ma Allah ya taimake ni gobe zan gama exams d’ina..wallahi abubuwa duk sun yi min yawa especially a gidan Ammi, dan ma akwai Maama.. Mace mai kirki wani lokacin fa ita take taya ni wasu abubuwan, ta ma ce za ta shigo ta duba Inna.’’
Manubiya ta k’arashe maganar tana mai neman waje ta zauna a kusa da Jidda.

‘’Allah sarki,sannu!ki yi hak’uri duk ni na janyo muku’’
Jidda ta fad’i hakan cikin rashin jin dad’i.

Murmushi Manubiya ta yi
tana kallon ta kafin ta ce ‘’Ba komai kar ki damu, Allah yasa mu dace’’

Ahankali Jidda tace’’Ameen’’dai dai nan Baba ya shigo bakinsa d’auke da sallama.

ahankali ya nemi guri ya zauna..cikin girmamawa suka gaida shi ya amsa kafin Jidda ta mik’e ta fita domin ta je ta kawo masa abinci, daga haka d’akin ya yi shiru kowa da tunanin da yake yi a ransa.

Manubiya Yashjub ne ya b’ata mata rai, jiya aka yi mata ƙorafin abu dan haka ta ce masa “akwai report via watsapp..
(Akwai ƙorafi ta watsapp)”

Kanshi tsaye ya amsa mata da reply ɗin da ya dame ta ya hanata sukuni ’’Okay dear, you can report to me tomorrow
as planned, take care.
(Tam dear, za ki iya sanar min da ƙorafin nasu gobe kamar yadda muka tsara, ki kula da kanki)”.
Tabbas ya kusa tarwatsa mata zuciya da ta gani, dan me yasa zai ce mata wani ‘dear’,
bai san yadda zuciyarta ta buga ba da taga reply d’in har yanzu bata gama dawowa daidai ba.
Gaba d’aya ya sakar mata da kasala daga reply d’in, anya kuwa ba za ta tura masa bayanan ta watsapp ba goben ta ƙi zuwa ta yi k’aryar bata da lafiya…
dan tun jiya ta fara fargabar had’uwar su ta gobe, bata so ta fara feeling wani (jin wani) abu na daban game da bawan Allahn nan dan bata shirya shan wahala akan soyayya ba..iyakar ganin sa da muryarsa ma kad’ai kid’ima ta su ke yi dama yanzu kuma ya kama ya wani ce mata ‘dear’
Tun safe ya rikitata……

Shigowar Jidda ne ya katse musu tunani gaba d’aya su biyun, da ladabi ta k’arasa ta ajjiye abincin a gaban Baba sannan ta koma gefe ta zauna.

A hankali Baba ya d’ago ya kalli Manubiya kafin ya zaro bandir na kud’i daga aljihunsa ya mik’a mata….
cikin nutsuwa ta matsa ta sanya Hannu ta karb’a, tana shirin yin magana ya ce “gashi gobe idan kin je ki bawa Ammi, na ke da Muhsin, kun bar aiki kenan inshaaAllah.
ku samu ku huta Allah ya yi muku albarka.
InshaaAllah wani satin idan aka koma makaranta da shi(Muhsin ɗin) za a shiga….
Idan kin huta zuwa ko anjima ne sai ki je ki tambayi kud’in uniform da shiga da duk abubuwan da ya kamata a makarantar Mazan chan, zuwa dare inshaaAllah zan bawa Musbahu kud’in ya je ya biya masa in Allah ya kaimu aka koma sai a fara tare da shi.”

A hankali Manubiya ta ce ‘’An gode Baba Allah ya saka da alkhairi, ya k’ara bud’i, ya bawa Inna lafiya’’

Cikin tsananin sanyin jiki Jiddah ma ta ce ‘’an gode Baba’’

A hankali Baba ya ce ’’Ameen’’.

Daga nan duk su biyun suka yi shiru….

…A Ina ya ke samun kud’i?
Gashi tun last time ya kora musu warning d’in ‘kar wadda ta sake tambayar sa a inda ya ke samun kud’i, idan ba haka ba kuma ransu zai yi mummunar b’aci, Wallahi….’

Har ya gama cin abincin ba wadda ta iya sake cewa komai, ya na gamawa ya mik’e da shirin sake fita…cikin girmamawa su ka yi masa a dawo lafiya, sai da ya je ya shafa fuskar Inna wadda take baccin ta cikin kwanciyar hankali tukunna ya sa Kai ya fice daga d’akin…

Yana fita Jidda ta ce
‘’Adda Manu inajin tsoro fa, ta
Ina Baba yake samun kud’i haka lokaci guda??’’

Ajiyar zuciya Manubiya ta sauk’e kafin tace ‘’Jiddah ni kam ta ya za a yi in sani?
let’s just hope for the best(kawai mu yi fatan hakan alkairi ne),
dan nima gaskiya kaina a d’aure yake.
kina karatu kuwa sosai?
post utme d’in ku fa ta matso. ‘’

Ahankali jiddda tace ‘’eh,Ina yi, ku taya ni da addu’a’’

‘‘InshaaAllah’’
Manubiya ta ce,kafin ta mik’e ta koma gefe ta d’auki takarda ta shiga karatu…dan gobe mai tashin kafin asuba ce saboda exams d’in 9 gare ta, ga shi a goben ne za ta had’u da Yash, Allah ya taimake ta ita da gidan Ammi sun yi bye bye, ba dan haka ba da bata san yaya zata yi goben ba.
….
Kalar tsalle da murnar da Muhsin yayi lokacin da ya ji labarin tafiyar sa makaranta sai da ya bawa su Manubiya mamaki, amma da suka tuna yadda Yaron yake da k’ulafucin makaranta sai suka yi masa uzuri, dan bai yi murnar barin su aiki a gidan Ammi ba kamar yadda ya yi murnar saka shi a makaranta da za ‘ayi..
Tun daga lokacin da ya ji zancen kuwa..in dai ya san sunan abu da turanci to fa ba zai fad’a da Hausa ba, murna da shak’iyanci kala-kala haka ya dinga yi ya yi ta saka su dariya da walwala kuwa
dan wunin ranar haka suka kasance cikin farin ciki wanda hakan ne ya taimakawa Manubiya ta samu fargaba da tunanin had’uwarta da Yash ta gobe ya d’an yi skipping mind d’in ta(ya ɗan bar kanta).
••••••••
Da ikon Allah yau har aka fara gabatar da dinner su Yasira ba su yi wa Ummi rashin ɗa’a ko kallon banza ba, wanda hakan ya riga ya Zamto d’abiar su..dan in dai suka had’u to wajibi ne ta fuskanci rashin mutunci daga gare su.

Ba su gaishe ta ba dai kuma Daddy bai ce su gaishe tan ba kamar kullum, haka ake kan gabatar da dinner d’in..
ta kuwa ji zafi amma yadda ta yi alk’awarin fita harkar Daddy da ya’yansa ne ya sanya ta tartarasu ta zuba a kwandon shara.

Sai da aka kusa kammalawa tukunna Yassir ya sak’k’o k’asan.
Daddy kawai ya gaisar daga nan ya cewa Yusra ta yi serving d’in sa…

A hankali Munirat ta d’an d’ago ta kalle sa ai kuwa suka had’a ido, murmushi yayi mata daga nan ya d’auke Kai da sauri gudun kar Kausar ta kama sa..

Ɗaya bayan ɗaya duk suka shiga watsewa har dining d’in ya rage daga Yassir sai Daddy, Ya’isha da Yash.

Yassir yana shirin tashi
Yash yace ‘’Days ago (kwanan baya) na je d’akinka kana bacci’’

‘’Yeah’’
kawai Yassir d’in ya ce ba tare da ya kalli inda Yash yake ba ma, daga haka ya mik’e da niyyar barin wajen gaba d’aya.

Har ga Allah Yash ya d’an so su fahimci juna a kan abunda ya faru amma attitude d’in da Yassir( yadda Yassir ɗin) yayi masa ne yasanya ya fasa, dan haka cikin b’acin rai ya ce ’’ban gama da kai ba’’

Still ba tare da Yassir ya kalli Yash ba ya ce ’’good 9te,Daddy(Daddy sai da safe)”

A zuciye Yash ya mik’e amma kafin ya yi wani abun tuni Daddy ya tsaida shi ta hanyar ruk’o hannunsa, da sauri ya maida shi ya zaunar da shi.

Hakanan Yassir ya sa Kai ya wuce, yana wucewa Ya’isha ma ta yi musu sai da safe ta wuce..

Da kyar Yashjub ya d’an yi
controlling kansa tukunna ya bawa Daddy labarin abunda ya faru wanda har ta kai sa ga dukan Yassir d’in.
Sannan ya d’aura da cewa “ya kamata Yassir ya bar cikin gida haka tun kafin a samu matsala’’.

Cikin son fahimtar da shi Daddy ya ce ’’Yashjub, kai ne ka ce Yassir ya dawo cikin gida, bai yi ja-in-ja da kai ba haka Yaron nan ya yi maka biyayya duk da baya so amma a hakan ya hak’ura ya dawo ya zauna, duk dan a zauna lafiya..kaga kuwa idan ka ce sai ya sake komawa wajen ka yanzu a gaskiya ba ka yi adalci ba Yash,
besides i don’t think
(Bayaga haka ma bana jin ) bayan abunda ya faru a tsakanin ku zai yarda ya dawo ku zauna tare.
Ya yi min maganar kafin kai ka yi.
Ka kwantar da hankalinka zai bar cikin gida amman sai nan da three months idan an gama masa nashi ginin wanda za a fara a wanchan filin da yake jikin gidan nan in yaso in an gama sai a fasa a had’e da nan…

Yassir is not a kid (Yassir ba Yaro bane ba) dan haka bai
kamata mu ce za mu dinga juya shi muna controlling d’insa haka ba, he deserves to make his own decisions(ya kamata a barshi ya yi yadda ya ga daman tsara rayuwarsa).

Maganar Yarinyar nan kuma, na fahimci komai da kaina, tun kafin ma in ji wannan bayanin naka tsaf na fahimci ‘ita take kai kanta gare shi’
so na same shi na ja masa kunne kuma ya yi min alk’awarin zai fita a harkarta har abada..

therefore
Yassir is good to live here
(Dan haka babu aibu da damuwa a cikin zaman Yassir a nan),
har zuwa lokacin da za a gama masa ginin sa shima, ya koma.

Kar ma ka ce ya koma side d’inka a gaban shi ya yi maka musu daganan raini ya shiga tsakanin ku, dan nima ban goyi bayan ya koma d’in ba bayan abunda ya faru a tsakanin ku, na fi ganin dacewar ku zauna a saperate wajen zama(wajen zama daban daban), dan na san ba zaku zauna lafiya ba, na san ka da zuciya..za ka ce ya yi abu which na san definitely ba zai yi ba (wanda inada tabbacin shi kuma ba zai yi ba)..zai yi maka rashin kunya kai
Kuma zaka ce zaka dake shi shi kuma zai ce zai rama daganan kuma abun ba zai yi dad’i ba…!
Chapter 51 · 0% Book details