← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 84

Sashe 62

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da aka sake saitawa Ya Musbah da ya Nafi’u bindigu tukunna suka nutsu!
Baba kuma ya ce “shikenan ya yarda zai d’aura auren”
ya fad’a musu hakan, a ransa kuma yana tunanin ta yadda zai nemi mafita su samu su zille.

Wani kalar murmushi black snake yake ta zubawa wanda ya ke nuna tsantsar farin cikin da ya ke a ciki…
bai tab’a had’uwa da Macen da ta sace zuciyarsa tashi d’aya kamar Manubiya ba, shiyasa har Allah Allah yake ayi ayi a d’aura musu aure, ya samu cikakken iko a kanta, za ta ga soyayya, ya san za ta yarda da shi, duk da kuwa taurin kanta da yadda ya fahimci tana jin tsoronshi amma ya san idan ta ga ya riga ya zama Mijinta to dole ta yarda da shi sannan zai sameta yadda yake so dan ya san za ta yi mishi biyayya….

Ga Manubiya matarsa wadda zata haifa mishi y’a y’a ga kuma jidda a gefensa mistress..
wannan wacce iriyar rana ce haka mai sa’a ta riskeshi!
Tabbas ya zama dole ya yi wa Kabir babban kyauta idan komai ya tabbata.
••••
Around 2:OO pm,
yana tsakiyar meeting kira ya shigo wayarshi, kamar ba zai kalla ba sai kuma ya d’an zaro wayar, ganin sunan Najeeb ya sanya shi saka wayar a silent ya ajjiye ta a gefensa, dukda kuwa ya san koma menene tou it’s very important tunda har Najeeb ya yi kiran shi a dai dai wannan lokacin…dan ba su dad’e da gama waya da shi ba ya ce masa ‘zai sake shiga wani important meeting d’in da su Daddy, bak’in nasu har yanzu basu tafi ba, but in ya fito zai kira shi.’

Ba zai yiu ya amsa wayar ba, dan meeting d’in da su ke yi mai matuƙar mahimmanci ne, shiyasa ya bari akan idan sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb ya ji dalilin kiran..
Kawai dai yana fatan Allah ya sa dalilin kiran ba abune mai mahimmanci sosai sannan wanda ake buƙatarsa da gaggawa ba, sannan yana fatan Allah ya sa har zuwa lokacin da za su gama meeting ɗin nasu lokaci bai riga da ya ƙure game da kiran da Najeeb ɗin ya yi masa ba….
*MANNUBIYA*
*37*

Ba zai yiu ya amsa wayar ba, dan meeting d’in da su ke yi mai matuƙar mahimmanci ne, shiyasa ya bari akan idan sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb ya ji dalilin kiran..
Kawai dai yana fatan Allah ya sa dalilin kiran ba abune mai mahimmanci sosai sannan wanda ake buƙatarsa da gaggawa ba, sannan yana fatan Allah ya sa har zuwa lokacin da za su gama meeting ɗin nasu lokaci bai riga da ya ƙure game da kiran da Najeeb ɗin ya yi masa ba…..
…..
Kiran Yashjub Najeeb yake yi yana sake maimaitawa..ganin ya jera masa kira sun fi sha biyar amman bai d’aga ba ne ya sanya Najeeb d’in yanke shawarar ya tura masa message kawai, dan haka ya rubuta:’Yash, Manubiya tana da buƙatarka, ban san menene ya faru ba amma her friend(Abbakar)ya ce min
It’s very urgent!.’
Daga haka ya tura masa tare da address d’in police station d’in da su Abbakar suka turo, yana adduar Allah yasa ya gani ya kira.

A bangaren Yashjub kuwa dama tun d’azu ya nemi nutsuwarsa ya rasa, haka kurum ya ke ta jin wani iri..
so yake ya amsa kiran ko ya yi excusing kan sa ya fita amma kuma ya san idan yayi hakan zai gamu da b’acin ran Daddy ba na wasa ba!…
Yana cikin wannan tunanin ya ji k’arar shigowar message dan haka ya juya ya kalli wayar tasa.

Wani Irin bugawa k’irjinsa ya yi!
Bai san lokacin da ya mik’e tsaye ba
sakamokon message d’in sir Najeeb daya samu damar karantawa ta saman notification bar.

Da sauri Daddy ya ce
‘’Yash.’’

A d’an rikice ya kalli Daddy
sai kuma ya kalli Yasira da ragowar turawan da ke a wajen kafin ya ce
“sorry,i have to
go, it’s very important
(Ku yi haƙuri, zan je ga wannan kiran, yanada matuƙar mahimmanci)”
Ya fad’i hakan yana mai kallon wayar tasa sannan yana kallonsu, kafin ya tura kujerar tasa baya riƙe da wayar ya fita daga hall d’in gaba d’aya
kamarwalkiya yana mai cewa “pls excuse me(dan Allah a yi min afuwa)”.

Yana fita ya shiga kiran number Najeeb…in banda bugawa ba abunda k’irjinsa ya ke yi..Manubiya a police station kuma!ta ya?garin yaya!…..
shi da yake ta fafutukar zuwa k’auye wajen ta, mai ya dawo da ita har ya kaita ga zuwa police station.
Yana wannan tunanin ya ji Najeeb ya d’auka, a d’an rikice ya ji muryar Najeeb d’in sannan kamar ma driving yake yi, dan yana amsa kiran ya ji Najeeb ya fara magana
“kaga message d’ina ko?
Abbakar ne ya kirani yanzun, ban samu na d’auka ba shine ya turomin message, inaga shima yana wajen.
Ina ganin message d’in na kira shi, an d’auka amma ba a magana..
Babban abun tashin hankalin kamar muryar black snake na ji a wajen, kuma Yash kamar maganar aure su ke yi
da shi da Manubiya!
Amma
ka kwantar da hankalinka
ganinan na ma kusan ƙarasawa police station ɗin.’’

Kashe wayar kawai ya ji Yashjub yayi…..

A yadda ya nufi k’asa sai da ya bawa wasu
tsoro da mamaki, dai-dai nan Daddy yana fitowa dan akwai
speech wanda Yashjub zai bada kuma lokaci ya yi.

Cikin fushi Daddy ya bi shi a baya amman kafin ma ya gama sauk’a k’asan ya hango tashin motar Yashjub ta glass ɗin dake ajikin gefen stairs d’in…
‘Tabbas zai ci uwar Yashjub kam yau!’
Daddy ya raya hakan a cikin ransa,
amma yanzu bari ya koma ya gama da waennan mutanen,first.

Kafin ya koma cikin hall d’in ya turawa Yasira message ya ce ta shirya ita za ta bada speech d’in a madadin Yash…
hakan kuwa aka yi Allah ya taimaka Yasirar ta san kan abun, dan haka ta d’an had’a abubuwan da za ta iya ta bayar taron ya watse.

Daddy kamar ya fashe saboda tsananin takaici, dan ko da ya koma kiran Yashjub ya ci gaba da yi amman sam bai d’auka ko d’aya ba, k’arshe ma message ya yo masa wai ‘’wani abu mai mahimmanci ya taso masa, su k’arashe meeting d’in babu shi kawai!’’.

Me zai fiye mishi wannan meeting ɗin da su ke yi mahimmanci?
Menene har ya fi mahimmanci a wajensa sama da kare mutuncin company da kuma mutuncin shi kansa Daddyn.
Har wanne
irin abu ne zai sanya ya tafi ya bar shi stranded (babu madafa) cikin bak’in mutane haka ya kunyatashi…..
….

Tun kafin ya k’arasa police station d’in ya kira babban office na dss yace ‘yana
buk’atar su,
Black snake yana Nigeria, kano.’
Sannan ya fad’a musu sunan police station d’in.’
Ashe dama neman sa ake yi, ruwa a jallo.

Sun tab’a yin case da Yashjub ta inda ‘black snake ɗin ya so ya cinye masa filinsa, da kyar ya kwato filin nashi’
a ta dalilin hakan ne Yashjub ya san wayene black snake da kuma record d’insa dan ko satin da ya shige ma sai da suka yi maganar sa da Najeeb akan ‘ya je ya gina hotel a filin wani yace filin nasa ne, ana tsakiyar yin case d’in da ya ga za a damk’e sa shine ya gudu’.
Kuma still an banka’do ‘yayi sanadiyyar sace y’an mata, y’an secondary school guda ashirin’.
Shiyasa da yaga za a yi masa tunb’ir a tona masa asiri sannan a kamasa shine ya gudu zaman Nigeria ya gagare sa, ya bari akan in komai ya lafa sai ya dawo.
..
Yash yana gama waya da DSS
ya kira AIG yace ‘’a dakatar da duk wani abu da ake gudanarwa a police station d’in da Najeeb ya gaya masa su Manubiyan su ke”
sannan yace’’ kar a bar kowa ya fita,dss suna hanya za su kama black snake’’.

Tafiyar mintuna goma ce ta kai shi police station d’in dan bashi da nisa da su, sannan bai bi k’a’idodin hanya da titi ko guda d’aya ba sakamokon uban gudun da ya tsula kamar ba gobe.

Motarsa tana yin parking ta wani dss shi d’aya ko uniform babu a jikinsa ta yi parking, da sauri ya k’araso ya nunawa Yashjub id card d’in sa kafin yace ‘’kai ne ka yi waya ko? ina kusa sosai na ga assignment d’in shine na k’araso da wuri but mota biyar tana hanya, yanzunnan zaka gansu inshaaAllah. “

Sam Yashjub bai ji dad’i ba, dan so yayi ace tawagar su ce tazo da wuri haka saboda ya san black snake baya yawo shi kad’ai,
dan ga police station d’in ma yanzu haka ya cika tapp da motocin da ya tabbatar nasa ne da shi da Jama’ar sa.

Kamar yadda jami’in dss d’in ya nunawa Yashjub Id card haka ya k’arasa ya nunawa ragowar y’an sandan dake harabar wajen id card d’insa dan haka a take suka sara masa suka bi bayan sa su ka yi ciki gaba d’ayan su……

…..4 minutes before now.
(Mintuna huɗu da suka shuɗe)…

Ana shirin fara d’aura aure
Dpo ya fita domin amsa waya,
kafin minti d’aya sai gashi ya dawo…jikinsa har yana d’an karkarwa.

Da mamaki black snake ya ke kallon sa yana shirin yin magana Dpo d’in ya k’arasa inda yake ya ce
‘’Muna da problem fa! an san kana nan’’

Dariya black snake yayi kafin yace
‘’Relax(kwantar da hankalinka), babu wanda ya Isa ya yi arresting ko ya iya dakatar da ni’’

Cikin yin k’asa da murya dpo ya ce
‘’Ban san ya akayi ba, amman Dss ne a hanyar zuwa nan fa black snake, sun san kana nan gurin
Sun kusan ƙarasowa ma yanzu haka, sannan oga kwata kwata ya kirani ya ce
In tsayar da koma me ake yi anan ɗin sannan in kama ka!!

da farko ma da suspending d’ina ya yi, sai da na rantse masa akan ban san da case d’in ‘ana neman ka’ ba tukunna ya bar ni yace in tabbata na kama ka!’’
Chapter 62 · 0% Book details