← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 84

Sashe 69

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko iskar da ta d’ebo ta bai yarda ya kalla ba, ya sake rik’e hannun Yaron ya zo zai shige cikin gidan…suna zuwa da
Yaron ya gane ashe uwarsa ce tare da masu adaidaita sahun ai kuwa nan ya hau ihun sai ya bi ta.

Tana gani ya fara tsalle ana jan shi yana tirjewa ta dawo ta kama kunnesa ta ja tukunna tace
“in na sake jin sunana a bakinka sai na ci uban ubanka! shegen Yaro kawai sai kace dashi na zo’’
daga haka ta juya zata wuce
ta ji Ya Musbah ya ce ’’Babana yi
hak’uri, mu wuce mu shiga gida,
yawo a titi bai kamace ka ba’’

Ai kuwa cikin fushi Baraka ta juyo
‘’Ai sai ka bari in gidan naka ne sai ka yi tink’aho da shi, talaka mara matsugunni kawai,
gara ni idan na tafi yawo a titin ba’a gidan haya zan k’are ba!
kai kuwa nan da y’an kwanaki za a zo ayi waje da kai dama darajata yasa mai gidan yake d’aga maka k’afa yanzu kuwa na san ba zai barka ka cigaba da zama daga kai sai uwarka b……”

Da sauri ya d’auke me sunan baba, ya wuce ciki ya banko k’ofar dan bai shirya biyewa Baraka a k’ofar gida ba…
Ta jima kuwa tana ta tijara ita kad’ai sai da masu mashin d’in suka ce mata “in bata shirya tafiya ba, zasu sauk’e mata kayanta su yi gaba’’
tukunna ta shiga ta zauna a take kuma sai ta fashe da kuka.

To dai Baraka tun kan aje koina sai da ta ji dama bata fito daga gidan mijin nata ba saboda d’ayan mai mashin d’in bai rik’e mata amana ba…dukda kuwa tafiyar da sukayi bata wuce ta mintuna biyar a tsakani ba
amma
da yayi wura wura ya ga babu ido a kansa
chan ya chanza hanya.

Sai da ta Isa k’ofar gidansu tukunna ta lura babu napep d’aya.
••••••••
Tun lokacin da Yashjub ya bar office Daddy ya k’ule, ganin la’asar har ta gota bai kira kuma bai zo ba ne ya sanya shi ya kira Najeeb a fusace ya bashi sa’ko amman gashi har bayan Magrib Yashjub d’in bai iso ba.

Yassira ce ta guntsawa su Mommy abunda Yashjub d’in yayi yau a office, gashi kuma har yanzu bai dawo ba..hakan kuwa ba k’aramin sake d’aga musu hankali yayi ba dan tashi
d’aya suka yanke cewa
‘’wannan yarinyar da suke zargi ce ta kirasa’’
Saboda Yasirar ta ce musu ko bayan da aka tashi daga office sai da suka biya d’ayan company d’in Yash d’in ita da Daddy amma akace musu yau throughout bai je chan ba.
Ta tambayi Racheal kuma, ta ce mata ‘’batun estates d’insa komai stable(dai-dai)’’
dan haka matslar ba anan take ba kenan.
Shiyasa suke da tabbacin wannan yarinyar ce kenan…tabbas kuwa zama bai kamasuba dan Indai har matsalarta zata sanya ya mik’e tsulum ya fice ana tsakiyar meeting sannan ya ƙi d’aga wayar kowa har yanzu saboda tsabar yadda ya bata mahimmanci, to hakan ya nuna da akwai babban bound (abu) a tsakanin sa da ita wanda ya zame musu dole su tarwatsa shi tun wuri su yakiceta daga cikin rayuwarsa, tun kafin ya k’ak’abo musu k’adangaren bakin tulu!.

Hakanan gidan ya kasance shiruu kowa da abunda yake tunani har aka yi dinner aka watse babu Yashjub babu alamar sa.

Zuwa wannan lokacin Daddy ya sauk’o daga duk wani fushin da yayi da Yashjub!
dan duk hankalinsa ya tashi,
shiyasa ya yanke shawarar idan k’arfe goma ta yi Yash bai dawoba tou zai kira y’an sanda da sojoji su saka Hannu a nemo masa d’anshi.

Tunda sukayi dinner kowa ya bar dining ya koma cikin parlourn ya zauna….
In banda safa da marwa ba abunda Ddaddy ya ke yi, a kallo d’aya ake iya hango tsantsar damuwa da tashin hankali kwance akan fuskarsa, ya kasa tsaye ya kasa zaune…tabbas yau ya sake tabbatarwa Yashjub shine rayuwarsa.
*MANNUBIYA*
*42*

Tun asalin farko baya k’aunar ganin fushi ko b’acin ransa wannan dalili ya sanya hajiya Mama ta d’auke shi ta maida shi gabanta dan ta ce ‘muddin ta bar masa shi a yadda yake tsananin son nan nashi to ba zai iya yi masa tarbiyya mai kyau ba.’

Daddy ya kasance Mutum mai tsananin k’aunar ya’yanshi amma son da yake yi wa Yashjub wani irin so ne na daban wanda bai tab’a jin kwatankwacin kalar son akan kowa ba bayan uwar da ta haifesa sai ga Khadijah mahaifiyar Yahanasu.

Bayaso ya yarda da cewa ya fi son Yash dan baya son ya samu banbanci a tsakanin Ƴaƴan nasa amma yau kam ya yarda ya tabbatar, dan gashi kwata-kwata ko awanni 12 ba ayi ba amma rashin sanin inda Yash ɗin ya ke yana neman haukatasa, ji yake yi kamar ya d’aga Hannu ya zunduma ihu.
Gashi dai laifi ya yi masa amma
zuwa wannan lokacin har laifin ya gogu a idanun Daddy…..kawai shi matsalar da ke a gabansa a halinda ake ciki itace ya san inda Yashjub d’in yake da lafiyar sa.

Gashi ya kira gidan su Najeeb shima ance bai Isa gida ba kuma duk wayoyinsu a kashe, hakan ya sanya tashin hankalin nasa ya sake hauhawa.

Mommy kuwa za’a iya cewa tashin hankalin nata ya kusan k’etare na Daddy dan dai kawai ita ɗin tana iya danne nata ne.
Babban tashin hankalinta shine ‘wannan Yarinyar da ko sunanta basu saniba ballantana su samu su fara bi takanta, dan indai har ita ce ta kira Yash ta sanya shi ya yi wannnan dogon zango haka to kuwa sunada babbar matsala, dan haka abar a fara bi takanta tun da wuri.

Kausar itama daurewa kawai ta ke yi amma had’iyar zuciya ne kawai ya rage batayi ba….
basu riga sun gama tabbatarwa ba amma tabbas in dai maganar Baba Larai ta zamto gaskiya ce! To wallahi sai ta nemo yarinyar nan a duk inda ta ke ta halaka ta!
Bata da wani zaɓin da ya wuce ta kaita lahira dan ba a halicci Macen da ta Isa ta shiga zuciyar Yashjub ba wallahi!
Ko ta shiga sai ta fito…..

A b’angaren Yassir kuwa,
ba k’aramin sake hawa ya yi ba, yadda hankalin Daddy ya tashi ne ya fi komai d’aga masa nashi hankalin….duba da yadda laifi fa Yashjub d’in yayi fushi ya kamata ace Daddyn yayi da shi
amman ya b’ige da damuwa akan rashin sanin inda yake sai kace wani jinjiri.
Zuwa wannan lokacin shi kam ba ya buk’atar wasu shaidun da za su sake tabbatar masa da ‘Yashjub na musamman ne a cikin gidan nan’ dan ya riga ya yarda sannan ya aminta da hakan….

Ya tabbatar inda ace shine ya b’ace haka to da babu wanda zai damu..kwanakin da suka shuɗe lokacin da ya yi fushi ya tafi, Daddy bai san inda yake ba amma bai damu ba!
haka aka share kwanaki ko neman sa bai yi ba, kuma bashi da niyyar neman nasa….

Inaa, gaskiya da sake! dan ba zai yiu a dake shi sannan a hana shi kuka ba..ba zai kuma yiu ace uwa d’aya uba d’aya su haifesu ba amma ace ya fi shi fada !kud’i!farin jini!jama’a!ilimi
sannan ya d’auke soyayyar iyayen su…ya zama dole ya gyara hakan, in kuma ba zai gyaru ba to dole ya bi ta ko wacce hanya ce yayi maganin wannan matsalar tun kafin bak’in ciki ya kashe sa!!
Dan shi kad’ai ya san me yake ji a cikin zuciyarsa…a halinda ake ciki k’ok’ari kawai yake yi yana danne kansa amma ji yake yi kamar ya had’a Daddy da Yashjub d’in ya saka musu bomb!! Musamman ma da ya tuno da abunda Kausar ta gaya masa ‘’ace wai Yashjub yanada 50% (kaso hamsin) shi kuma wai 1 %’’
wannan rashin adalcin har Ina haka!?.
••••••
A chan b’angaren su Manubiya kuwa, tun tafiyar Baraka…
tsabar b’acin rai tsakanin Aisha Jidda da Manubiya babu wadda ta iya cewa komai, ko abincin da Aishar ma ta kawo duk kasa ci suka yi.
Inna kuwa ta lumshe idanuwanta kawai dan bata so ta bud’e hawaye su fito ta sake d’aga musu hankali, shiyasa kawai ta lumshe idanun nata ta yi shiruu iskar fiffitar da suke yi mata su duka ukun tana ratsata.

Suna a zaune Ya Musbah ya shigo,
shi da mai sunan baba wanda yaketa faman zabga ihu da shure-shuren shi sai ya bi mamansa….

Ganin khairat abokiyar wasan shi ne ya d’an rage zafin abun, kafin dare sharr Yaron ya sake ya shiga mutane yanata wasa.

Ba su dad’e sosai ba, ya Nafi’u ya zo, dan haka gaba d’ayansu suka nufi gida bayan ya Nafi’u ya sanya su Manubiya sun yi mishi alk’awarin ba za su gayawa Baba komai game da zancen Baraka ba tukunna.

A ranar Baba ya ga gata,
har da kwallar farinciki sai da yayi.
Kamar komai bai faru ba
haka suka zauna har Ya Nafi’u da Aisha aka sha hira,
aka ɗan kwantarwa da juna hankali.

Sun jima tukunna Ya Nafi’u da Aisha tare da khairat suka yi shirin tafiya, dan haka Baba ya cewa Ya Musbah shima ya tashi ya bisu kar a bar Baraka ita kad’ai.
Da “to” ya amsa shi, daganan ya yi musu sallama suma suka fice shi da mai sunan baba.

Su Ya Musbah suna fita su Jidda suka sanarwa Baba
‘ai d’azu ma Siyama ta kira, lokacin suna asibiti, wai mamanta ba lafiya, shiyasa ma bata je ba.’’

Ba tare da b’ata lokaci ba ya ce musu
“su mik’e su je su dubota,
ai da sun fad’a tun d’azu, Allah yasa su Siyaman ba su riga sun yi bacci ba.’’

Da “to” suka amsa, daga haka suka fita….bayan fitar tasu ne Baba ya matsa kusa da Inna…
duk abinda ya faru yau ba abunda ya b’oye mata, saboda yanaso ta sani domin ta fahimce sa kuma ta goya masa baya akan aurar da su Jidda da yake shirin yi cikin gaggawa.
Yaga alamar amincewa kuwa a fuskarta dan har lumshe masa idanuwa ta yi ta bud’e, dan haka ya sake jin dad’i ya kuma samu kwarin guiwa….hakanan yayi ta mata magana dukda ya san ba za ta mayar masa ba amma ya san tana sauraronshi, kuma ta fahimcesa.
Chapter 69 · 0% Book details